* Rarara ya ba shi kyautar mota
FITACCEN mawaƙi a Kannywood, Abdul D. One, ya bayyana cewa auren da ya yi a farkon wannan makon ya kawo masa kyakkyawan yanayi a rayuwar sa.
A hirar da angon ya yi da mujallar Fim kwana huɗu bayan an ɗaura auren sa da amaryar sa, Ummu-Salma Sulaiman (Salma Fresh), a Kano, ya labarta mana yadda rayuwa ta fara kasancewa a gare shi
Abdul, wanda cikakken sunan sa Abdulƙadir Tajuddeen, ya ce: “Gaskiya rayuwa ta ta da da ta yanzu akwai bambanci sosai, sakamakon in lokacin sallah ya yi za a tada ni in yi sallah, za a ba ni abinci in ci, haka kuma idan zan saka kaya mata ta ta ruga ta ɗauko min kayan da zan saka, wanda a da ni na ke ɗaukowa da kai na. Haka kuma ruwan wanka ta na dafa min.

“Duk da haƙƙi na ne in dafa mata, in girka mata abinci, haƙƙi na ne in yi mata duk wasu abubuwa na rayuwa da ka sani, saboda addinin Musulunci yadda ya tanadar kai za ka yi mata, duk abin da ta yi maka kyautatawa ne kawai. A gaskiya na ji daɗi sosai.
“Ina ganin bambancin rayuwa, don a wurin bikin ne aka ba ni kyautar mota. Lallai na ga canji a rayuwa ta sosai.”
Angon ya ƙara da cewa: “Haƙiƙa na yi farin ciki sosai. Wannan lokaci na farin ciki ne a cikin rayuwa ta.
“Ina godiya ga masoya na sosai saboda halartar taron biki na da su ka yi, don an zo biki sosai, waɗansu ma ban san su ba, ban taɓa ganin su ba.”
Idan dai ba ku manta ba, mun kawo maku labarin za a yi auren.
An dai ɗaura auren Abdul da Salma Fresh a safiyar ranar Lahadi, 12 ga Disamba, 2021 a Layin Transformer, Kwanar ‘Yan Ghana da ke unguwar Tudun Murtala a birnin Kano a kan sadaki N100,000.
‘Yan fim da mawaƙa da dama sun halarci ɗaurin auren.
A daren ranar da aka ɗaura auren an shirya gagarumar dina a ɗakin taro mai suna Gidan Biki da ke Titin Magajin Rumfa, Kano.

‘Yan fim sun yi wa D. One kara, domin kuwa kusan ɗaiɗai ne ba su halarta ba. An yi nishaɗi tare da taya ango da amarya murna.
Wani abin farin ciki kuma a wurin dinar shi ne fitaccen mawaƙin siyasa Dauda Adamu Kahutu (Rarara) ya gwangwaje angon da kyautar mota ƙirar Honda samfurin ‘End off Discussion’.
Wasu daga cikin waɗanda su ka halarci dinar sun haɗa da Ali Nuhu, Dauda Rarara, Abdul Amart, Umar M. Shareef, Tijjani Faraga, Abubakar Bashir Maishadda, Sadiq M. Mafia, Naziru Ɗanhajiya, Maimuna Ali Nuhu, Amal Umar, Khairat Abdullahi, Mommy Gombe, A’isha Najamu da sauran su.

Kwana ɗaya kafin ranar ɗaurin auren, wato ranar Asabar, an buga wasan ƙwallon ƙafa a filin wasa na Ahmed Musa da ke Kano, tsakanin ‘yan kamfanin ‘FKD Production’ na Ali Nuhu da ‘yan ‘Shareef Studio’ na Umar M. Shareef wanda ango Abdul ke ƙarƙashin sa.






