MAWAƘI a Kannywood, Abubakar Abdullahi, wanda aka fi sani da Auta Waziri, a yau Juma’a ya zama cikakken mutum.
An ɗaura auren sa da santaleliyar sahibar sa, Halima Mustapha (Marmah).
An ɗaura auren da misalin ƙarfe 1:15 na rana, bayan gama sallar Juma’a a masallacin Juma’a da ke Makarantar Tunawa da Sardauna (SMC) da ke Unguwar Dosa, Kaduna, a bisa sadaki N200,000.

Bayan ɗaurin auren, an gudanar da walima a ɗakin taro na Umaru Musa ‘Yar’Adua da ke Murtala Square.
‘Yan Kannywood da suka halarci ɗaurin aure da walima sun haɗa da Aminu Ala, Abubakar Sani, Umar M. Shareef, Nura M. Inuwa, Adamu Hassan Nagudu, Usman Sojaboy, DJ AB, Ado Gwanja, Kawu Ɗansarki, Umar M.B., Sani Sabo Kwarko, Ikram Kano, S.S. Danko, Umar Big Show, Abba D. Malam, A.A. Rasheed Kabala, Hamza S. Matawalle, Musa Mairabo, Haruna Haji da Yusuf Waza-Waza.



Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba.
Idan kun tuna, a wurin wasan ƙwallon ƙafa don taya murnar wannan bikin ne Allah ya ɗauki ran fitaccen mawaƙi El-Mu’az Muhammad Birniwa shekaranjiya.