• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, May 14, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ba za a yi bala’i a zaɓen Edo ba, inji Oba na Benin

by DAGA WAKILIN MU
August 28, 2020
in Nijeriya
0
Daga hagu: Oba na Benin, Ewuare II, tare da Farfesa Mahmoud Yakubu a lokacin ziyarar

Daga hagu: Oba na Benin, Ewuare II, tare da Farfesa Mahmoud Yakubu a lokacin ziyarar

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
• INEC ta shirya wa zaɓen – Farfesa Yakubu
 
Oba na Masarautar Benin, Ewuare II, ya bayyana tabbacin cewa ba za a yi wani bala’i a zaɓen gwamna da za a yi a Jihar Edo a ranar 19 ga Satumba ba, akasin yadda wasu ke hangowa.
 
Shi Oban, wanda shi ne sarkin masarautar, ya yi wannan bayani ne a lokacin da shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya kai masa ziyara a fadar sa tare da wasu kwamishinoni na ƙasa na hukumar a jiya Alhamis.
 
A cewar Oba na Benin, kada mutane su ji fargabar komai, domin ana ta addu’a da azumi a kan zaɓen.
 
Haka kuma ya ce kafin ranar zaɓen zai gayyaci ‘yan takarar gwamnan zuwa fadar sa don ƙara nanata yarjejeniyar zaman lafiya da Kwamitin Wanzar da Lumana na Ƙasa, wato ‘National Peace Committee’, zai yi da su kwanan nan a Birnin Benin.
 
Ya ce: “Mu na kula da duk yadda lamarin ke gudana. Akwai damuwa matuƙa, amma a ƙarshe dai za mu ga haske.
 
“Mu ci gaba da yin addu’a, domin ta fi bakin bindiga ƙarfi saboda babu matsalar da addu’a ba ta iya warwarewa.
 
“Kowa na ta yin kiraye-kiraye ga sojojin ruwa da ‘yansanda da sojojin sama sai ka ce wani yaƙi za a yi. Edo ba filin daga ba ce.
 
“Duk wanda ke so ya jawo rikici ko zubar da jini, to a kan sa abin zai ƙare. Alhaki na nan fa. Na damu da yadda ake ta gudanar da al’amarin.
 
“Ina kira ga mutanen mu da kada su salwantar da ran su saboda wani mutum. Su waɗanda ke amfani da ‘ya’yan wasu wajen rikici ai  ba su barin nasu ‘ya’yan su fito. Idan an kashe ko an raunata waɗanda su ka shiga rikici, su kuwa sai su ci gaba da wawurar kuɗaɗen jama’a.”
 
Oba na Masarautar Benin ɗin, wanda ya tabbatar da cewar fadar sa ba ta da wani ɗan lele a cikin ‘yan takara a zaɓen, ya shawarci masu zaɓe da su tsaya da kyau su duba ɗan takara kafin su zaɓe shi. Ya ce kada a zaɓi duk wani wanda halayyar sa ba ta da kyau a matsayin wanda zai ɗare kujerar nan mai daraja ta gwamna.
 
A wani labarin mai kama da wannan, shugaban Hukumar Zabe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa hukumar sa ta shirya tsaf domin gudanar da zaɓen na gwamnan Jihar Edo.
 
Ya yi wannan bayani mai ƙarfafa gwiwa ne a jiya Alhamis, lokacin da ya ke ganawa da Kwamitin Tuntuɓar Harkokin Tsaron Gudanar da Zaɓe a Benin, babban birnin jihar.
 
A cewar sa, ya zuwa yanzu INEC ta samu nasarar aiwatar da tsare-tsare har guda 10 daga cikin 14 da ta ƙudiri aniyar aiwatarwa dangane da zaɓen.
 
Ya ƙara da cewa, “Dalilin wannan ziyara shi ne domin mu ga irin shirye-shiryen da aka fara tun yanzu kafin gabatowar ranar zaɓe. Tabbas, mu na samun dukkan rahotannin shirye-shiryen da ke gudana. Amma duk da haka mu ka ga ya dace mu zo da kan mu, domin gani da idon mu ƙarara.
 
Shugaban INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu na gabatar da jawabi a gaban Oba na Benin
“Wannan hukuma ta fitar da jadawalin tsare-tsaren yadda matakan zaɓukan Edo da Ondo za su gudana, tun a ranar 6 ga Fabrairu, 2020. Wato kenan mun bayar da sararin watanni kusan bakwai zuwa takwas domin a shirya wa zaɓuɓɓukan biyu sosai.
“To a yau ina farin cikin cewa mun aiwatar da tsare-tsare 10 daga cikin 14 da INEC ta shirya aiwatarwa. Kuma babu wanda aka samu wani tsaikon da har sai da ta kai an sake ɗage ranar da za a aiwatar da shi.
 
“Abu na ƙarshe shi ne damƙa rajistar gaba ɗayan masu jefa ƙuri’a adadin su baki ɗaya ga jam’iyyu 14 da za su fafata takara.”
 
Farfesa Mahmood Yakubu ya ce ayyuka huɗu da su ka rage wa INEC sun haɗa buga sanarwar zaɓe da za a yi ranar Talata mai zuwa, gabatar da sunayen ejan-ejan na kowace jam’iyyar da ta shiga takara, duk a rana ɗaya.
 
“Sai kuma dakatar da kamfen sa’o’i 24 kafin zaɓe. Wato kenan za a dakatar da kamfen da ƙare 12 na daren Alhamis, kafin Asabar ɗin da za a yi zaɓe.
 
“Saboda haka mu dai sai mu ce mun ma rigaya mun kimtsa, sai jiran zuwan ranar zaɓe kawai.”
 
Shugaban ya yi tsinkayen cewa zaɓen gwamnan Jihar Edo ne zaɓen farko da INEC za ta fara gudanarwa a lokacin annobar korona.
 
A kan haka ya ce hukumar zaɓen ta fito da ƙa’idojin yadda za a gudanar da zaɓen a wannan yanayi da ake ciki.
Shugaban Hukumar Zaɓe, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya na gaisuwa ga Oba na Benin, Ewuare II
Ya ce, “Mun jaraba tsarin da ƙa’idojin a wani ƙaramin zaɓen cike-gurbi a Jihar Nasarawa. Kuma mun shirya maimaita tsarin a wannan babban zaɓe na Edo.”
 
Tun da farko, sai da Kwamishinan Zaɓe na Jihar Edo, Mista Johnson Alalibo, ya yi bayanin cewa akwai masu rajista mutum 2,210,534 a Jihar Edo, waɗanda a cikin su 1,159,325 maza ne, mata kuma 1,051,209.

Loading

Previous Post

Zaɓen Edo: INEC za ta yi amfani da rajistar 2019, inji kwamishina

Next Post

Gwamnatin Kano za ta haɗa gwiwa da wani kamfani don gyara fasalin Kannywood

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya na jagorantar zaman majalisar zartaswa ta jihar

Gwamnatin Kano za ta haɗa gwiwa da wani kamfani don gyara fasalin Kannywood

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!