• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, May 14, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gwamnatin Kano za ta haɗa gwiwa da wani kamfani don gyara fasalin Kannywood

by DAGA IRO MAMMAN
August 28, 2020
in Labarai
0
Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya na jagorantar zaman majalisar zartaswa ta jihar

Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya na jagorantar zaman majalisar zartaswa ta jihar

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
WANI kamfani mai zaman kan sa ya gabatar wa da gwamnatin Jihar Kano wani tsari kan yadda za ta gyara masana’antar finafinai ta Kannywood domin a samu ƙarin kuɗin shiga.
 
A takardar sanarwa ga manema labarai da mai ba gwamna shawara kan aikin jarida, Abba Anwar, ya rattaba wa hannu, wadda mujallar Fim ta samu, an bayyana cewa kamfanin, mai suna ‘Credent Capital and Advisory’, ya gabatar da shawarwarin sa ne a cikin wata takarda da shugaban kamfanin ya miƙa wa gwamnatin a ranar Laraba, 26 ga Agusta, 2020.
 
A yayin da ya ke gabatar da jawabin sa a gaban majalisar zartaswa ta jihar a Gidan Gwamnati (Africa House), Kano, Manajan Darakta na kamfanin, Dakta Charles A. Kachill, ya nuna damuwar sa kan abin da ya kira rashin samun kuɗin shiga ga Kannywood sakamakon rashin kyakkyawan tsari saboda rashin kataɓus ɗin ‘yan masana’antar da sauran masu ruwa da tsaki.
 
Mista Kachill ya bayyana cewa kamfanin sa zai haɗa hannu da gwamnatin Jihar Kano don a yi wa masana’antar garambawul.
 
 Ya ce, “Kannywood fa industiri ce wacce darajar ta ta haura dala miliyan ɗari takwas ($800m). To amma ba a tsara ta yadda za ta ci moriyar shirye-shiryen da ke akwai a ƙasa ba daga Gwamnatin Tarayya da sauran hukumomi da ƙungiyoyin ƙasashen waje.
 
“Saboda haka ya kamata a gyara ta yadda za ta zama masana’anta ta gaske sosai.”
 
Bugu da ƙari, ya ce, “Mu na magana ne kan matasa sama da miliyan biyu da za su iya samun aikin yi a masana’antar. Mu na da furodusoshi, daraktoci, ‘yan wasa maza da mata, marubuta, ‘yan kasuwa, masu raba finafinai, masu kyamara, mamallaka gidajen sinima, da sauran su da dama.”
 
Shugaban kamfanin ya faɗa wa majalisar cewa kamfanin sa na Credent ya na so ya zama babban mai ɗora masana’antar a kan turbar cigaba a yayin da ita kuma gwamnati za ta mara masa baya wajen tabbatar da an yi duk abin da ya dace.
 
Haka kuma ya bayyana cewa akwai buƙatar a gyara wannan masana’anta ta nishaɗantarwa ta yadda za a ci moriyar ta sosai a jihar, musamman wajen samun kuɗaɗen shiga ga gwamnati. 
 
Mista Kachill ya kawo shawarar a kafa wani kamfani na kasuwanci wanda gwamnatin jihar za ta riƙa gudanarwa, wanda ta hanyar sa za a riƙa isar da tsare-tsare ga ‘yan fim ɗin da ke masana’antar Kannywood kamar yadda ya kamata.
 
Bayan ya gama jawabin sa, sai Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi nasa jawabin, inda ya ce majalisar zartaswar za ta duba takardar da Mista Kachill ya kawo domin ta yanke shawara a kai.
 
A takardar sanarwa ga manema labarai da mai ba gwamna shawara kan aikin jarida, Abba Anwar, ya rattaba wa hannu, an ce gudanar da wasu ayyuka ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da ‘yan kasuwa ya na daga cikin muhimman tsare-tsaren wannan gwamnatin ta Jihar Kano.

Loading

Previous Post

Ba za a yi bala’i a zaɓen Edo ba, inji Oba na Benin

Next Post

Afakallah: Abin da ya sa Adam Zango ya yi mubaya’a

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Adam A. Zango (a dama) tare da Malam Afakallah a lokacin ziyarar ... cike da murmushi

Afakallah: Abin da ya sa Adam Zango ya yi mubaya'a

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!