• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, July 23, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Babu ranar tsayar da gidauniyar Auwal Ɗanborno, cewar Aunty Baby

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
July 3, 2023
in Labarai
0
Marigayi Auwal Garba Ɗanborno (a hagu) da Hajiya Umma Sulaiman 'Yan'awaki (Aunty Baby)

Marigayi Auwal Garba Ɗanborno (a hagu) da Hajiya Umma Sulaiman 'Yan'awaki (Aunty Baby)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ƊAYA daga cikin makusantan Alhaji Auwal Garba Ɗanborno ta bayyana cewa su shaƙiƙan marigayin sun ƙudiri aniyar tabbatar da cewa rayuwar ‘ya’yan sa ba ta tagayyara ba saboda rashin sa.

Fitacciyar marubuciya a Kano, Hajiya Umma Sulaiman ‘Yan’awaki (Aunty Baby), ita ce ta bayyana haka a hirar ta da mujallar Fim inda ta ce: “Duk wata damawa, in Allah ya yarda mu ne za mu zama makwafin sa. Kuma kowane ɓangare na kula da rayuwar ‘ya’yan sa za mu shiga.”

Mujallar Fim ta ba da labarin rasuwar fitaccen marubuci kuma ɗan sanda Auwal Ɗanborno a haɗarin mota da ya ritsa da shi a ranar Lahadi, 25 ga Yuni, 2023.

Haka kuma mujallar ta ba da labarin cewa wasu makusantan mamacin sun kafa gidauniya ta musamman don ganin an tallafa wa iyalan sa, kuma tuni aka fara tattara kuɗaɗen tallafi a gidauniyar.

Aunty Baby, wadda ta na ɗaya daga cikin masu harhaɗa kuɗin, ta yi wa wakilin mu bayani dangane da manufar su, ta ce, “E to, gaskiya wannan kwamiti da aka yi shaƙiƙan Auwalu G. Ɗanborno, duk wanda ka gani a wannan zaman da mu ka yi kowa ya na ganin ya fi kusa da Ɗanborno a kan wanin sa. Don haka mu shaƙiƙin mu ne, mutumin mu ne, a ko da yaushe mu na tare, sannan duk wani abin rayuwar sa mun sani kuma shi ma ya san namu, don haka mun zama ɗaya mu da shi.

Shi ya sa mu ka ga me za mu yi bayan babu shi, don haka mu ka yanke shawarar mu taimaki iyalan sa, iyalin nasa ma kuma ‘ya’yan sa. 

“Sai mu ka ga hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka, don haka tunda mu na da yawa sai mu ka kafa wannan gidauniyar wadda mu kan mu mu ka sassaka wani abu a ciki don tallafar marayun da ya bari na ‘ya’ya guda goma da ya ke da su.”

Ta ci gaba da cewa, “Babbar manufar mu a nan ita ce a tallafa wa ‘ya’yan sa su yi karatu, saboda shi burin da ya tafi da shi kenan a zuciyar sa, ‘ya’yan sa su yi karatu, don ‘ya’yan sa ya kai su makarantu masu kyau ya na kula da su. 

“So mu ke kada yaran su kalla su yi kukan rashin uba, kada ya kasance wata rana a koro su daga makaranta saboda babu kuɗin makaranta. Don haka duk wata damawa, in Allah ya yarda mu ne za mu zama makwafin sa. Kuma kowane ɓangare na kula da rayuwar ‘ya’yan sa za mu shiga.”

Dangane da adadin kuɗin da aka samar zuwa yanzu kuwa, cewa ta yi, “To a yanzu dai mun samu miliyan ɗaya da dubu ɗari biyu da ‘yan kai. Kuma wannan gidauniyar babu ranar tsayar da ita, don haka ba mu san iya abin da Allah zai ba mu ba sai dai abin da mu ka gani kawai.”

Da mujallar Fim ta tambayi Aunty Baby ko akwai wani abu da su ka zartar za su samar na kula da yaran zuwa yanzu, sai ta amsa da cewa, “To, gaskiya a yanzu dai ba mu kai ga zartarwa ba, mu na dai kan haɗa kuɗin, sai yadda shawara ta tsaya a kan abin da za a yi da kuɗin. A yanzu dai sirri ne namu na cikin gida. 

“Kuma ka gane ba iya marubuta ba ne makusantan Auwalu G.

Ɗanborno, don haka duk wani makusancin sa ko a cikin marubuta ya ke ko a wani ɓangaren ya ke, to ya na cikin wannan gidauniyar.

“Don haka kamar yadda na ke faɗa, kowa ya san halin Ɗanborno, ya na da kyan hali, ya zauna da mutane lafiya, ya gama da duniya lafiya. Mutum ne adali, karimi, kuma duk wata gidauniyar da za a yi a ɓangaren marubuta Auwalu G. Ɗanborno shi ya ke fara buɗe ta.

“Don haka jama’a ina kiran ku duk wanda Allah ya hore wa ya na iya taimakawa da duk abin da ya sauwaƙa. Shi aikin Allah da taimako ba ya yawa kuma ba ya yin kaɗan.”

Loading

Tags: Aunty BabyAuwal Garba ƊanbornogidauniyamutuwatallafiUmma Sulaiman 'Yan'awaki
Previous Post

Akwai daɗi da kuma ƙalubale a rubutun onlayin – Ummulkhairi Sani Panisau (Khairat Up)

Next Post

Aure: Yakubu Lere zai zama mai igiya uku a ranar Asabar

Related Posts

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa
Labarai

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa

July 17, 2025
Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano
Labarai

Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano

July 11, 2025
Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 
Labarai

Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 

July 10, 2025
Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a
Labarai

Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a

July 9, 2025
Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu
Labarai

Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu

July 7, 2025
MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 
Labarai

MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 

June 29, 2025
Next Post
Yakubu Lere

Aure: Yakubu Lere zai zama mai igiya uku a ranar Asabar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!