• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, May 31, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ban taɓa samun karramawa kamar ta Zuma ba – Daso

Gwamnatin Tarayya ta ba Saratu Giɗaɗo kyautar 'Lifetime Achievement'

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
December 12, 2023
in Tattaunawa
0
Ban taɓa samun karramawa kamar ta Zuma ba – Daso

Hajiya Saratu Giɗaɗo da kambin karramawar da NFC ta yi mata

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A RANAR Asabar, 9 ga Disamba, 2023 aka yi bikin karramawa na ‘Zuma Film Festival’ wanda Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya (Nigerian Film Corporation) ta saba yi a duk shekara a Abuja. A bikin, wanda ake yi shekara-shekara, wannan hukumar ta Gwamnatin Tarayya ta kan karrama jarumai da kuma fitattun ‘yan Nijeriya da su ka bayar da gudunmawa ga cigaban ƙasa a wani fannin fasahar fim.

A bikin na bana, fitacciyar jarumar Kannywood, Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso) ta na ɗaya daga cikin waɗanda aka karrama, ko inda aka ba ta Kyautar Gwarzantaka a Tsawon Rayuwa, wato ‘Lifetime Achievement Award’.

Mujallar Fim ta tattauna da jarumar barkwancin a game da wannan abin farin ciki da ya same ta, kamar haka:

 

FIM: Kin samu babban kambu na karramawa daga Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya a taron da ta gudanar. Ki yi wa masu karatun mu ƙarin bayani.

SARATU GIƊAƊO: Wato Allah mai iko kamar yadda ka ce an karrama ni a zaɓen gwaraza da zan kira shi na duniya, don har da ma mutanen Ingila a ciki na gani; sun zo daga Faransa da sauran ƙasashe, duk sun zo, mun yi hotuna ma da su. Kuma ni a Arewa ni kaɗai ce aka zaɓa saboda sun ga cancanta ta a kan irin aiki na na sana’a ta ta fim su ka gayyace ni kamar yadda saƙon ya zo mani ta soshiyal midiya saboda duk yanzu na fi mayar da ayyuka na a kan soshiyal midiya. Don haka duk wanda ya ke so ya yi magana da ni ta soshiyal midiya ake samu na, ba sai an tambayi wani lamba ta ba.

Daso na karɓar kambin karramawar ta

To, don haka wannan gayyatar ma ta Instagram su ka yi mani magana, don haka sai na ji daɗin karramawar saboda ban san su ba, kuma ban taɓa ganin su ido da ido ba; kawai a fim su ka gan ni su ka ga cancanta ta ba tare da sun bi ta hannun kowa ba, su ka bi ta shafi na na Instagram mu ka yi magana har su ka turo mani kuɗin jirgi su ka samar mani da masauki. Kuma kafin wannan sun turo mani da katin gayyata na ranar da za a yi, kafin wata guda a yi taron, amma ban sanar ba saboda halin rayuwa, sai ranar da za a yi na sanar.

Kuma a yanzu Allah ya sa mun je an yi taro an tashi lafiya na dawo gida na tare da kambun karramawa da aka ba ni.

FIM: Da yake jama’a ne masu yawa aka karrama, ko yaya ki ka samu kan ki a cikin wannan taron?

SARATU: To, gaskiya kamar yadda na faɗa maka ni kaɗai ce daga Arewa a fannin sana’ar mu, haka ma mutum ɗaya ne daga Kudu wanda shi bai samu zuwa ba, kuma duk wasu harkokin rayuwa daga Arewa ma ni kaɗai ce na je wanda aka karrama, sai dai waɗanda aka gayyata. Don haka na ji daɗin wannan karramawar sosai, saboda na wakilci Arewa kuma na wakilci Kannywood. Don haka wannan abin alfahari ne a gare ni.

Tare da Minista Dakta Mariya Bunkure a zauren taron

FIM: Ba a wannan ba ne ki ka fara samun kambu na karramawa. Me ya bambanta wannan da waɗanda ki ka samu a baya?

SARATU: E haka ne, na sha samun karramawa, ina ganin tun da na shiga harkar fim ma na ke samun hakan. Yau shekara 23 kenan ina samun kyaututtukan karramawa daga ɓangarori na jama’a da dama. Amma dai wannan shi ne mafi girma da na samu, saboda shi ne aka kira ni har zuwa Abuja don a karrama ni kuma aka haɗa mu da manyan mutane na duniya aka aka karrama mu. Kuma shi ma kambun karramawar na musamman ne, don haka zan iya cewa wannan shi ne mafi girman karramawa da na samu a yanzu; ban san nan gaba ba ko za a kira ni zuwa Ingila da Amurka don a karrama ni.

Kuma alhamdu lillahi wannan ya ƙara mani ƙarfin gwiwar da na samu da zan ci gaba da harkar fim da aka san ni da ita, domin irin wannan shi ne ya ke ƙara wa irin mu ƙarfin gwiwa saboda ba don mun san wani ko wata hanya ba, kawai Allah ne ya sa aka ga mun cancanta aka ba mu, saboda an ga yadda na ke a cikin harkar fim, na mayar da abin sana’a ba wai na ɗauki abin da wasa ko wata kwalliya ba, kawai ina sana’a ne don na samu kuɗi na gudanar da rayuwa ta cikin mutunci.

Tare da Alhaji Abdulkareem Mohammed

Don haka ina kira ga abokan sana’a ta ‘yan fim, su daure su ci gaba da ƙwazo kamar yadda mu ke yi, don su ma wata rana za a kira su a ba su wannan karramawar, domin kafin a ba ni na san an bai wa waɗansu. Amma a wannan shekara ta 2023 Saratu Giɗaɗo (Daso) aka bai wa wannan babbar karramawa. Don haka su ci gaba da bada ƙwazo su ɗauki wannan sana’ar a matsayin sana’ar su, kada a ɗauke ta don neman suna, don ba a yin suna sai an zama gwarzo.

Sannan ina kira ga mutanen waje da su ke kallon mu duk waɗanda su ke zagin mu sudaina. Idan ka na kallon sana’ar mu a matsayin marar kyau, to kai ma a wajen wani taka sana’ar ba mai kyau ba ce, don haka mu rinƙa yi wa junan mu adalci mu na fatan Allah ya yi mana jagora.

FIM: To, madalla mun gode.

SARATU: Ni ma na gode.

Hajiya Saratu a zauren taron

Loading

Tags: Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso)lifetime award
Previous Post

Shekara 10 da aure: Ina fatan Allah ya kashe ni a ɗakin miji na – Fati Ladan

Next Post

Jarumin Kannywood Isma’il Koli zai angwance da Nasira

Related Posts

Ba faɗuwar zaɓen MOPPAN ta sa muka kafa ƙungiyar NEKAGA ba, inji Ability 
Tattaunawa

Ba faɗuwar zaɓen MOPPAN ta sa muka kafa ƙungiyar NEKAGA ba, inji Ability 

March 1, 2025
Za mu kawo sauyi ga matan Kannywood da tallafin NITDA, inji Mansurah Isah
Tattaunawa

Za mu kawo sauyi ga matan Kannywood da tallafin NITDA, inji Mansurah Isah

November 13, 2024
Bikin auren ‘ya’ya na ya ɗaga daraja ta – Aminu Ala
Tattaunawa

Bikin auren ‘ya’ya na ya ɗaga daraja ta – Aminu Ala

August 2, 2024
Buri na in samar wa MOPPAN tsarin shugabancin da za a riƙa tunawa da ni – Habibu Barde
Tattaunawa

Buri na in samar wa MOPPAN tsarin shugabancin da za a riƙa tunawa da ni – Habibu Barde

March 13, 2024
Mahaifiyar Afakallahu ta kwanta dama
Tattaunawa

Afakallahu: Abin da mahaifiyar mu ta karantar da mu

March 11, 2024
Gaskiyar abin da ya faru gare ni a haɗarin da na yi – Jarumar Kannywood Maryam CTV
Tattaunawa

Gaskiyar abin da ya faru gare ni a haɗarin da na yi – Jarumar Kannywood Maryam CTV

February 14, 2024
Next Post
Jarumin Kannywood Isma’il Koli zai angwance da Nasira

Jarumin Kannywood Isma'il Koli zai angwance da Nasira

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!