• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, July 30, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ban tsaya yawon maula ba bayan na bar ‘Ɗaɗin Kowa’, cewar Sallau

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
September 16, 2022
in Labarai
0
Malam Umar Sani Jigirya ('Sallau')

Malam Umar Sani Jigirya ('Sallau')

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FITACCEN jarumin Kannywood, Malam Umar Sani Jigirya, ya bayyana cewa ya ci gaba da harkokin sa a ɓangaren aikin rediyo bayan an cire shi daga diramar ‘Daɗin Kowa’ ta gidan talbijin na Arewa 24, inda ya riƙa fitowa da sunan Sallau.

Tun bayan da aka daina ganin sa a shirin, mutane dama sun yi ta tambayar ko ina ya shiga?

A tattaunawar da ya yi da mujallar Fim kan halin da ya ke ciki a yanzu, Jigirya ya nuna cewa ko kaɗan bai tagayyara ba bayan ya bar shirin.

Ya ce, “To shi da man shirin ‘Daɗin Kowa’ ba ni na samar da shi ba, na wasu ne da su ka samar da masu rubutun labari su ka rubuta masu, su ke ɗaukar ma’aikata kuma ni ma sai ya zama ina cikin wanda labarin ya kira ni, su ka ga na dace da shi su ka ɗauke ni a daidai lokacin da labarin ya kira ni. 

“Domin ai ka ga a farkon shirin ‘Daɗin Kowa’ babu Sallau, sai daga baya Sallau ya shigo, kuma ana tafiya Sallau ya je gaɓar da babu shi. Kusan sau biyu ko uku Sallau ya na tafiya ya na dawowa.

Sallau a gona

“To, wannan yanayi ne na labarin da su masu rubutun za su duba su ga a ina mutum ya dace ya fito, a ina ya dace a ajiye shi. Wani ma za ka ga kashe shi ake yi a labarin. To, duk yanayi ne ya ke zuwa da haka, don haka ko da an ga a yanzu babu Sallau a cikin shirin ‘Daɗin Kowa’, to labarin ne ya zo da haka.

“Ta yiwu kuma nan gaba labarin ya dawo da Sallau ko kuma ya tafi kenan.”

Dangane da ko a ina ya sa gaba a yanzu kuwa, sai jarumin ya ce, “To da man ni ina aikin jarida, don na yi aiki a gidan Rediyon Rahama, sannan na yi aiki a gidan Rediyon Arewa, sannan kuma kusan shekara talatin ni ɗan fim ne da na fara tun ana wasan daɓe.

“Don haka a yanzu ina yin harkokin da su ka shafi rediyo da fim da tallace-tallace. Kai, har ma siyasa ina yi tun a lokacin baya! Don haka ba na tsaya ba ne ina yawon maula. 

“Sannan akwai tashar TV ta YouTube da na buɗe, Jagora TV, da na ke saka finafinan da na yi. Kuma ana gayyata ta zuwa wasu finafinan.

“To ka ga ba za a ce an rasa inda aka dosa ba. Da man dai a rayuwa bai kamata a ce mutum ya tsaya ya na kallo da ido ɗaya ba, kamata ya yi mutum ya kalli ko’ina don ya gano idan babu wannan waje ina kuma zan yi amfani da damar da na samu. 

“Domin idan mutum ya yi amfani da damar da ya samu, to abin da zai samu a gaba ya fi kuɗin da za a biya shi idan ya yi aiki. 

“Don haka ni ina ganin wasu ne su ke wasa da damar su idan su ka samu, kuma idan ta tafi sai su rasa abin da ya kamata su yi.”

Jigirya ya yi kira ga ‘yan fim da su riƙa amfani da damar da ta zo masu, domin babu wani abu da ya ke ɗorewa.

Loading

Tags: aikin rediyoArewa24Daɗin KowaJagora TVRediyo RahamaRediyon ArewaSallauUmar Sani Jigirya
Previous Post

Rarara ya buɗe manhajar kallon finafinan Kannywood ta ‘Arewa Cinema’

Next Post

Dattijo ya sha alwashin rungumar ‘yan Kannywood na Kaduna idan ya zama sanata

Related Posts

Wani mai suna Bashir Abdullahi ya damfare ni miliyan bakwai da rabi, inji Halisa
Labarai

Wani mai suna Bashir Abdullahi ya damfare ni miliyan bakwai da rabi, inji Halisa

July 28, 2025
Gaskiyar magana kan ji-ta-ji-tar ‘mutuwar’ Aminu Ala
Labarai

Gaskiyar magana kan ji-ta-ji-tar ‘mutuwar’ Aminu Ala

July 28, 2025
KADIFF 2025: Uganda ta fi yawan finafinai a bikin baje-kolin na Kaduna – Israel Kashim Audu
Labarai

KADIFF 2025: Uganda ta fi yawan finafinai a bikin baje-kolin na Kaduna – Israel Kashim Audu

July 25, 2025
Karya dokar liƙi: Kotu ta ɗaure G-Fresh da Hamisu Breaker tsawon wata biyar-biyar
Labarai

Karya dokar liƙi: Kotu ta ɗaure G-Fresh da Hamisu Breaker tsawon wata biyar-biyar

July 24, 2025
‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar
Labarai

‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar

July 23, 2025
Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa
Labarai

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa

July 17, 2025
Next Post
Muhammad Sani Abdullahi (Dattijo), a tsakiya; a kusa da shi (daga dama) El-Mu'az Birniwa, daga (hagu), Alh. Ahmad Maiyaƙi, Baban Kausar da sauran 'yan fim a yayin ziyarar

Dattijo ya sha alwashin rungumar 'yan Kannywood na Kaduna idan ya zama sanata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!