SANANNEN mai ba da sutura kuma jarumi a Kannywood, Sadiqu Ahmad, wanda aka fi sani da Artist, shi ma lokacin aure ya yi, domin kuwa za a haɗa shi da masoyiyar sa Amina Aminu (Hajiya) a ranar Asabar, 27 ga Mayu, 2023.
Za a ɗaura auren su da misalin ƙarfe 11:00 na safe a masallacin Wudilawa da ke Titin Gidan Sarki, kusa da sakatariyar Municipal, a Birnin Kano.
Za a haɗu a bakin Hikima Multimedia, inda daga nan za a wuce wurin ɗaurin auren. Sannan akwai walima bayan ɗaurin aure, sai dai ba a bayyana inda za a yi ba.

Sadiqu Artist ya na ɗaya daga cikin mutanen da ake ganin cewa sun ƙi aure a Kannywood, kasancewar a baya ya yi soyayya da jaruma A’isha Tsamiya, wadda ta yi auren ta ta bar shi.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa a baya an sha kai ruwa rana tsakanin Artist da darakta Mu’azzam Idi Yari a kan ita A’isha Tsamiya ɗin, amma a ƙarshe duk su biyun babu wanda ya samu nasarar auren ta, wani ya laɓaɓo ya yi masu kwaf ɗaya.
Da ma Hausawa sun ce matar mutum kabarin shi.