• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, June 7, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

BBC Hausa za su bayyana gwarzuwar Gasar Hikayata ta 2022 a yau

by DAGA IRO MAMMAN
November 3, 2022
in Marubuta
0
Hagu zuwa dama: Hassana Labaran Ɗanlarabawa, Amira Souley da Maryam Muhammad Sani a ofishin BBC Hausa a Abuja (Hoto: Ibrahim Sheme)

Hagu zuwa dama: Hassana Labaran Ɗanlarabawa, Amira Souley da Maryam Muhammad Sani a ofishin BBC Hausa a Abuja (Hoto: Ibrahim Sheme)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A YAU Alhamis ne gidan rediyon Sashen Hausa na BBC zai bayyana sunan gwarzuwar Gasar Hikayata ta marubuta mata ta shekarar 2022.

Za a faɗi sunan ne a wani ƙwarya-ƙwaryan bikin bayar da kyaututtuka ga zakarun gasar wanda za a yi a ɗakin taro na Yar’Adua Centre da ke Abuja.

A taron, wanda za a fara daga ƙarfe 4 na yamma, za kuma a bayyana wadda ta zo ta biyu da wadda ta zo ta uku a gasar.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa Gasar Hikayata gasa ce ta rubutun gajerun labaran ƙirƙira ta marubuta mata zalla.

Gasar ta bana ita ce ta bakwai daga shekarar 2016 lokacin da BBC Hausa su ka fara shirya ta a kowace shekara.

Matasa uku – Hassana Labaran Ɗanlarabawa, Amira Souley da Maryam Muhammad Sani – su ne marubutan da su ka zo mataki na ƙarshe na gasar a bana. 

Maryam da Hassana matan aure ne daga Kano, yayin da Amira malamar makarantar firamare ce daga garin Maraɗi na Jamhuriyar Nijar.

Hassana ta zo matakin ƙarshe ɗin ne da labari mai taken ‘Haihuwar Guzuma’, Amira ta zo matakin da labari mai suna ‘Gudun Gara’ ko ‘Garar Biki’, yayin da Maryam ta kai matakin da labari mai suna ‘Al’umma Ta’.

Wannan shi ne karo na biyu da wata wadda ba ‘yar Nijeriya ba ta kai matakin ƙarshe a gasar domin a bara an samu Nana Aicha Hamissou Abdoulaye – ita ma daga Maraɗi – ta zama cikin zakaru uku na gasar.

Kamar dai zakarun gasar na bara, su ma waɗannan dukkan su marubuta ne masu yin yawancin rubutun su a intanet, waɗanda a turance ake kira ‘online writers’. Sai dai ita Hassana Ɗanrabawa ta buga wasu daga cikin littattafan ta. 

Mujallar Fim ta samu ganawa da zakarun uku a ofishin BBC da ke Abuja a jiya Laraba, inda kowacce ta bayyana farin cikin ta kan wannan nasara da ta samu.

A hirar, kowacce ta bayyana cewa ta taɓa shiga gasar a baya, amma sai a wannan karon ne Allah ya ba ta sa’a.

Maryam, wadda ‘yar shekara 27 ce kuma uwar ‘ya’ya uku, ta ce: “Alhamdu lillah. Na ji matuƙar daɗi. Ina jin abin tamkar a mafarki, tamkar ba gaske ba… Alhamdu lillah, na ji daɗi sosai da sosai, daɗin da baki ba zai furta shi ba.”

Amira kuma, wadda ‘yar shekara 24 ce, ta ce: “A gaskiya ba zan misalta farin cikin da na shiga ba.” 

Ta ƙara da cewa sai da ta yi wani mafarki inda ta ga Hassana Ɗanlarabawa da wata ‘yar Kano da kuma ɗaya wadda ba ta san ko wacece ba. Da yake a bara ma ta yi irin wannan mafarkin, kuma ya kasance gaskiya, to sai ta yi zaton a bana ma ba ta cikin zakarun gasar.

Amira ta ce: “Ina nan a zaune, ban tashi daga ko kan shimfiɗa ta ba, sai ga kira da nombar Nijeriya. Sai na ɗauka, gaba na ya na faɗuwa. Sai akai min albishir (da cewa) ina cikin gwaraza uku. Ni kai na ban san halin da na shiga ba. Ana cewa ana shudujul shukur, ni kuwa raka’atul shukur na yi!”

A nata ɓangaren, Hassana Ɗanlarabawa ta ce tun daga lokacin da BBC su ka bayar da sanarwar cewa labarin ta ya na cikin labarai 20 na farko da za a tsamo uku daga cikin su, ba ta yi sanyi da addu’a ba. Haka kuma kullum wayar ta a cikin caji ta ke saboda jiran tsammanin samun kira daga BBC.

Hassana, wadda ‘yar shekara 29 ce, ta ce: “To, kwatsam, ranar da za a kira nin, sai ya kasance ba ni da caji, sai na je na saka cajin, sai kuma na zo na zauna haka ina wasu abubuwa na, sai bacci ya ɗauke ni.

“Da bacci ya ɗauke ni, to ashe ma BBC sun kira ni, waya ta na ta ringin ban ɗaga ba, ni kuma ina nan ina ta bacci na.

“Sai can wajen azahar, yarinya ta ta dawo daga makaranta sai ta buga gida, sai na je na buɗe. Da na buɗe sai na ce bara na je na je na duba waya ta in gani.

“Ina dubawa, sai na ga ‘missed call’ haka na baƙuwar nomba. Ina gani, kawai sai na ji faɗuwar gaba, na ce to bara na bi wannan kira, ban sani ba ko alkhairi ne.

“To, ina bin kiran, kawai sai na ji murya, namiji ya ɗaga ya ce, ‘Assalamu alaikum. Usman ne daga Sashen Hausa na BBC; suna na Usman Minjibir.’ Wayar ta so ta faɗi daga hannu na saboda ina jin sunan sa ya ce daga BBC, to na tabbatar na samu nasara ne!”

A hirar su da mujallar Fim, gwarazan sun bayyana jigogin da labaran nasu su ka ƙunsa.

An gina labarin ‘Al’umma Ta’ na Maryam Muhammad Sani ne a kan jigon siyasa a ƙauye. A ciki, an bayyana irin gwagwarmayar da wata marainiya mai suna Hauwa’u (wadda a ƙauye ake kira Kululuwa) ta yi a ƙauyen su. Mace ce wadda ta yi karatu har zuwa matakin takardar shaidar malanta ta NCE. 

Kululuwa ta riƙa zuwa kafafen yaɗa labarai irin su rediyo da soshiyal midiya, ta na kambama ‘yan siyasa a kan cewa sun yi wa al’ummar ta kaza da kaza na cigaba ko da kuwa ba su yi ba, wanda hakan ya jawo ‘yan siyasar su ka riƙa zuwa su na yi wa ƙauyen irin waɗannan ayyukan. A ɓoye ta ke yin hakan, da sunan ƙarya da ta ba kan ta, wato Majadun Maijaki. 

Amma asirin ta ya tonu bayan ta yi kuskuren mantawa ta yi ɓad-da-kama a wani lokaci, wanda a ƙarshe ya janyo mata duka a wajen ‘yan banga.

Kululuwa ta ci gaba da gwagwarmaya har mutanen yankin su ka gaji da yaudarar da ‘yan siyasa su ke yi masu, inda a ƙarshe ta shiga takarar zaɓen ciyaman na ƙaramar hukumar su, kuma ta samu goyon bayan al’ummar ta, ta ci zaɓen. Abokin adawar ta ya garzaya kotu domin kai ƙara kan rashin amincewa da sakamakon zaɓen.

Ita kuma Hassana Ɗanlarabawa, jigon labarin ta na ‘Haihuwar Guzuma’

shi ne kwaɗayi irin na wasu iyaye mata a wajen aurar da ‘ya’yan su. Labarin ya hasko wata uwa wadda ta ke so yarinyar ta ta auri hamshaƙin attajiri kaɗai, bayan kuma shi uban yarinyar ba haka ya ke so ba.

A ƙarshe, aka samu wani mai alamun kuɗi aka yi auren da shi. To amma sai ya zo wa amaryar tasa da buƙatar kuɗi domin duk kuɗin sa sun ƙara a neman auren da biki, ga shi wai zai shiga wata harkar kasuwanci inda za a samu babbar riba.  

Ita kuma ta faɗa wa uwar ta. Mahaifiyar ta amince, ta ba da dukkan abin da ta mallaka, har ta haɗa da sayar da dukkan kadarar ta, su ka ba mijin kuɗin.

A daidai lokacin, wato wata uku da yin auren, sai yarintar ta samu ciki. Mijin ya kai ta asibiti, daga can ta wuce zuwa gida ta sanar da uwar ta. Ana ta murna an hau hanyar cin gado. Sai dai ta na komawa gida sai ta tarar mijin ya bar mata takardar saki uku, kuma ya kwashe kayan gidan ƙarƙaf, ya gudu. A takardar da ya bar mata, ya nuna mata cewa shi da ma can yaudarar ta ya yi. Ya ce gidan ma ba nasa ba ne, na haya ne, kuma komai da komai da aka yi, har da waliyyan sa, duk na bogi ne.

Shi ma labarin Amira Souley, wato ‘Gudun Gara’ ko ‘Garar Biki’ ya zo ne da jigon yaudara. An gina shi ne a kan yadda wasu iyaye mata su ka ɗauki garar biki da wani babban muhimmanci, su na yin ta bakin rai bakin fama saboda gudun gori. Wasu ma har bashi su ke ci domin su yi gara.

Amira ta zayyano yadda tauraruwar labarin, Fati, da uwar ta su ka dage kan sai sun yi gara ta kece raini idan bikin yarinyar ya zo. Ana nan aka kawo wa Fati da Hauwa, ɗiyar kawun ta, kuɗin aure.

Shi kuwa uban Fati, wanda ladani ne, ya ce ba zai yi wata gara ba.

Fati ta haɗu da Sani, wanda ya yaudare ta a kan ta riƙa tura masa hotunan tsiraicin ta, shi kuma ya na ba ta kuɗi. Ta amince.

Ana kwana uku bikin ta, sai ya yi mata barazanar ko dai ta je ta same shi su yi lalata ko ya saki hotunan nan da ta ke tura masa.

Har ƙoƙari ta yi mota ta banke ta ta mutu don kauce wa kunyar duniya, amma a banza. Tilas ta je ta kwana da shi ba a sani ba. 

A daren aka ɓalle ɗakin yayar ta aka sace kayan garar da uwar ta tara. Sani ya saki hotuna. Maganar aure ta watse. An ji kunyar da aka guda, an faɗa tsaka mai wuya tare da yin da-na-sani.

A cikin waɗannan labarai uku za a ji wanne ne gwarzo.

BBC Hausa kan bayar da tukwicin kuɗi ga gwarazan uku a kowace shekara.

Dama zuwa hagu: Maryam Muhammad Sani, Amira Souley da Hassana Labaran Ɗanlarabawa lokacin hirar su da mujallar Fim a ofishin BBC Hausa a Abuja (Hoto: Ibrahim Sheme)

Wakilin mu bai gano nawa ne za a bayar a bana ba, amma a bara an ba wadda ta zo ta ɗaya a gasar kyautar tsabar kuɗi dalar Amurka dubu biyu ($2,000) da lambar yabo; an ba wadda ta zo ta biyu dala dubu ɗaya ($1,000) da lambar yabo, sannan an ba ta uku kyautar dala ɗari biyar ($500) da lambar yabo.

BBC Hausa sun ce sun samar da Gasar Hikayata ne don ƙarfafa wa mata marubuta gwiwa da kuma haɓaka rubutu a harshen Hausa.

A bara, shugaban Sashen Hausa na BBC, Malam Aliyu Tanko, ya ce, “Gasar ta kasance wata turba ga mata marubuta wurin fito da batutuwan da su ka shafe su da zaƙulo hanyoyin matsalolin da su ke fuskanta. Kuma mu da ma fatan mu kenan.”

Gwarazan Gasar Hikayata na shekaru shida da su ka gabata dai su ne kamar haka:

2016 – A’isha Mohammed Sabitu

2017 – Maimuna Sani Idris Beli

2018 – Safiyya Jibril Abubakar

2019 – Safiyya Ahmad

2020 – Maryam Umar

2021 – Aishatu Musa Dalil

A yammacin yau za a ji wadda za ta shiga wannan jerin a bana.

A wata sabuwa, a bikin na yau kuma BBC Hausa za su bayyana gwarzon mawaƙin da ya lashe gasar yi wa Sashen Hausa na BBC waƙa cikar sa shekara 65 da kafawa.

Wannan shi ne karo na farko da gidan ya shirya gasar mawaƙan Hausa.

Wakilin mu ya samu labarin cewa Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau, masanin waƙar baka ta Hausa wanda ya yi ritaya daga Jami’ar Bayero, Kano, kwanan baya, shi ne jagoran alƙalan gasar mawaƙan.

Haka kuma an ce wani masanin waƙar baka ɗin, Farfesa Muhammad Bunza, zai gabatar da maƙala kan maudu’in waƙa a taron.

Haka kuma mujallar Fim ta samu labarin cewa fitacciyar mawaƙiyar nan da ke Kaduna, Khairat Abdullahi, za ta nishaɗantar da taron da waƙar da ta yi wa Sashen Hausa na BBC a kan cikar sa shekara 65.

Loading

Previous Post

Amira Souley, ‘yar shekara 24, ta lashe Gasar Hikayata ta BBC Hausa ta 2022

Next Post

Hotunan ‘auren’ Daushe da Zarah sun tayar da ƙura a ciki da wajen Kannywood

Related Posts

Gasar rubutu: Ba a taɓa ba marubutan Hausa dama irin wannan ba – Balannaji 
Marubuta

Gasar rubutu: Ba a taɓa ba marubutan Hausa dama irin wannan ba – Balannaji 

January 1, 2025
Zubairu Balannaji ya zama gwarzon gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

Zubairu Balannaji ya zama gwarzon gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai

December 31, 2024
‘Dakan ɗaka…’: Kanawa sun lashe gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

‘Dakan ɗaka…’: Kanawa sun lashe gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai

December 20, 2024
Mutane 15 sun yi nasarar zuwa zagayen kusa da na ƙarshe a gasar rubutu na Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

Mutane 15 sun yi nasarar zuwa zagayen kusa da na ƙarshe a gasar rubutu na Hukumar Tace Finafinai

November 30, 2024
Tsakanin matan aure biyu da budurwa ɗaya za a san gwarzuwar gasar Hikayata ta 2024 a yau
Marubuta

Tsakanin matan aure biyu da budurwa ɗaya za a san gwarzuwar gasar Hikayata ta 2024 a yau

November 27, 2024
Ƙungiyar matasa da mata za ta naɗa Ado Gidan Dabino Sarkin Mawallafan Arewa
Marubuta

Gasar rubutu: Hukumar Tace Finafinai ta bayyana gwaraza 50 na zagayen farko

November 24, 2024
Next Post
Rabi'u Ibrahim (Daushe) da Zarah Muhammad (Diamond)

Hotunan 'auren' Daushe da Zarah sun tayar da ƙura a ciki da wajen Kannywood

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!