KAMAR dai yadda aka saba, wannan karon ma wasu hotunan kafin aure (pre-wedding pictures) na wasu jaruman Kannywood sun bayyana a soshiyal midiya.
Da yammacin yau Alhamis, darakta Falalu A. Ɗorayi ya ɗora hotunan a shafin Fezbuk da Instagram, ya kuma rubuta, “Allah ya sanya alkairi, ya nuna mana lokacin. Rabi’u Ibrahim Daushe @realdaushe & Zarah Muhd Diamond @diamond_zarah___
#GidanBadamasi
#GidanBadamasiSeason5″.

Kamar yadda aka gani dai, jarumin barkwanci Rabi’u Ibrahim Daushe da jaruma Zarah Muhammd, wadda aka fi sani da Diamond Zarah, su ne a hotunan, waɗanda sun kai kala biyar.
Ɗora hotunan a soshiyal midiya ke da wuya, sai mutane su ka yi caa da tambayoyi. Wasu daga cikin su sun gane ina aka dosa, wasu kuma tambaya su ke yi idan auren gaske ne za su yi.
Ga dukkan masu kallon shirin ‘Gidan Badamasi’ a tashar talbijin ta Arewa 24, inda Daushe ya fito a matsayin Alhaji Adnanu tare da jaruma Hadiza Gabon a matsayin matar sa, ana kiran ta da Hajiya Tani, waɗannan hotuna su na nuni da cewa Alhaji Adnanu zai yi wa Hajiya Tani kishiya ne.

Idan kun tuna, a kwanan baya ma daraktan ya ɗora irin waɗannan hotunan jarumai biyu, Umar Gombe da Hauwa Ayawa, wanda su ma duk a cikin shirin su ke.
Wannan ba sabon abu ba ne a Kannywood.
Daushe da Zarah dai ba auren gaske za su yi ba, aure ne a cikin shirin ‘Gidan Badamasi’.
![]()







