JARUMAR Kannywood Amal Umar ta roƙi wata kotu a Kano da ta hana kwamanda mai kula da shiyya ta 1 ta Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya da ke Kano da kwamishinan ‘yan sanda na jihar da jami’in ‘yan sanda mai bincike su kama ta da su ke ƙoƙarin yi.
Tun da farko dai wani mutum mai suna Alhaji Yusuf Adamu ne ya shigar da ƙarar wani saurayin Amal mai suna Ramadan bisa zargin ya ba shi kuɗi naira miliyan 40 domin ya gudanar da kasuwancin waya kuma kuɗin su ka salwanta.
Ya gurfanar da shi ne a Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 17.
Bayan an kai shi kotu, saurayin jarumar ya shaida wa alƙali cewa a cikin kuɗin da aka ranta masa ɗin ya buɗe wa Amal kanti ya zuba mata kaya na naira miliyan 5, kuma ya saya mata ƙatuwar mota, sannan ya biya wa mahaifin ta naira miliyan 3 domin biyan wata buƙata tasa.
A kan haka ne ‘yan sanda su ka kama Amal, kotu ta tsare ta na ɗan wani lokaci, kuma ta karɓe motar.
A zaman kotun na jiya Alhamis, 3 ga Nuwamba, 2022, lauyan mai ƙara, Sulaiman Usman, ya nemi da a ba su wata rana domin kawo ƙarin wasu hujjojin da su ke da su a game da shari’ar, inda kotun ta amince, kuma ta ɗage sauraren shari’ar zuwa ranar 16 ga Disamba, 2022.
Bayan ta samu beli, daga baya sai Amal ta shigar da ƙara ta hannun lauyar ta, Adama Usman, a kan ta na neman kotun ta hana jami’an ‘yan sanda su kama ta har zuwa ranar da za a koma kotun, wato abin da ake kira ‘injunction’.