• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Aure: Isma’il Afakallah da Ruƙayya Dawayya sun zama ɗaya

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
November 4, 2022
in Ranar Murna
0
Ango Isma'il Na'abba (Afakallah) da amarya Ruƙayya Umar Santa (Dawayya)

Ango Isma'il Na'abba (Afakallah) da amarya Ruƙayya Umar Santa (Dawayya)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ABIN nan da Hausawa ke kira dakan ɗaka shiƙar ɗaka ya faru a yau lokacin da aka ɗaura auren Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Malam Isma’il Na’abba (Afakallah), da shahararriyar jaruma kuma furodusa, Hajiya Ruƙayya Umar Santa (Dawayya).

An ɗaura auren su da misalin ƙarfe 2 na rana a yau Juma’a, 4 ga Nuwamba, 2022 a Masallacin Juma’a na unguwar Tishama a Kano a kan sadaki N100,000, wanda aka biya lakadan.

Ɗimbin jama’a na ciki da wajen masana’antar shirya finafinai ta Kannywood sun halarci taron.

Da ya ke gabatar da huɗubar auren, Limamin masallacin, Sheikh Mohammed Jabir, ya hori jama’a da su riƙa kiyaye haƙƙoƙin aure, musamman ma a wannan lokacin da al’umma ta samu kan ta a cikin wani mawuyacin hali. 

Afakallah da mahaifiyar amarya da kuma amaryar sa

Haka kuma ya yi kira ga ma’aurata da su riƙa kai zuciya nesa a cikin zamantakewar aure. Daga nan ne sai ya ɗaura auren Isma’il da Ruƙayya.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa an daɗe ba a ga irin wannan taron ɗaurin auren ba wajen tara jama’a a Kannywood. Wurin ya zama taron sada zumunci da aka daɗe ba a ga juna ba.

‘Yan fim da su ka halarci taron sun haɗa da Adamu Sani, Auwalu Isma’il Marshal, Sani Sule Katsina, Baba Ƙarami, Ado Ahmad Gidan Dabino, Alhassan Kwalle, Alhaji Musa Maikaset, Nura Hussaini, Salisu Officer da sauran su.

Bayan an kammala addu’ar auren, sai mahalarta taron su ka raka ango zuwa gidan su amarya domin gaisuwar surukai. 

Abin sha’awa shi ne an yi tafiyar ne a ƙasa daga masallacin zuwa gidan, kuma tafiyar ta ɗauki hankalin jama’ar unguwar ta Kawon Lambu, ta kuma tabbatar da cewa Ruƙayya da Isma’il mutane ne masu jama’a masoya.

A gidan su amarya, an shirya wata ƙwarya-ƙwaryar walima inda mahalarta su ka ci abinci tare da abin sha.

A lokacin da ya ke tattaunawa da mujallar Fim, ango Afakallahu ya nuna farin cikin sa da Allah ya nuna masa wannan rana ta ɗaurin auren sa da Ruƙayya. 

Sannan ya yi godiya ga dukkan jama’ar da su ka halarci ɗaurin auren.

Ango da abokan arziki a wajen ɗaurin auren

Shi dai wannan aure, ba kowa ba ne ya san za a yi shi saboda yadda ma’auratan su ka ja bakin su su ka yi gum a kan shi, har sai da mujallar Fim ta fara ba da labarin soyayyar Afakallah da Dawayya, daga nan duk duniya ta ɗauka. To ga shi Allah ya kawo wannan rana.

Mu na fatan Allah ya ba su zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Ango tare da su Ado Gidan Dabino da Jamilu Ibrahim Home Alone da sauran masoya
Ango Afakallah tare da Abubakar Bashir Maishadda da sauran mahalarta ɗaurin auren
Ango da amarya tare da abokan arziki a gidan su amarya
Ango a tsakanin ‘yan’uwan amarya
Amarya da ango a gidan su amarya

Loading

Tags: censors boardDawayyaɗaura aureHukumar Tace FinafinaiIsmail Na'abba Afakallah.KannywoodKanoKawon LambuRuƙayya Umar SantaSheikh Mohammed JabirsoyayyaTishamawalima
Previous Post

An maka saurayin jaruma Amal Umar a kotu bayan ya kashe miliyoyin naira da ya ranto a kan ta da mahaifin ta

Next Post

INEC ta gargaɗi sababbin kwamishinonin zaɓe da su nisanci ‘yan siyasa ko shiga gidan gwamnati

Related Posts

Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji
Ranar Murna

Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji

August 24, 2026
An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki
Ranar Murna

An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki

August 23, 2026
Uwargida na ce ta biya sadakin aure na da amarya ta – darakta Aminu Saira
Ranar Murna

Uwargida na ce ta biya sadakin aure na da amarya ta – darakta Aminu Saira

August 2, 2026
Bikin auren darakta Aminu Saira a Azare ya ja hankalin jama’a
Ranar Murna

Bikin auren darakta Aminu Saira a Azare ya ja hankalin jama’a

July 31, 2026
An taya Aisar, jikar marubuciya Sadiya Garba Yakasai, murnar cika shekaru 5
Ranar Murna

An taya Aisar, jikar marubuciya Sadiya Garba Yakasai, murnar cika shekaru 5

July 15, 2026
Jarumin Kannywood Tijjani Faraga ya aurar da ‘yar sa ta biyu
Ranar Murna

Jarumin Kannywood Tijjani Faraga ya aurar da ‘yar sa ta biyu

July 12, 2026
Next Post
Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban INEC, ya na gabatar da jawabi ga sababbin kwamishinonin zaɓen da ya rantsar

INEC ta gargaɗi sababbin kwamishinonin zaɓe da su nisanci 'yan siyasa ko shiga gidan gwamnati

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!