• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Buhari ya naɗa shugabannin Hukumar Naƙasassu

by DAGA WAKILIN MU
August 25, 2020
in Nijeriya
0
Buhari ya naɗa shugabannin Hukumar Naƙasassu
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
SHUGABAN Ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa shugabannin sabuwar Hukumar Kula Da Naƙasassu ta Ƙasa, wato National Commission for Persons with Disabilities, kamar yadda Dokar Hana Wariya Ga Naƙasassu ta 2019 ta tanadar.
 
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Mista Femi Adesina, shi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya bayar a ranar Litinin.
 
Hukumar za ta kasance ne a ƙarƙashin Ma’aikatar Harkokin Agaji tare da Jinƙai ta Tarayya inda a yanzu Hajiya Sadiya Umar Faroukh ta ke minista.
 
Dokar dai ta tanadi cewa za a samar da shugaba tare da membobi shida waɗanda dukkan su naƙasassu ne daga sassan ƙasar nan guda shida waɗanda za su jagoranci Majalisar Gudanarwar hukumar na tsawon shekara huɗu, kuma za a iya ƙara masu wa’adin shekara huɗu na ƙarshe, tare da amincewar Majalisar Dattawa.
 
Haka kuma dokar ta ce za a naɗa Babban Sakatare, wanda ke ƙarƙashin Majalisar Gudarwar, don aiwatar da ayyuka da tsare-tsaren hukumar, wanda kuma shi ma tilas ya kasance naƙasasshe ne, kuma zai yi wa’adin shekara biyar, sannan za a iya daɗa masa wa’adin shekara biyar na ƙarshe.
 
Sanarwar daga fadar shugaban ƙasa ta bada sunaye da muƙaman waɗanda aka naɗa da kuma yankin da su ka fito, kamar yadda shugaban ƙasan ya amince. Su ne kamar haka:
 
Hon. Dakta Hussaini Suleiman Kangiwa – Shugaba – daga Arewa-Maso-Yamma
 
Oparaku Onyejelam Jaja – Memba – Kudu-maso-Gabas
 
Philomena Isioma Konwea – Memba – Kudu-maso-Kudu
 
Omopariola Busuyi Oluwasola – Memba – Kudu-maso-Yamma
 
Amina Rahma Audu – Memba – Arewa-maso-Yamma
 
Mrs Esther Andrew Awu – Memba – Arewa-ta-Tsakiya
 
Abba Audu Ibrahim – Memba – Arewa-maso-Gabas
 
James David Lalu – Babban Sakatare – Arewa-ta-Tsakiya

Loading

Previous Post

Matsala ta da manema aure na – Shalele Umar

Next Post

Bikin Finafinai na Kaduna ya kankama ta hanyar intanet

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Shugaban Kaduna International Film Festival, Mista Kashim Audu Israel, da daraktar bikin, Hajiya Zainab Ahmad

Bikin Finafinai na Kaduna ya kankama ta hanyar intanet

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!