ADAM A. Zango jarumi ne wanda ya ke kan sahun gaba na ‘yan fim. Hasali ma dai in ka debe Ali Nuhu babu dan wasa kamar sa. Wasu ma sun dauka ya kere Alin a fagen jarumtaka. Kai, za ma a iya cewa in dai harkar fim ce, to Zango ya yi wa Ali tazara saboda a yayin da ya ke yin duk abin da Ali ke yi, shi Ali akwai abin da Zango ke yi wanda ba ya yi: waka. A fagen wakar ma, Zango ya na cikin sahun gaba. Ya yi fayafaye (album) masu tarin yawa, na kallo da na ji.
To amma duk da nasarorin da ya samu, Adamu ya na daga cikin ‘yan fim da ake wa wani kallo. Da bakin sa ya taba fada wa jaridar Leadership Hausa cewa kashi 90 cikin dari na ‘yan fim ba su son shi. Shin me ya sa? Haka kuma ya taba yin sabani da mujallar Fim har abin ya kai gaban ‘yan sanda, aka rabu dutse a hannun riga. Amma yanzu an shirya, sai jajantawa!
Kwanan nan, Adam A. Zango ya lashe gasar zama Jarumin Jarumai na bana wanda mijallar Tozali ta ke shiryawa a dik bayan shekara biyu. Jamila Umar Nagudu ta lashe gasar zama Jarumar Jarumai a bikin, wanda aka yi a katafaren wajen taro na International Conference Centre, a Abuja ran Asabar, 8 ga Oktoba, 2016.
Bayan taron, mujallar Fim ta tattauna da Zango inda ya bayyana farin cikin sa. Haka kuma ya yi tsokaci kan rantsuwar kaffara da ya yi kan masu cewa akwai ‘yan luwadi da ‘yan madigo a industiri, da batun film billage, abubuwan da ya koya a tafiye-tafiyen da ya yi a wasu kasashe, da batun batawar sa da wannan mujallar, da sauran su. Wannan tattaunawa dai ta kafa tarihi, domin ta nuna cewa Adamu da mujallar Fim sun dinke barakar su, kuma za su hada karfi da karfe don ciyar da harkar fim gaba. ASHAFA MURNAI BARKIYA, wanda ya taba rike mukamin Editan mujallar Fim, shi ne ya zanta da Adamun a harabar zauren taron bikin karramawa na Tozali a Abuja jim kadan bayan an gama bikin.
FIM: Adamu, mujallar Fim na taya ka murnar lashe kyautar Tozali Awards ta Gwarzon Jarumi na Kannywood da ka yi a nan Abuja.
ZANGO: Ni ma ina godiya kwarai da har Mujallar Fim ta taya ni murnar wannan nasara da na yi.
FIM: Wane irin kwarin gwiwa wannan kyauta za ta kara maka?
ZANGO: Ta kara min kwarin gwiwa kwarai, don za ta sa na kara hazaka ko watakila wata shekara mai zuwa ma na sake yin nasara. Kuma irin wannan muhimmiyar kyauta za ta kara wa ‘yan fim tsara na da wadanda su ka zo daga baya na kwarin gwiwa domin su ma su ga sun kai fagen samun irin wadannan kyaututtuka. Lallai wannan ta na daya daga cikin manyan awards da ake yi a arewacin kasar nan wadda kowa ke kwadayin ya ga ya samu. Ni dai Allah Ya ci da ni a wannan shekarar, kuma zan kara sa rai watakila idan Allah Ya nufa na sake lashewa a shekara mai zuwa. Idan kuma wani Allah ya ba, to Allah Ya ba mai rabo nasara!
FIM: A cikin shekarun nan kusan kai ne a sahun gaba wajen kara samun karbuwa da kuma nasibi. Wace irin dangantaka ka ke da ita da jarumai, furodusoshi da kuma sauran ‘yan fim?
ZANGO: Gaskiya ina da kyakkyawar dangantaka da kowannen su. Kuma hakan ya sa a yanzu abubuwa na su ke tafiya lafiya yadda ya kamata, kamar yadda ku ma ku ka shaida. A baya an samu matsaloli tsakani na da wasu, amma yanzu kakaf a masana’antar fim ba ni da abokin gaba, ba ni da abokin rigima. Kowa nawa ne, kuma ni na kowa ne a tsakani na da ‘yan fim.
FIM: Kwanan nan na ga wani bidiyo da aka nuno ka ka je ganin gida a Zango, jama’a sun kewaye ka. Shin a baya ayyukan ka kan hana ka zuwa ganin gida ne?
ZANGO: Ba shakka kwanan nan na je ganin gida, kuma a gaskiya a baya yanayin aiki na kan hana ni zuwa gida. Ko me za a yi ma a cikin dangin mu ban a samun damar halarta. Kai, ko a gida na ma su kan dauki lokaci kafin su gan ni. Amma daga shekara biyu zuwa yanzu, na gyara wannan al’amarin. Ina da lokacin iyali na, ina da lokacin halartar duk wata gayyata da aka yi min domin halartar wasu lamurra ko biki na ‘yan’uwa da abokan arziki, ko ta’aziyya inda duk ta kama.
Ai ka ga kwanan nan na tashi na je har Zangon Kataf garin mu, na kai ziyara, daga can na wuce wasu garuruwan, har Doka, domin sada zumunci tsakanin ‘yan’uwa da abokan arziki.
FIM: Wace irin karba su ka yi maka a wannan ziyara da ka kai?
ZANGO: Gaskiya sun karbe ni hannu biyu-biyu. Wasu yaran ma a lokacin da na bar garin ba a haife su ba, su ma tashi kawai su ka yi su ka rika jin ana cewa ni dan’uwan su ne, amma sai a wannan lokacin su ka fara gani na.
FIM: A cikin ‘yan shekarun nan ka je kasashe da dama duk a dalilin fim. Me ka koyo kuma me ka gano wanda aka ke ganin ya kamata ka yi magana a kan sa?
ZANGO: Babban abin da zan fada shi ne, a gaskiya ba a son ‘yan fim din Hausa a Nijeriya, an fi son su a kasashen waje. Inda mu ke dan lekawa can ne su ka fi alfahari da mu, su ka fi jin dadin abin da mu ke yi kuma su ka yarda cewa abubuwan da mu ke yi mu na tarbiyyantar da ‘ya’yan su da al’adar mu da kuma addinin mu. Amma ba kamar nan ba da kowane lokaci zagin mu ake yi. Kuma a gaskiya ina jin kwarin gwiwa yadda idan na shiga kasashen Afrika ake nuna min na ci gaba da abubuwan da na ke yi na jaddada al’ada da fadakarwa. Ni da ma ba na yin abubuwan da su ka saba wa addini. Ina yin fim don abubuwa uku: Na farko don sana’a, na biyu ina kokarin in ga na fadakar, sai na uku kuma ina kokarin in ga na nishadantar.
FIM: Kwanan baya wata wuta mai harshe biyu ta tunkari masana’antar fim gadan-gadan, kuma kowace sai da ka fito ka yi magana a shafin ka na Instagram. Me ya yi zafi sai aka gan ka har da dora Alkur’ani a ka, ka na rantsuwa?
ZANGO: Wadannan abubuwa da su ka faru dai na farko akwai magana a kan Film billage da aka yi, inda na fito na ce duk dan fim din da bai fita a soshiyal midiya ya yi zanga-zanga ba, to munafiki ne. Abin da ya sa na fadi haka kuwa, babu abin da wasu ‘yan fim din su ke yi a soshiyal midiya sai su ci kwalliya kawai su na daukar hoto su na turawa don su nuna cewa su wasu ‘yan gayu ne. To amma ga wani ci-gaba ya zo, kuma ana nema a wargaza mu, a hana mu wannan ci-gaban. To kuma wai sai kowa ya nade hannun sa, ba zai fito ya fadi albarkacin bakin sa ba. Ba wanda aka ce ya fito ya yi wata rashin kunya, amma ga abin alheri ya samu, ana neman a hana. To ka fito ka nuna kai ma ka na bakin ciki da haka kan wannan abin alheri da ake kokarin a yi mana. Abin da na fito na nuna kenan.
Abu na biyu kuma da ya sa na dora Alkur’ani a kai na na yi wannan rantsuwa shi ne saboda ana yi mana jama’u cewa mu ‘yan luwadi ne, ana ce wa matan mu ‘yan madigo ne, wanda ni a masana’antar fim babu ko mutum daya da zan iya shaida dan luwadi ne ko ‘yar madigo ce ko mazinaci ne. Wannan dalili ne ya sa na fito na nuna wa duniya cewa ni ba dan luwadi ba ne, ban taba yi ba, ba a taba yi da ni ba, kuma ban san masu yi ba. Ni ban ce babu abin da ake zargi ba, amma dai ni na fito na ce ba na yi kuma ban san masu yi ba.
Kuma na yi haka ne saboda in wanke wa masoya na zuciyar su, su san cewa ni da su ke so din nan ba na yin wadancan abubuwa da ake magana a kai. Kuma ban damu da duk abin da mutane za su fada ba, na yi haka ne don masoya na.
FIM: Da farko a situdiyo aka fara sanin ka ka na buga waka, ga shi dalilin rikidewar ka fim ka yi shaharar da yanzu ana yi maka kallon daga Ali Nuhu sai kai, wasu na cewa kankankan ku ke, wasu ma cewa su ke yi ka maye gurbin Ali Nuhu. To kai ya ka ke jin kan ka a yanzu?
ZANGO: Duk abin da masoya na za su fada, ni ba zan ga laifin su ba. Amma dai ni har yanzu ban dauki kai na wanda ya fi Ali Nuhu ba. Ko da a yau Ali ba ya cikin masana’antar fim, ba zan tabbatar da kai na a sama da shi ba. Ali Nuhu ya yi min komai, kuma ya taimaka wa rayuwa ta tun daga farko har zuwa yanzu. Don haka idan masoyi na ya ce na fi Ali Nuhu, babu yadda zan yi da shi. Haka shi ma Ali idan masoyan sa su ka ce ya fi Zango, ba yadda zai yi da su. Wannan ra’ayin masoya ne masu kallon finafinai. Amma ni a kankin kai na ban taba dora kai na a kan Ali Nuhu ba.
FIM: Tambaya ta karshe, dan fim da dan jarida duk al’umma su ke kallo su na bayyana halin da al’ummar ke ciki – ko halin kwarai ko na aibi. Sai ga shi can baya sabani ya shiga tsakanin ka da mujallar Fim. Ya haka ta kasance?
ZANGO: To ni dai ban taba samun sabani da wani dan mujallar Fim ba bayan Aliyu Gora. To sai ya kasance Aliyu Gora ko in ce Fim, duk wani abin alheri da na yi ko na samu, ba su bugawa. Amma da na yi wani kuskure ko na aikata wani abu ba daidai ba, za su yi sauri su buga. To a gaskiya wannan abin bai yi min dadi ba.
Ni kuma sai na ga idan har za a buga aibi na me ya sa ba za a buga ci-gaba na ba ko alherin da na samu? Sai na ce tunda haka ne, a daina shirin, ba za a nemi ni a same ni ba ballantana har a yi hira da ni. Ai an sasanta mu ni da Gora har maganar ta wuce. Daga lokacin ba a daina buga wani abu a kai na ba.
Amma kowane lokaci girma ake yi. Ko a wancan lokacin ma akwai yarinta a tattare da ni. Don haka na gano cewa ita daukaka dole sai ka yi hakuri da duk abin da za a fada a kan ka, ka toshe kunnen ka, ba ka ji ba; ka rufe idon ka, ba ka gani ba. Wannan ce ta sa na daina rigima da ‘yan jarida (dariya).
FIM: To Zango, Fim ta gode.
ZANGO: Godiya mujallar Fim (dariya).