• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Cewar Minista: Gwamnatin Tinubu ba za ta daƙile ‘yancin aikin jarida ba

by WAKILIN MU
May 3, 2024
in Nijeriya
0
Cewar Minista: Gwamnatin Tinubu ba za ta daƙile ‘yancin aikin jarida ba

Alhaji Mohammed Idris ya na jawabi a taron

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAN Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya tabbatar da cewa babu wani ɗan jarida ɗaya da aka kama ko aka ɗaure a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu saboda gudanar da aikin jarida yadda ya kamata.

Ya jaddada cewa kafafen yaɗa labarai suna da cikakken ‘yanci a Nijeriya.

Idris ya faɗi haka ne a yayin da ya ke amsa wata tambaya a wani taron manema labarai da ma’aikatar sa ta shirya tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Kula Da Muhalli ta Tarayya da kuma Hukumar Ilimi da Kimiyya ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO), domin tunawa da Ranar ‘Yancin ‘Yan Jarida ta Duniya ta bana wanda aka yi a Abuja ranar Juma’a.

Ya ce: “A zamanin wannan gwamnatin, a misali, ban ga wani mutum wanda aka ɗaure ko kuma ya yi gudun hijira sakamakon ‘yancin aikin jarida ba.

“Mun san abin da ya faru a ƙasar nan a baya. A wasu shekarun da suka gabata, mun san cewa dole ne ku bar ƙasar nan don samun damar ba da rahoto. Zan iya gaya muku cewa ‘yan jarida a Nijeriya suna da ‘yanci amma za a iya ƙarfafa ‘yancin ne idan aka tabbatar da gaskiya ta hanyar da muke kawo rahoto.”

Daga hagu: Mai ba Shugaban Ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabaru, Mista Bayo Onanuga; Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Dakta Ngozi Onwudiwe; Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris; Ƙaramin Ministan Muhalli, Dakta Iziaq Adekunle Adeboye Salako, da Shugaban Ofishin UNESCO na Abuja, Mista Abdourahamane Diallo, a wajen taron

Ministan ya ce Shugaban Ƙasa Tinubu ya fahimci muhimmancin yaɗa labarai yadda ya kamata wajen wayar da kai, faɗakarwa, da ilimantar da ‘yan Nijeriya da duniya baki ɗaya, inda ya ƙara da cewa ta hanyar ba da sahihan bayanai a kan lokaci za a iya faɗakar da kowa sosai, kuma kafafen yaɗa labarai na iya zama makami mai ƙima na bunƙasa gaskiya da riƙon amana.

“A matsayin mu na Ma’aikata da Gwamnati, mun ba da dama ga ‘yan jarida ba tare da wata matsala ba kuma mun samar da yanayi mai dacewa wanda ya ci gaba da ƙarfafa wa kafafen yaɗa labarai na Nijeriya ƙwarin gwiwa don bunƙasa,” inji shi.

Ministan ya tunatar da kafafen yaɗa labarai cewa yaɗa labarin ƙarya bai dace da aikin jarida ba kuma ba za a iya kwatanta shi da ‘yancin jarida ba.

Ya ce yayin da Shugaba Tinubu ke ƙoƙarin ganin Nijeriya ta zama wata ƙasa mai jan hankali wajen zuba jari kai-tsaye daga ƙasashen waje, dole ne kafafen yaɗa labarai su gabatar da kyakkyawan bayanin ƙasar ga ƙasashen duniya.

Yayin da ya ke magana kan taken Ranar ‘Yancin ‘Yan Jarida ta Duniya na bana, wato ”Jarida ta Duniya: Aikin Jarida a yayin da ake fuskantar Matsalar Muhalli,” Idris ya ce duniya na fuskantar matsalar muhalli mai girman gaske wanda ba a taɓa ganin irin sa ba, wanda ke haifar da barazana ba kawai ga duniya ba amma ga makomar bil’adama.

Ya ce sauyin yanayi, asarar rabe-raben halittu, gurɓacewar yanayi, da ƙarewar albarkatu munanan abubuwa ne da ke buƙatar ɗaukar matakin gaggawa kan wayar da kan jama’a.

Ya ce, “Mu yi imani da cewa ‘yancin ‘yan jarida ba wai kawai haƙƙin ɗan’adam ba ne; ya na da muhimmanci don ɗorewar muhalli. Idan babu ‘yan jarida masu ‘yanci da zaman kan su, ba za mu iya fatan magance matsalolin muhalli da mu ke fuskanta ba.

“Yaɗa labaran ƙarya yana lalata fahimtar jama’a game da matsalolin muhalli kuma yana hana mu damar ɗaukar matakai masu ma’ana.

“Don haka dole ne mu tsaya tsayin daka wajen kare ‘yancin ‘yan jarida tare da tallafa wa ayyukan ‘yan jarida masu sadaukar da kai wajen bayar da labarin gaskiya.”

Mahalartan taron

Taron ya samu halartar Ƙaramin Ministan Kula da Muhalli, Dakta Iziaq Adekunle Salako; Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Mista Bayo Onanuga; Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Watsa Labarai Da Wayar Da Kai, Dakta Ngozi Onwudiwe; Shugaban Ofishin UNESCO na Abuja, Mista Abdourahamane Diallo, da shugabannin hukumomin Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai da kuma Ma’aikatar Kula da Muhalli.

Loading

Tags: 'yan jaridaAlhaji Mohammed Idris Malagigwamnatin Tinubu
Previous Post

Haihuwa ta 10: Mawaƙi Sanusi Anu ya samu A’ishatul Humaira

Next Post

Ƙungiyar tsofaffin jarumai mata masu aure ta karrama Rarara

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Ƙungiyar tsofaffin jarumai mata masu aure ta karrama Rarara

Ƙungiyar tsofaffin jarumai mata masu aure ta karrama Rarara

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!