INNA lillahi wa inna ilaihir raji’un! A rana mai kamar ta yau, wato ranar 18/06/99 ne Allah SWT ya ɗauki ran Alhaji Dakta Mamman Shata, wani shahararren mawaƙi da ya shafe sama da shekaru sittin ya na rera waƙoƙi a fage daban-daban da ya shafi rayuwar al’umma. Zan so in yi amfani da wannan dama don yi masa addu’a tare da fatan Allah ya gafarta masa dukkan kurakuran shi kuma ya yi masa masauki a gidan Aljanna.
WASU MUHIMMAN BAYANAI 22 DANGANE DA SHATA
1. Shata ya rasu ranar Juma’a, 18/06/99 a Asibitin Malam Aminu Kano da misalin ƙarfe 11:30 na dare.
2. Shata ya rasu ya na da shekaru 76 a duniya.
3. Shata bai bar wasiyyar a rufe shi a garin Daura ba. Kusanci da soyayya da ke tsakanin su da marigayi Sarkin Daura Muhamnadu Bashar ta sa ɗiyar shi, Barrister Jamila Shata, wadda ita ce ke tare da shi lokacin da ya rasu, ta ɗauke shi ta kai shi Daura kuma aka yi masa sutura a can.
4. Shata ya rasu ya bar matan aure uku:
1. Hajiya Furera (Ta rasu)
2. Hajiya Hadiza (Ta-Falgore)
3. Hajiya Amina (Ta-Dukke)
5. Shata ya bar ‘ya’ya 20, guda 9 maza guda 11 mata:
a. Lawal Shata (Magaji)
b. Mamuda Shata (ya rasu a 2017)
c. Aminu Shata
d. Salisu Shata
e. Nura Shata (ya rasu a 2016)
f. Sagir Shata (Bala)
g. Bishir Shata
h. Muntari Shata
i. Sunusi Shata (Khalifa)
j. Binta Shata (Mami)
k. Hadiza Shata
l. Amina Shata
m. Jamila Shata
n. Bilkisu Shata
o. Hadiza Shata (Lami) (ta rasu a 2003)
p. Hauwa Shata
q. Halima Shata
r. Ramatu Shata
s. Umma Shata
t. Rabi Shata
6. Shata ya mallaki motar hawa ta farko tun a shekara ta 1953.
7. Shata sau ɗaya rak ya je aikin Hajji, wato a 1956. Sai dai ya biya wa mutane da dama sun je Makka. Ko a shekara ta 1970 ya biya wa mutum 20 su ka tafi lokaci ɗaya.
8. Shata ya kai Kassu Zurmi da Sale Gambara da Muhammadu Gawo Filinge da Abubar Uwawu (‘Ƙusoshin birni Uwawu’) Makka.
9. Shata ba shi da wasu aljanu a matsayin ‘yan amshin sama.
10. Shata ba ya atisayen waƙa, wato ‘rehearsal’.
11. Asalin kakannin Shata Fulani ne daga Sayyina, Ƙaramar Hukumar Tambuwal, ta Jihar Sokoto.
12. Shata ya taɓa zama kansila a Ƙaramar Hukumar Kankiya (lokacin Musawa na ƙarƙashin Kankiya).

13. Shata ya taɓa zama shugaban jam’iyyar SDP na Ƙaramar Hukumar Funtuwa.
14. Shata ya taɓa bayyana aniyar tsayawa takarar shugabancin Nijeriya a shekara ta 1992/93 a ƙarƙashin jam’iyyar SDP.
15. Shata ya je ƙasar Amurka da London a shekara ta 1989.
16 . Mati Attah (‘Ɗan-‘Yarbayye’) ya na ɗaya daga cikin amintattun yaran Shata kuma tare da shi aka je Amurka. Duk abubuwan da Shata ya faɗi dangane da Mati a waƙa ya yi ne cikin wasa da raha.
17. Shata ya samu digirin digirgir na girmamawa, wato ‘Dr.’ wanda Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) ta ba shi a ranar 23/01/1988.
18. Shata ya samu lambar yabo ta ƙasa, MON (Member of the Order of the Niger) a lokacin gwamnatin Obasanjo a ranar 14/03/77.
19. Shata ya samu lambar yabo daga Shugaban Ƙasa Goodluck Ebele Jonathan a ranar Juma’a, 28/02/ 2014 (Centinary Award).
20. Sardaunan Dutse, Alhaji Bello Maitama, shi ne wanda Shata ya fi yi wa waƙoƙi da yawa.
21. Shata ne ya fara bai wa Ɗankabo hayar mota tun lokacin Ɗankabo na buga bulon sayarwa a bakin hanya.
22. Shata ba ya cewa “Ya wane” a cikin waƙa sai dai ya ce “Wo wane”. Duk inda ka ji ya ce “Ya”, to sunan Allah zai kira saboda girmamawa.
Allah ya jiƙan Na Ali Hukumar Waƙa, ya gafarta masa, kuma ya albarkaci zuri’ar shi baki ɗaya, amin.
Malam Hamisu Adamu Gamarali Funtua ma’aikaci ne a National Broadcasting Commission (NBC), inda shi ne shugaban ofishin hukumar a Katsina