• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, July 18, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ciyamomin MOPPAN na jihohi sun taya Habibu Barde murnar zama shugaban ƙungiyar

* Sun yi wa Dakta Sarari fatan alheri

by ABBA MUHAMMAD
February 2, 2024
in Labarai
0
Ciyamomin MOPPAN na jihohi sun taya Habibu Barde murnar zama shugaban ƙungiyar

Alhaji Habibu Barde Muhammad (a hagu) tare da Alhaji Haruna Mohammed Godowoli,

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ƘUNGIYAR ciyamomin Jihohi na ta taya sabon shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), Alhaji Habibu Barde Muhammad, murnar ɗarewa kan muƙamin nasa.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wasiƙar taya murnar da shugaban ƙungiyar ciyamomin, Malam Haruna Mohammed Godowoli, ya aika masa, wanda mujallar Fim ta samu kwafe.

A takardar, Godowoli ya ce, “Na yi wannan rubutun ne a madadin ƙungiyar Ciyamomin MOPPAN na Jihohi don taya ka murnar naɗa ka shugaban riƙo na Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) na ƙasa.

“Wannan babbar nasara ce kuma shaida a kan aikin ka tuƙuru, sadaukarwa da sha’awa a kan industirin Nijeriya.”

“A matsayin mu na ciyamomin jihohin na Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya mai girma, mun shaida irin gudunmawar ka na samun girma da cigaban wannan ƙungiya a lokuta daban-daban na shekara biyu.

“A kowane lokaci ka na nuna manyan matakai na alhaki, mutunci da girmamawa ga ƙungiyar da kuma membobin ta.

‘Mu na da kyakkyawar fata a kan shugabancin ka. MOPPAN za ta ci gaba da bunƙasa da cimma manufofin ta da hangen nesa.

“Ina yi maka fatan alheri a sabon mataki da kuma duba cigaba da aiki tare da kai, domin ba da goyon baya da inganta industirin Nijeriya da bayan ta.”

Har ila yau, ƙungiyar ciyamomin ta nuna damuwar ta game da murabus ɗin da tsohon shugaban ƙungiyar ta ƙasa, Dakta Ahmad Sarari, ya yi.

A cikin wasiƙar, shugaban ciyamomin ya ce, “Mun shiga damuwa mai tsanani a kan hukuncin da ka yanke na murabus daga muƙamin ka na Shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN). Amma ba mu da zaɓi da ya wuce mu karɓa a matsayin ƙaddara. Kuma mun kalle shi an riga an yanke shawara.”

Ya ci gaba da cewa, “Yallaɓai, ka kasance shugaba mai girma, mai ba da shawara, kuma aboki a gare mu tsawon shekara huɗu a matsayin shugaban mu. Ka yi mana wahayi da hangen nesa, ka zaburar da mu da sha’awar ka, ka goya mana baya da jagorancin ka, ka yi mana tsari mai kyau a ƙungiyar mu mai girma. Kuma ka sa mu alfahari da wannan babbar ƙungiyar tamu.

“Mu na so mu nuna godiyar mu ta gaske da godiya ga duk abin da ka yi mana. Ka koya mana fasaha masu mahimmanci da jagoranci mai salo, ka ba mu ra’ayi mai ma’ana, kuma ka taimaka mana girma cikin sana’a da kan mu.

“Haka nan ka ƙirƙiro tsari mai kyau kuma za mu iya ba da shaida, inda ana mutunta mu, ana daraja mu, da kuma ba mu iko.

“Ko yaushe ka kasance don mu, cikin lokuta masu kyau da marasa kyau. Kuma a madadin ƙungiyar ciyamomin jihohi ta MOPPAN, za mu yi kewar ka sosai.

“Mu na yi maka fatan alheri a ayyukan ka na gaba. Mu na fatan za ka samu farin ciki da nasara a duk abin da ku ka zaɓa a gaba, musamman Kannywood TV.

“Mu na da ƙwarin gwiwar za ka cigaba da haskawa da kawo canji a duk inda za ka je. Za ka samu wuri na musamman ko yaushe a cikin zukatan mu a matsayin ka na tsohon shugaban mu.

“Mun gode da kasancewar ka gwarzon shugaba. Na ruwaito, aikin jarumin mu na baya ba zai taɓa tafiya a banza ba. Ba za mu taɓa mantawa da kai ba.”

Loading

Tags: Ahmad SarariHabibu Barde MuhammadHaruna Mohammed GodowoliMOPPANshugabanci
Previous Post

Minista na so masu zanen gine-gine su riƙa bayyana kyakkyawan tarihin mu

Next Post

Cire tallafin fetur: Minista ya yaba wa IPMAN don rungumar shirin CNG

Related Posts

Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano
Labarai

Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano

July 11, 2025
Labarai

Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 

July 10, 2025
Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a
Labarai

Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a

July 9, 2025
Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu
Labarai

Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu

July 7, 2025
MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 
Labarai

MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 

June 29, 2025
Ƙungiyoyin harkar fim, KAFIGAN da MOPPAN, sun yi wa Rahama Sadau ta’aziyyar rasuwar mahaifin ta
Labarai

Ƙungiyoyin harkar fim, KAFIGAN da MOPPAN, sun yi wa Rahama Sadau ta’aziyyar rasuwar mahaifin ta

June 23, 2025
Next Post
Cire tallafin fetur: Minista ya yaba wa IPMAN don rungumar shirin CNG

Cire tallafin fetur: Minista ya yaba wa IPMAN don rungumar shirin CNG

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!