A DAIDAI lokacin da ake shirin shiga zaman gida a Kano sakamakon umarnin da gwamnatin jihar ta bayar na killace mutanen jihar a cikin gidajen su, kwamitin kasuwanci na cikin masana’antar finafinai ta Hausa, wato ‘Distribution Committee,’ ya raba kwalin taliya guda 80 ga masu buƙatar taimako a cikin masana’antar domin rage masu raɗaɗin zaman gida da za su yi.
Jami’in yaɗa labarai na kwamitin, Isma’ila Khalil Ja’en, ya shaida wa mujallar Fim cewa, “A wannan rana ta 16/4/2020 wannan kwamiti namu da Alhaji Sani Sule Katsina ya ke jagoranta, mun yi yunƙuri na samar da kayan tallafi ga masu buƙata, wanda a wannan yunƙurin aka samar da kwalin taliya guda tamani domin raba wa masu ƙaramin ƙarfi.
“Don haka a yanzu ma an gudanar da aikin rabon inda aka rarraba kayan ga wasu jarumai da su ke buƙatar tallafin, sai dattawan cikin mu da ma wasu na waje da su ke buƙatar taimako.
“Kuma abin alfahari, aikin rabon kayan an yi shi cikin kwanciyar hankali ta yadda aka bi tsarin kowanne ɓangaren aka kirawo shugabannin su su ka zo su ka karɓa a madadin su.”
Daga ƙarshe, Isma’ila Khalil Ja’en ya yi roƙon Allah ya kawo mana ƙarshen wannan masifa da ta buwayi duniya.