MINISTAR Harkokin Agaji Da Jinƙai, Hajiya Sadiya Farouq, ta bayyana cewa ‘yan Nijeriya 198, waɗanda su ka maƙale a ƙasar Lebanon sakamakon hutun dole na annobar korona, yanzu sun samu damar dawowa gida.
A cewar ministar, ma’aikatar ta, tare da haɗin gwiwar Cibiyar Yaƙi Da Fataucin Mutane ta Ƙasa (NAPTIP) da kuma Cibiyar Agajin Gaugawa ta Ƙasa (NEMA), sun tarbi waɗanda su ka dawo ɗin a ranar Laraba, 12 ga Agusta da ranar Alhamis, 13 ga Agusta, 2020.
A wata sanarwa ga manema labarai da aka bayar a ranar Juma’a, ministar ta kuma bayyana cewa akwai ‘yanmata ‘yan Nijeriya 5,000 da su ke maƙale a Lebanon yanzu.
Ta ce, “Jimillar ‘yan Nijeriya 198 waɗanda su ka maƙale a Lebanon sun samu ‘yancin su kuma sun iso gida.
‘’Akwai aƙalla ‘yanmata ‘yan Nijeriya 5,000 a maƙale a Lebanon bayan an ja su an kai su da sunan wai za su yi aikatau a gidaje, wanda daga cikin su Ofishin Jakadancin Nijeriya ya kammala tattara bayanai kan mutum 256 waɗanda su ka amince su dawo gida.
“Ma’aikatar mu tare da cibiyoyin da abin ya shafa a ƙarƙashin ta sun sadaukar da kan su wajen tabbatar da cewa ‘yan Nijeriyan da su ka maƙale a Lebanon da wasu ƙasashen sun dawo gida lafiya lau.”
Hajiya Sadiya ta ƙara da cewa gwamnati ta samu kiraye-kirayen neman agaji daga ‘yanmata ‘yan Nijeriya a Saudi Arebiya, Oman, Masar da sauran sassan ƙasashen ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya.
Saboda haka ta yi kira ga ‘yan Nijeriya, musamman matasa, da su guji bari ana yaudarar su ta hanyar shafa masu mai a baki da alƙawuran ƙarya cewa za su samu rayuwa mafi inganci a can, nan kuwa aikin zubar da mutunci za su je yi.
Maimakon haka, ta shawarce su da su yi amfani da shirye-shirye daban-daban da ke akwai waɗanda gwamnati ta fito da su domin taimaka masu su samu hanyoyin kyautata rayuwar su a cikin Nijeriya.
Ta ƙara da cewa babu inda ya fi gida.
Ministar ta yaba da aikin masu ruwa da tsaki cikin lamarin irin su gwamnatin Jihar Oyo, da IOM da al’ummar ‘yan ƙasar Lebanon da ke Nijeriya saboda goyon bayan da su ka bayar wajen dawo da ‘yan Nijeriyar gida lafiya lau.
Ta nanata cewa za a ɗauki bayanan dukkan waɗanda su ka dawo ɗin tare da goyon bayan hukumar NAPTIP.