• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 16, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

INEC ta ƙaddamar da sabon Tsarin Sadarwa

by DAGA WAKILIN MU
August 15, 2020
in Nijeriya
0
Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban INEC

Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban INEC

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yi kira ga masu ruwa da tsaki a harkokin zaɓe da su haɗa hannu da hukumar wajen ƙarfafa yin amfani da hanyoyin fasaha da tabbatar da gudanar da zaɓe mai nagarta.
 
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka a wajen wani taro ta hanyar intanet wanda aka gudanar don ƙaddamar da kundin “Sabon Tsarin Sadarwa na INEC” a ranar Juma’a.
 
Farfesa Yakubu, wanda a taron ya samu wakilcin Mista Festus Okoye, babban kwamishina kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu zaɓe na hukumar, ya ce hukumar ta na sane sosai da cewa tilas ne a musanya tsohon tsarin da ake amfani da shi wajen gudanar da zaɓe da sabon tsari ta hanyar shigo da hanyoyin fasaha na zamani a hankali a hankali.
 
Ya ce: “Wannan ne dalilin da ya sa mu ka kafa gidan yana domin rajistar ‘yan takara na jam’iyyu, da gidan yana domin rajistar masu sa ido a zaɓe, da gidan yana domin rajistar ‘yan jarida.
 
“Domin tabbatar da aminci da inganci wajen bayyana sakamakon zaɓe, mun gina gidan yana don duba sakamakon zaɓe inda hukumar kan saka fom mai suna Form EC8A don jama’a su gani.
 
“Mu a wannan hukuma za mu ci gaba da ƙara wa kan mu sanin makamar aiki da ake amfani da ita a sassan duniya a harkar yaɗa labarai da sadarwa kan harkokin zaɓe.
 
“Za mu ci gaba da ƙara wa kan mu ilimi kan al’amurra da hanyoyin zaɓe, don haka mu na kira ga kafafen yaɗa labarai da ƙungiyoyi masu zaman kan su da ma duk wanda abin ya shafa da su haɗa hannu da hukumar wajen amfani da hanyoyin fasaha da ƙere-ƙere na zamani a harkokin zaɓe.
 
“Mu na kira ga manyan masu ruwa da tsaki da su haɗa hannu da hukumar don tabbatar da aminci da inganci a zaɓe da fidda sakamakon zaɓe.
 
“Wannan buri namu na son cimma waɗannan ƙudirori shi ne dalilin mu na fito da wannan sabon Tsarin Sadarwar.”
 
Farfesa Yakubu ya bayyana Tsarin Sadarwa na INEC a matsayin cikakken kundi da aka fito da shi don gudanar da al’amurran gudanarwa na cikin gida da na waje a hukumar.
 
Ya ce an yi tsarin ne saboda a cire aikin garaje da rashin shiri a wajen gudanar da aikin sadarwa a hukumar.
 
Shugaban ya yi kira ga dukkan waɗanda su ka halarci taron da su yi wa kundin tsarin sadarwar karatun ta-natsu don su fahimci manufa da kuma burin kundin.
 
Haka kuma ya faɗa masu cewa su kalli kundin ba kawai don fahimtar aikin tsarin sadarwar INEC ba, har ma don gane ɗimbin ƙalubalen da ke akwai.
 
Ya ce akwai wahalar gudanar da aikin sadarwa a cikin gida da waje a daidai lokacin da kowane mutum da kuma ƙungiyoyi su ke fuskantar ƙalubalen rayuwar su a dalilin annobar korona da ta zo wa duniya.
 
Ya ce: “Ya na da wuya mutane da ƙungiyoyi da hukumomi su tattara hankalin su kan harkar zaɓe a lokacin da tsoro da damuwa da ma abin da ya fi haka ya addabe su.
 
“Da wuya a sa mutane da ƙungiyoyi su tattara hankalin su kan harkokin zaɓe a daidai lokacin da babu maganar da aka fi yi a duniya kamar ta wannan annoba da hanyoyin magance ta.
 
“Da wuya a sa mutane su tattara hankalin su kan batun zaɓe a lokacin da su ke fargabar za su iya rasa aikin su ko ma har sun rasa aikin nasu ko kuma su na zama a cikin sansanin ‘yan gudun hijira. 
 
“Da wuya a sa mutane su tattara hankalin su kan batun zaɓe a daidai lokacin zaman ɗar-ɗar.”
 
Farfesa Yakubu ya ƙara da cewa sanar da mutane wani abu da su ke ganin bai zama dole a gare su ba a lokacin da su ke fuskantar annoba ko wahalhalu abu ne da ke buƙatar sabbin dabaru da ƙarfafawa, wanda kuma hakan na buƙatar sabbin tunani da dabaru.
 
”Saboda haka,  tilas ne masana da manajoji kan yaɗa labarai da sadarwa su fito da hanyoyi da dabarun da za su sa mutane su tattara hankalin su kan saƙonni masu alaƙa da al’amurran gudanar da zaɓe.
 
“Haka kuma ya na da muhimmanci a yaɗa irin waɗannan saƙonni da labaran ta hanyoyin da mutane za su fahimta a sabon yanayin nesantar juna, zaman dole da ƙaruwar masu kamuwa da cuta a kullum.
 
“Don haka tilas ne manajojin kafafen yaɗa labarai su riƙa aikin su na sadarwa ta hanyar da mutane za su gani su fahimci zaɓe a matsayin wani abu da ya dace da rayuwar su.”
 
Har ila yau, shugaban hukumar ya bayyana cewa an fito da Tsarin Sadarwar ne saboda a bai wa INEC damar gudanar da aikin sadarwa yadda ya kamata.
 
Farfesa Yakubu ya nemi haɗin kan dukkan manyan masu ruwa da tsaki a harkar sadarwa a INEC, tare da cewa hukumar ta na buƙatar fahimta da haɗin kan kafofin yaɗa labarai domin ta isar da saƙonnin ta ga jama’ar Nijeriya.
 
Lokacin da ya ke gabatar da sharhi kan kundin sabon Tsarin Sadarwa na hukumar, babban sakataren yaɗa labarai na shugaban hukumar ta INEC, Mista Rotimi Oyekanmi, ya ce kundin mai shafi 55 ya ƙunshi al’amurra da dama waɗanda za su inganta harkar sadarwa ta hukumar.
 
Oyekanmi ya ce kundin ya nanata cewa a tabbatar “ƙwararru ko ma’aikatan da aka horas ne kaɗai za a ɗora kan aikin hulɗa da ‘yan jarida da wayar da kan masu zaɓe a hukumar” a kowane mataki.

Loading

Previous Post

Cutar korona: ‘Yan Nijeriya 198 sun dawo daga Lebanon – Sadiya Farouq

Next Post

Mas’alar fyaɗe da taɓarɓarewar tarbiyya a ƙasar mu

Related Posts

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Next Post
Yarinya na tallar lemo da ruwa a Akwanga, Jihar Nassarawa

Mas'alar fyaɗe da taɓarɓarewar tarbiyya a ƙasar mu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!