• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, July 1, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Da daɗi, ba daɗi: Muhimman abubuwan da su ka faru a Kannywood a cikin 2021

by DAGA ABBA MUHAMMAD
December 31, 2021
in Nijeriya
0
Daga hagu: Aisha ‘Izzar So’, Lawan Ahmed, Momee Gombe da Garzali Miko sun yi shiga don nuna murnar cikar Nijeriya shekara 61 da samun ‘yanci... a ranar 1 ga Oktoba

Daga hagu: Aisha ‘Izzar So’, Lawan Ahmed, Momee Gombe da Garzali Miko sun yi shiga don nuna murnar cikar Nijeriya shekara 61 da samun ‘yanci... a ranar 1 ga Oktoba

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MASANA’ANTAR shirya finafinan Hausa ta Kannywood ta ga samu ta ga rashi a cikin wannan shekara mai ƙarewa a daren yau. Akwai ‘yan fim da su ka samu ƙarin ɗaukaka, har ma da kuɗi da gida da mota, akwai kuma waɗanda koma-baya su ka samu.

Mujallar na tare da ‘yan fim da mawaƙa a ko yaushe, don haka ta wallafa labarai daban-daban kan abubuwan da su ka wakana ko aka faɗi daga masana’antar.

A nan, ga jerin wasu daga cikin muhimman abubuwan da mu ka ba ku labari a kan su. Sai dai a wannan jerin babu labaran aure, haihuwa da mace-macen da aka yi, domin su sun shiga cikin wasu labaran ne masu zaman kan su da mu ka bayar a yau, waɗanda za ku iya karantawa.

LABARAI

JANAIRU:

* Fitaccen mawaƙin siyasa Dauda Abdullahi Kahutu (Rarara) ya ba wa fitattun jarumai Tijjani Asase da Jamila Nagudu kyautar motoci. Asase ya samu Matrix, ita kuma Jamila ta samu Hyundai.

* Sheikh Dakta Bashir Aliyu Umar na Masallacin Alfurƙan da ke Kano ya jawo ka-ce-na-ce cikin wa’azi, da ya yi misali da cewa idan ka saki matar ka a fim, matar ta gaske ta saku don ba a wasa da sha’anin aure. Shugabannin Kannywood Sani Mu’azu da Hamisu Iyan-Tama sun yi masa tambihi.

* Shugaban Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, Malam Isma’il Na’abba (Afakallahu), ya bayyana dalilin da ya sa hukumar ta fara aikin sabunta rajistar ‘yan fim.

* Shugabar gidauniyar taimaka wa mabuƙata ta ‘Creative Helping Neddy Foudation’ kuma fitacciyar marubuciya da ke Kano, Malama Fauziyya D. Sulaiman, ta ƙaryata ji-ta-ji-tar da ake yaɗawa cewa darakta Ashiru Nagoma ya samu lalurar taɓin hankali.

* Fitaccen jarumi Shehu Hassan Kano ya ƙaryata ji-ta-ji-tar da ake yaɗawa cewa ya makance.

FABRAIRU

* Masoyan fitaccen mawaƙi Nura M. Inuwa sun yi zanga-zanga a Kano a ranar wata Litinin domin nuna damuwar su ta rashin ganin sababbin waƙoƙi daga gare shi.

* Fitacciyar jaruma Maryam Aliyu Obaje, wadda aka fi sani da Madam Korede, ta bayyana dalilin ta na yin gwajin cutar ƙanjamau (HIV/AIDS).

* Fitaccen jarumi Aminu A. Shareef (Momoh) ya bayyana cewa a yau muhimmancin raya harkar fim a ƙasar Hausa ya fi na gina masallaci ko makarantar Islamiyya.

* Hukumar Tace Finafinai da Bidiyo ta Ƙasa (NFVCB) ta gargaɗi ‘yan fim da mawaƙa na Hausa da su daina sakin finafinai ko waƙoƙin su a YouTube ba tare da amincewar ta ba.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano tare da ‘yan fim da su ka kai masa ziyara sa a cikin Satumba
Ado Ahmad Gidan Dabino, MON (a hagu) ya na karɓar kambin karramawar sa na Jarumin Jaruman Afrika a gasar ‘WAMMA Awards’ ta bana, a Yamai ɗin Jamhuriyar Nijar cikin watan Satumba

MARIS

* A wani zama da aka yi tsakanin Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano da Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), an cimma matasaya kan cewa humakar ba za ta ƙara kama wani ɗan fim ba har sai ta tuntuɓi kwamitin ladabtarwa da MOPPAN za ta kafa a cikin gaggawa.

* Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta cafke fitaccen mawaƙin yabon Manzon Allah (s.a.w.) Malam Bashir Ɗandago tare da gurfanar da shi a gaban kotu.

* Wasu ɓarayi sun auka gidan matashin jarumi Nasiru Naba, su ka ƙwace motar sa kwana biyu da sayen ta. Amma daga baya an kama su.

AFRILU

* Fitacciyar jaruma Ummi Ibrahim (Zee-Zee) ta bayyana cewa an damfare ta ɗaruruwan miliyoyin naira, wanda hakan ya sa ta na so ta kashe kan ta.

* Ummi Zee-Zee ta bayyana cewa ‘yan Nijeriya waɗanda ba Musulmai ba sun fi jinƙai.

* An shiga zazzafan ruɗani a kan wani labari da ya ɓulla a soshiyal midiya cewa fitacciyar jarumar Kannywood Ummi Zee-Zee ta rasu. Amma ƙanwar ta Hasina Ɗanchana ta ƙaryata labarin.

MAYU

* Fitaccen jarumi Tijjani Asase ya kafa kamfanin sa na shirya finafinai, ya kuma ɗaura ɗamara domin taimaka wa matasa masu tasowa ta hanyar sanya su a cikin finafinan su domin rage harkar daba da shaye-shaye a tsakanin su.

* Fitacciyar jaruma Ummi Zee-Zee ta ragargaji wani jarumi da ta ke ganin ya fi kowane ɗan wasa takalar ta a soshiyal midiya. An fahimci cewa wani ɗan garin Kaduna ne.

* Shugaban Zauren Malamai na Jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya ce sana’ar fim halastacciya ce a cikin addinin Musulunci matuƙar za a kiyaye ƙa’idojin da ya kamata a bi.

* Shugabar ƙungiyar matan masana’antar finafinan Hausa (Kannywood Women Association of Nigeria, K-WAN), Hajiya Hauwa A. Bello (Edita), ta bayyana cewa ‘ya’yan ƙungiyar sun shirya tsaf domin fatattakar maza daga dukkan ayyukan da ya kamata a ce mata ne su ke gudanar da su a masana’antar.

* Aƙalla ‘yan wasa 500 aka tsara za su fita a fim ɗin nan mai dogon zango na ‘Gidan Dambe’, wanda fitaccen mawaƙi Dauda Kahutu (Rarara) ya ɗauki nauyin shiryawa, a cewar darakta Abdulmumin Tantiri.

* Tsohon Mataimakin Shugaban Buɗaɗɗiyar Jami’ar Nijeriya (NOUN), Farfesa Abdalla Uba Adamu, ya ƙwanƙwashi ‘yan fim ɗin Hausa tare da ƙalubalantar su da cewa in dai su na so a kira su ƙwararru, to sai sun nemi ilimi mai zurfi a kan harkar fim.

* Mujallar Fim ta wallafa labarin cda ta gano cewa fitacciyar jaruma Mansurah Isah ta ta daɗe da barin gidan Sani Danja, inda ta tare a wani gida da ta kama haya a Kano, bayan tsinkewar igiyar auren ta da Sani Musa Danja. Labarin ya ja hankali sosai.

* Mansurah Isah ta bayyana cewa mutuwar auren ta da Sani Danja ita ce ta fi dacewa.

* Fitaccen mawaƙin siyasa Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara) ya raba kyautar naira miliyan uku ga wasu zaɓaɓɓu daga cikin jarumai maza da mata a masana’antar finafinan Hausa ta Kannywood su sittin.

Dauda Rarara ya bada tallafin miliyoyin naira da motoci ga ‘yan fim da dama a wannan shekara. A nan, ya na miƙa wa Tijjani Asase makullin kyautar mota da ya yi masa ne
Sheikh Ibrahim Khalil ya bayyana fatawar cewa harkar fim ta halasta a Musulunci, amma fa da sharaɗi

YUNI

* Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya naɗa fitaccen darakta kuma jarumi Ishaq Sidi Ishaq matsayin babban mai taimaka masa na musamman a kan harkokin fasaha.

* Furodusa Sani Sule Katsina ya ce zamani ne ya rusa harkar fim ba Afakallahu ba. 

* Shugaban Ƙungiyar Makaranta Mujallar Fim ta Ƙasa, Alhaji Sanusi Ibrahim Fari Gɗaɗawa, ya yi kira ga masu shirya finafinan Hausa da su sanya tsoron Allah a dukkan ayyukan su, musamman a wannan lokaci da ake ciki na sauyin zamani.

* Masu harkar fim a Nijeriya sun yi wani babban taro a Legas, wanda wata ƙungiya mai suna KAPA ta shirya, kan yadda za a daina nuna shan taba ko tallar ta a finafinan da ake yi a ƙasar.

YULI

* An wayi gari da labarin wai shahararren ɗan wasan kwaikwayo Alhaji Usman Baba Pategi (Samanja) ya rasu. Amma a ranar sai mujallar Fim ta zanta da shi, inda ya ƙaryata labarin.

* Babban Hafsan Hafsoshin Sojan Nijeriya (COAS), Manjo Janar Yahaya, ya aika da agajin kuɗi naira miliyan biyu ga tsohon ɗan wasan kwaikwayo Alhaji Usman Baba Pategi (Samanja).

* Masu garkuwa da mutane sun sace ɗaya daga cikin shugabannnin harkar fim a Jihar Zamfara, Alhaji Ali Bulala Gusau. Daga baya sun sako shi bayan an biya kuɗin fansa naira miliyan biyar.

* A hira da mujallar Fim, fitacciyar jaruma Maryam Yahaya da iyayen ta sun ƙaryata ji-ta-ji-tar da ake yaɗawa cewa wai an yi mata makaru ne wanda ya sa ta ke fama da rashin lafiya.

* ‘Yan fim ɗin Hausa sun yi tir da jaridar nan ta intanet mai suna ‘Sahara Reporters’, inda su ka shiga sahun sauran al’ummar Musulmi wurin yi mata tofin Allah-tsine, sakamakon ɓatancin da ta wallafa ga Annabi (s.a.w.).

* MOPPAN ta yi alƙawarin za ta samar wa jaruma Rahama A. Ibrahim, matashiyar nan da ta musulunta saboda kallon finafinan Hausa, da kyawawan yanayi a Kano, musamman abubuwan more rayuwa.

* A hira da mujallar Fim, sabuwar jaruma Rahama A. Ibrahim ta bayyana yadda kallon finafinan Hausa ne ya ba ta sha’awar shiga Musulunci tare da shigowa masana’antar finafinan Hausa don ta bada gudunmawar ta a harkar.

AGUSTA

* Gwamnatin Kano ta ƙudiri aniyar kawo gyara a labarin fim ɗin ‘A Duniya’, mai dogon zango na fitaccen jarumi Tijjani Abdullahi (Asase), wanda ake haskawa a YouTube.

* Fitacciyar jaruma Ummi Rahab ta gargaɗi tsohon ubangidan ta, fitaccen jarumi kuma mawaƙi Adam A. Zango, a kan ya fita daga sha’anin ta, har ta yi barazanar za ta tona masa asiri idan idan har bai daina ɓata mata suna ba.

* Fitaccen jarumi kuma darakta Ali Nuhu ya zama jakaden Skyline University of Nigeria da ke Kano. An yi taron naɗa shi a harabar jami’ar.

* Fitaccen jarumi Tijjani Abdullahi (Asase) ya ƙaryata masu cewa gwamnati ta dakatar da nuna shirin ‘A Duniya’.

* Fitacciyar jaruma Umma Shehu ta bayyana cewa wasu daga cikin shugabannin Hukumar Hisbah ta Jihar Kano manema mata ne. Ta faɗi haka ne wajen kare jaruma Sadiya Haruna kan sukar da ake mata dangane da tallar kayan ƙara ƙarfin mazakuta da ta ke yi a Instagram, inda wasu su ka ce ta na yin batsa.

* Adam A. Zango ya bayyana cewa ko kaɗan shi bai soyayya da Ummi Rahab ba kamar yadda wasu ke tunani. A madadin haka, rashin biyayyar ta a gare shi ne babban abin da ya raba shi da ita. 

* Kotu a Kano ta yanke wa jaruma kuma furodusa Sadiya Haruna hukuncin komawa makarantar Islamiyya.

* Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta bayyana cewa ta na neman jaruma Umma Shehu domin ta je ta kare kan ta kan ƙazafin da ta yi wa jami’an hukumar.

* Fitaccen jarumin barkwanci Ali Artwork (Maɗagwal) ya bayyana cewa Adam A. Zango ya daɗe ya na yaudarar ‘yan mata, ba Ummi Rahab ce farau ba.

* Wasu daga cikin ‘yan fim ɗin Hausa sun yi Allah-wadai da wasu kalamai da jaruma Umma Shehu ta yi a kan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano.

* Yasir M. Ahmad, wanda ke iƙirarin shi ɗan’uwan Ummi Rahab na jini ne, ya maida kakkausan martani kan maganganun da ake yaɗawa a kan sa. A ciki, ya ƙaryata Adam A. Zango kan iƙirarin wai bai taɓa soyayya da jarumar ba, da kuma batun wai ya rabu da ita ne saboda ba ta yi masa biyayya.

* A hira da mujallar Fim, Yasir M. Ahmad da Ali Artwork sun tona asirin Adam A. Zango da Ummi Rahab ta ce za ta tona.

* An kwantar da Babban Sakataren MOPPAN, Salisu Ma’azu, a asibiti bayan haɗarin mashin ya rutsa da shi.

A cikin Agusta, Ummi Rahab ta jawo surutu da ta gargaɗi Adam A. Zango da cewa za ta tona masa asiri idan bai ƙyale ta ba
Ummah Shehu ta jawo ka-ce-na-ce da ta ce a manyan ‘yan Hisbah na Kano akwai manema mata

SATUMBA

* Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana ƙudirin gwamnatin sa na ci gaba da taimaka wa masana’antar shirya finafinai ta Kannywood a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso. Haka kuma ya jinjina wa shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Alhaji Isma’il Na’abba (Afakallah), saboda sadaukarwar sa ga ciyar da gwamnatin sa gaba. Gwamnan ya bayyana haka ne a daren ranar Juma’a, 3 ga Satumba, a lokacin wani zama na musamman da ya yi tare da masu ba shi shawara na musamman kan harkokin nishaɗantarwa da kuma wasu manyan ‘yan fim.

* Hukumar yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta yi taro tare da haɗin gwiwar ‘yan fim ɗin Hausa domin magance matsalar ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a Jihar Kano.

* Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, ya zama Jarumin Jarumai a gasar mawaƙa da finafinai ta Afrika ta Yamma saboda rol ɗin sa a ‘Kwana Casa’in’, wanda ake nunawa a tashar talbijin ta Arewa24.Gasar, wadda a Turance ake kira ‘West African Music and Movie Awards (WAMMA Awards) an gudanar da ita ne a Yamai, babban birnin ƙasar Nijar. Shi ma jarumi, mawaƙi kuma furodusa T.Y. Shaban shi ne ya lashe matsayin zama mataimakin gwarzon jarumi (supporting actor) a gasar wadda aka yi a babban ɗakin taro na Palais des Congress da ke Yamai, babban birnin ƙasar Nijar, a ranar Lahadi, 19 ga Satumba, 2021.

* Mataimakin sakataren MOPPAN, Alhaji Salisu Muhammad (Officer), ya ce ba shi niyyar neman kujerar Afakallahu.

* An naɗa darakta Ahmad Salihu Alkanawy matsayin shugaban kwamitin zaɓe na MOPPAN.

* Naziru Sarkin Waƙa ya hayaƙa wasu ‘yan jarida a cikin shirin ‘Labari Na’, da ya nuna cewa ‘yan jarida ‘yan maula ne, har su ka mayar masa da martani.

* Gwamnatin Kano ta haramta shirya ko nuna duk wani fim da aka yi shi a kan yadda ake garkuwa da mutane ko sayarwa da shan kayan maye ko ƙwacen waya.

* Gwamnan Jihar Nassarawa, Injiniya Abdullahi A. Sule, ya bayyana ƙudirin sa na mayar da jihar cibiyar gudanar da harkokin finafinan Hausa saboda gudunmawar da masana’antar Kannywood ke bayarwa ga cigaban ƙasa.

* Fitaccen furodusa Abdul Amart Muhammad (Maikwashewa) ya ƙaddamar ƙungiyar ‘Yahaya Bello Network Group’ domin nema wa gwamnan Jihar Kogi kujerar shugabancin Nijeriya.

* MOPPAN ta ƙaddamar da sayar da takardun neman shugabancin ƙungiyar a matakai daban-daban.

* Ɗalibai ‘yan Nijeriya da ke karatu a Jami’ar Integral da ke garin Lucknow a ƙasar Indiya sun karrama fitacciyar jaruma Rahama Sadau, wadda ta je ƙasar domin ɗaukar wani fim ɗin Bollywood.

OKTOBA

* A ranar 1 ga Oktoba ‘yan fim da dama sun wallafa hotunan taya Nijeriya murnar cika shekaru 61 da samun mulkin kai.

* Furodusa Umar UK ya yi ƙarar jaruma Hafsat Idris, ya na neman diyyar miliyan goma a hannun ta saboda kasa halartar ɗaukar fim ɗin sa da ta yi bayan ta karɓi shigar ciniki.

* MOPPAN ta bayyana cewa a Lafiya ne, wato babban birnin Jihar Nassarawa, za a gudanar da babban zaɓen ƙungiyar.

* Mawaƙi Dauda Kahutu (Rarara) ya bayyana cewa zai tsaya takarar zama ɗan Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Bakori da Ɗanja da ke Jihar Katsina.

Wani malami ya na ba Rahama Sadau kyautar fulawa lokacin da malamai da ɗalibai su ka karrama ta a Jami’ar Integral da ke garin Lucknow a ƙasar Indiya

NUWAMBA

* An zaɓi shugaban MOPPAN na ƙasa, Dakta Ahmad Sarari, da Sani Mu’azu matsayin wasu daga cikin zaɓaɓɓun shugabannin wata ƙungiyar mai kare haƙƙin masu basirar ƙirƙira a Nijeriya, wato ‘Audio Visual Right Society’ (AVRS).

* Fitaccen furodusa Alhaji El-Sa’eed Yakubu Lere, ya maka shugaban hukumar daraktocin kamfanin rukunin gidajen rediyo na Vision FM da talabijin na Farin Wata a kotu, ya na neman ya biya shi diyyar naira miliyan 20.

* An zaɓi Alhaji Hamisu Jibril Goma matsayin shugaban MOPPAN reshen Jihar Kaduna.

DISAMBA

* An naɗa fitaccen jarumi Umar Gombe matsayin shugaban riƙo na MOPPAN reshen Jihar Kano.

* Tsohuwar jaruma Mansurah Isah ta yi gangamin sauke Alƙur’ani da karanta Alƙunut, sakamakon ibtila’in kashe-kashe da kidinafin da ya addabi Arewa.

* Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta taka wa kamfanonin da ke yaɗa finafinai da waƙoƙi a intanet ko talbijin burki domin za a iya amfani da su a jawo fitina a Nijeriya.

* Membobin Ƙungiyar Furodusoshi ta Jihar Kaduna a yau sun zaɓi Malam Uwaisu Abubakar a matsayin sabon shugaban su. An gudanar da zaɓen a ofishin Hajiya Fatima Ibrahim Ahmad (Lamaj) da ke Rigachikun, Kaduna, a ranar Asabar, 25 ga Disamba, 2021.

* Mawaƙi Naziru M. Ahmad (Sarkin Waƙa), ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta hana amfani da manhajar nan ta TikTok tun kafin lokaci ya ƙure.

Loading

Previous Post

Tsohuwar jaruma Fati Ladan ta shawarci matan Arewa kan zaman aure mai ɗorewa

Next Post

Aure da haihuwa a Kannywood a cikin 2021

Related Posts

Tawagar Gwamnatin Tarayya ta miƙa saƙon ta’aziyya daga Tinubu tare da yin addu’o’i a gidan Ɗantata a Madina
Nijeriya

Tawagar Gwamnatin Tarayya ta miƙa saƙon ta’aziyya daga Tinubu tare da yin addu’o’i a gidan Ɗantata a Madina

June 30, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta bada tabbacin akwai tsaro a Abuja duk da gargaɗin da Amurka ta ba matafiya

June 23, 2025
Kiran Gwamnatin Tarayya ga ‘yan jarida: Ku zama jigo wajen gina dimokiraɗiyyar Nijeriya
Nijeriya

Kiran Gwamnatin Tarayya ga ‘yan jarida: Ku zama jigo wajen gina dimokiraɗiyyar Nijeriya

June 21, 2025
Ministan Yaɗa Labarai ya yaba wa Hafsoshin Soji kan cigaban da aka samu a fannin tsaron ƙasa a shekaru biyu
Nijeriya

Ministan Yaɗa Labarai ya yaba wa Hafsoshin Soji kan cigaban da aka samu a fannin tsaron ƙasa a shekaru biyu

June 20, 2025
Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Next Post
Garzali Miko da amaryar sa Habiba Ahmad Dikwa

Aure da haihuwa a Kannywood a cikin 2021

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!