• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Aure da haihuwa a Kannywood a cikin 2021

by DAGA ABBA MUHAMMAD
December 31, 2021
in Nijeriya
0
Garzali Miko da amaryar sa Habiba Ahmad Dikwa

Garzali Miko da amaryar sa Habiba Ahmad Dikwa

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

KAMAR kowane sashe na jama’a, su ma ‘yan fim ɗin Hausa su na aure tare da hayayyafa. Mujallar Fim ce a kan gaba wajen bada labaran irin waɗannan abubuwa na farin ciki kamar yadda ake gani a shafin Ranar Murna. Kamar kowace shekara, a bana ma mun kawo maku jerin labaran aurarraki da haihuwa da aka yi waɗanda su ka danganci ‘yan fim da mawaƙan da ke cikin Kannywood. Ga su kamar haka:

AURE


 Asabar, 30 ga Janairu:Mawaƙi Umar Ɗanhausa da Fatima Bashir, a masallacin Juma’a na Ɗanfodiyo da ke Unguwar Sanusi, Kaduna, a kan sadaki N50,000.

Asabar, 30 ga Janairu:Furodusa Abba Sadau da Zainab Musa Yarima, a masallacin A’ishatu Ɗan’iyan Misau da ke Titin Shagari, unguwar Badarawa, Kaduna, a kan sadaki N100,000.

Amal Umar na murnar cikar ta shekara 23 da haihuwa a cikin Oktoba
Editan jaridar Rariya kuma jarumi Aliyu Ahmad da amaryar sa Hauwa Sa’idu Gambo a wajen bikin auren su 

Juma’a, 5 ga Fabrairu:Fitaccen jarumi Rabi’u Rikadawa ya aurar da ‘yar sa Fatima ga jarumi Salisu Abdullahi (Babangida), a masallacin Kabala Junction da ke Titin Nnamdi Azikiwe (Bypass), Kaduna, a bisa sadaki N100,000.

Abba Sadau da Zainab Musa Yarima a wajen bikin auren su

Juma’a, 12 ga Fabrairu:Tsohuwar jaruma Fati KK ta koma gidan tsohon mijin ta Alhaji Mu’azu Yusuf. An ɗaura auren a gidan su da ke Sabon Kawo, Kaduna.

Juma’a, 12 ga Fabrairu:An ɗaura auren Editan jaridar Rariya kuma jarumi a Kannywood, Aliyu Ahmad, da sahibar sa, Hauwa Sa’idu Gambo, a masallacin Juma’a na Babbar Kasuwar Muhammadu Buhari da ke garin Karu, yankin Abuja, a kan sadaki N100,000.

Adam A. Zango da Safiyya Umar Chalawa (Suffy) cike da murnar samun ƙaruwa da ‘ya mace, Furaira (Diyanah)
Mifrah Nura M. Inuwa (Mifrah)

Juma’a, 26 ga Fabrairu:Darakta Sheikh Isah Alolo da Basira Isma’il, a wani masallacin Juma’a da ke Titin Galadimawa, unguwar Hayin Ɗanmani, Kaduna, a kan sadaki N100,000.

Asabar, 27 ga Fabrairu:Mawaƙi Ibrahim Saleh (Yala) da Halima Muhammad Kauru (Sima), a Masallacin Sarkin Musulmi Bello da Unguwar Sarki, Kaduna, a bisa sadaki N100,000.

Asabar, 27 ga Fabrairu:Mawaƙi Mas’ud Idris da A’isha Abubakar, a wani Masallaci da ke Bakin Boda, Unguwar shanu, Kaduna, a kan sadaki N70,000.

Abba Muhammad da amaryar sa Jamila Ibrahim Dassi

Asabar, 27 ga Maris:Mawaƙi kuma jarumi Abdu Boda da Hafsat Sabi’u Sani, a gidan Muntari Masko da ke Layin Zana a unguwar Ƙofar Marusa, Katsina, a kan sadaki N50,000.

Asabar, 27 ga Maris:Fitacciyar jaruma Hafsat Idris ta aurar da ‘yar ta Khadija Kabir ga Abubakar Ibrahim Muhammad, a unguwar Ɗandago cikin ƙwaryar Kano, a kan sadaki N50,000.

Juma’a, 4 ga Yuni:Editan riƙo na mujallar Fim, Abba Muhammad, da Jamila Ibrahim Dassi, a Masallacin Sheikh Ja’afar Mahmud Adam da ke Unguwar Dosa, Kaduna, a bisa sadaki N70,000.

Juma’a, 18 ga Yuni:Tsohuwar fitacciyar jaruma Naja’atu Muhammad da fitaccen ɗan ƙwallon ƙafa Abdullahi Shehu, a Masallacin Umar Bin Khattab da ke Titin Zariya, Kano, a kan sadaki N50,000.

Asabar, 7 ga Agusta:Fitacciyar jaruma Zahra Muhammad (Diamond Zahra) ta yi aure a asirce.

Ibrahim Yala da amarya Halima Muhammad Kauru (Sima)

Juma’a, 20 ga Agusta:Fitaccen jarumi kuma mawaƙi Garzali Miko da Habiba Umar Ahmad Dikwa (Yarinya) a Masallacin Fajrul Islam da ke unguwar Rigasa, a kan sadaki N200,000.

25 ga Agusta:Fitacciyar mawaƙiya Maryam A. Baba (Sangandale) da matashin mawaƙi Abdul Kafinol sun cika shekara biyu da aure. Maryam ta wallafa hotunan da su ka ɗauka domin nuna murnar su a Instagram.

Asabar, 25 ga Satumba:Fitaccen furodusa kuma jarumi Abdullahi Abbas (Ubangari) da Zulaihat Ishaq Abdulrasheed, a Masallacin Adarawa, Jantiti, Rigasa, Kaduna, a bisa sadaki N200,000.

Laraba, 6 ga Oktoba:Fitaccen darakta kuma jarumi Al-Amin Ciroma da fitacciyar jaruma Wasila Isma’il sun wallafa hotuna kwafe bakwai a Instagram don murnar cikar su shekara 19 da aure.

Juma’a, 26 ga Nuwamba:Fitacciyar jaruma Maryam Musa Waziri da tsohon ƙan ƙwallon ƙafa Tijjani Babangida, a Kaltungo, Jihar Bauchi. 

Abdul Kafinol da Maryam A. Baba (Sangandale)
Abdullahi Abbas (Ubangari) da amarya Zulaihat Ishaq Abdulrasheed a wajen bikin auren su

Lahadi, 12 ga Disamba:Fitaccen mawaƙi Abdul D. One da Ummu-Salma (Salma Fresh), a Layin Transfomer, Kwanar ‘Yan Ghana da ke unguwar Tudun Murtala, Kano, a kan sadaki N100,000.

20 ga Disamba:Tsohuwar fitacciyar jaruma Fati Ladan da mijin ta Yerima Shettima sun cika shekara takwas da aure. Sun yaɗa hotunan murna. Daga bisani, Fati ta yi hirar musamman da mujallar Fim inda ta shawarci matan Nijeriya kan sirrin zama mai ɗorewa da mazajen auren su.

Juma’a, 24 ga Disamba:Fitaccen futodusa, marubuci kuma ɗan jarida Alhaji Ibrahim Sheme, ya aurar da ‘yar sa, Malama A’isha, ga sahibin ta, Malam Abubakar Muhammad Bello, a Masallacin Malam Khamis Al-Misri, da ke Titin Nnamdi Azikiwe, Western Bypass, kusa da Titin Dutsin-ma, Kaduna, a kan sadaki N100,000.

Al-Amin Ciroma da Wasila Isma’il tare da ‘ya’yan su huɗu lokacin da ma’auratan su ka yi bikin murnar cika shekara 19 da aure

HAIHUWA

Talata, 3 ga Agusta:Allah ya albakaci mawaƙi Sagir Ɗanyaro (Baban Kausar) da matar sa Fatima Muhammad da tagwaye duk mata. Fatima ta haihu a Asibitin Kadpoly, Kaduna. An raɗa wa jariran Hassana da Hussaina, amma mahaifiyar su na kiran su da Amna da Amra.

10 ga Agusta:Fitacciyar jaruma Jamila Umar Nagudu ta yi murnar zagayowar ranar haihuwar ta. Jamila, wadda uwa ce ga ɗan ta ɗaya, wato Mus’ab, ba ta shirya wani biki a bayyane ba, amma ta ɗora hotunan musamman da ta ɗauka domin wannan rana a Instagram.

Abdul D. One da amaryar sa Ummu-Salma Sulaiman (a tsakiya) tare da Ali Nuhu da matar sa Maimuna a wurin dinar auren

26 ga Satumba:Allah ya albarkaci fitaccen jarumi Mustapha Musty da matar sa Ghadir Mahmud Shareef da samun ɗan fari. Ghadir, wadda ake wa laƙabi da Soha, ta haifi santalelen yaro a birnin Kano.

Juma’a, 10 ga Oktoba:Fitaccen mawaƙi Nura M. Inuwa da matar sa Amina sun samu ƙaruwa da ɗiya mace a Kano. An raɗa jaririyar suna Amina (Mifra).

21 ga Oktoba:Fitacciyar jaruma Amal Umar ta cika shekara 23 da haihuwa. Don nuna murnar wannan rana, Amal ta wallafa hotunan ta da ta ɗauka a situdiyo a Instagram.

Jaruma Maryam Musa Waziri da angon ta Tijjani Babangida su na yi wa juna kallon ƙuda

Asabar, 6 ga Nuwamba: Allah ya azurta fittacen jarumi Adam A. Zango da Safiyya Umar Chalawa da ‘ya mace, a asibiti a Kaduna. An raɗa wa jarinya suna Furaira (Diana), sunan mahaifiyar Adam A. Zango.

Loading

Previous Post

Da daɗi, ba daɗi: Muhimman abubuwan da su ka faru a Kannywood a cikin 2021

Next Post

Yadda mutuwa ta ratsa Kannywood a cikin 2021

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Fitaccen jarumi Amude Booth a gaban kabarin mahaifiyar sa, Hajiya Zainab Musa Booth

Yadda mutuwa ta ratsa Kannywood a cikin 2021

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!