“Kullu nafsin za’ikatin mauti”. Haka Allah ya faɗa a cijin Alƙur’ani mai tsarki. Wato kowane rai sai ya ɗanɗani mutuwa.
A duk shekara, mutuwa ta kan yi wa ‘yan fim ɗin Hausa ɗauki ɗaiɗai: ko dai ta wuce da ɗan fim ko kuma wani nasa kamar uba ko uwa.
Hakan ya faru a bana. ‘Yan fim sun kwanta dama, wasu kuma sun yi rashin iyaye. Allah ya jiƙan rai!
A nan, mujallar Fim ta lissafa irin rashe-rashen da aka yi, ɗaya bayan ɗaya.
Juma’a, 5 ga Fabrairu:
Alhaji Isa Jibril Kibiya, mahaifin fitaccen mawaƙi Ali Isa Jita, ya rasu a unguwar Shagari Quarters cikin birnin Kano.
Lahadi, 14 ga Fabrairu:
Albania Muhammadu Sani Zangon Daura, mahaifin jaruma Asma’u Sani, ya rasu a gidan sa da ke unguwar Gama Tudu Birget da ke cikin birnin kano.
Laraba, 3 ga Maris:
Allah ya ɗauki ran fitaccen jarumi Sadiq Daba. Ya rasu a babban asibitin Ayinka da ke unguwar Ikeja, a Legas.

Talata, 16 ga Maris:
Allah ya yi wa fitacciyar zabiyar waƙoƙin yabon Manzon Allah (s.a.w.) Rabi’atu S. Haruna rasuwa a gidan mijin ta da ke Layin Ɗangaladima a Titin Abuja, unguwar Rigasa, Kaduna.
Laraba, 18 ga Afrilu:
Alhaji Jibril Giɗaɗo, mahaifin fitacciyar jaruma Maryam Giɗaɗo, ya rasu a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH), a Jihar Filato.
Alhamis, 29 ga Afrilu:
Allah ya ɗauki ran tsohon jarumi Ibrahim Mu’azzam a Kano.
Alhamis, 6 ga Mayu:
Allah ya ɗauki ran jaruma Khadija Abubakar Mahmud, a garin Jalingo, babban birnin Jihar Taraba.

Talata, 22 ga Yuni:
Hajiya Hadiza Muhammad, mahaifiyar jarumi A.S. Muhammed, ta rasu a Sabon Gayan, Jihar Kaduna.
Alhamis, 1 ga Yuli:
Allah ya ɗauki ran fitacciyar jaruma Zainab Booth a Kano sakamakon tiyatar ƙwaƙwalwa da aka yi mata.
Asabar, 10 ga Yuli:
Malam Muhammad Adamu, mahaifin jaruma A’isha Muhammad Adam, ya rasu a asibiti a Kano.
Asabar, 1 ga Agusta:
Allah ya ɗauki ran tsohuwar shugabar ƙungiyar furodusoshi mata a farko, Hajiya Umma Ali, a Asibitin Premier da ke Kano.
Lahadi, 2 ga Agusta:
Hajiya Bilkisu Sheriff Adam, mahaifiyar fitaccen mawaƙi Aminu Ladan Abubakar (ALA), ta rasu a Kano.

Asabar, 4 ga Satumba:
Allah ya ɗauki ran fitaccen mawaƙin siyasa Isyaku Muhammad (Forest) a wani asibitin kuɗi da ke Titin Karkasara, Kano.
Asabar, 12 ga Satumba:
Allah ya ɗauki ran fitaccen jarumin barkwanci Malam Aliyu Ahmad Tage a Kano.
Laraba, 12 ga Satumba:
Allah ya ɗauki ran fitaccen jarumi Yusuf Barau a asibitin Isolation Centre da ke Down Quarters, Kakuri, Kaduna.
Asabar, 18 ga Satumba:
Hajiya Hauwa S.U. Garba, mahaifiyar fitacciyar jaruma Fati S.U. Garba, ta rasu a asibitin IBB Specialist Hospital da ke Minna, Jihar Neja.

Talata, 21 ga Satumba:
Allah ya ɗauki ran shugaban mawaƙan Kaduna, Alhaji Sani Shu’aibu (Ciyaman), a gidan sa da ke Titin Maƙera, unguwar Rigasa, Kaduna.
Lahadi, 3 ga Oktoba:
Mawaƙi Sanusi Panbeguwa ya rasa ‘ya’yan sa biyu, Khaleed da Tasi’u, a cikin motar sa da ke fake a ƙofar gidan sa a garin Panbeguwa, Jihar Kaduna.
Lahadi, 3 ga Oktoba:
Farfesa Sule Bello, wanda babban mai tallafa wa harkar adabi a Nijeriya, ciki har da harkar finafinan Hausa ne, ya rasu bayan gajeren rashin lafiya. Ya rasu a Zariya, ya na da shekaru 73 a duniya. Kafin rasuwar sa, babban malami ne a Sashen Tarihi na Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, kuma shi ne shugaban wani tsagi na jam’iyyar PRP na ƙasa.
Alhamis, 28 ga Oktoba:
Nana Firdausi Nuhu, matar mawaƙi El-Bash Muhammad, ta rasu a gidan mijin ta da ke Green Fingers, unguwar Rigachikun, Kaduna.
Juma’a, 29 ga Oktoba:
Allah ya ɗauki ran shahararren marubuci, kuma ɗan wasan kwaikwayo, Alhaji Umaru Ɗanjuma Katsina (Kasagi), a Katsina. Ya rasu mako ɗaya bayan ya halarci bikin baje kolin littattafan Hausa da su Farfesa Ibrahim Malumfashi su ka shirya.
Talata, 16 ga Nuwamba:
Alhaji Sani Labaran, mahaifin fitaccen jarumi Umar Gombe, ya rasu a Asibitin Gwamnatin Tarayya, ‘Federal Medical Centre’, da ke Gombe.

Laraba, 15 ga Disamba:
Allah ya yi wa fitaccen jarumi Sani Garba SK rasuwa. Ya rasu ne a Asibitin Muhammadu Abdullahi Wase da ke unguwar Nasarawa, cikin birnin Kano, bayan ya yi fama da rashin lafiya.
![]()






