HUKUMAR Tace Finafinai ta Jihar Kano ta bayyana sunayen mutane uku a matsayin waɗanda suka yi nasara a gasar ƙirƙirarren labari da hukumar ta saka.
Waɗanda suka lashe gasar su ne Ɗanladi Z. Haruna da labarin sa, ‘Gadon Gida Sai Da Horo’, Hauwa Shehu da labarin ta, ‘Bahaushe Mai Arziki Ne’, da Zubairu Musa Ballannaji da labarin sa, ‘Bahaushiyar Al’ada.’
Hukumar ta bayyana 31 ga Disamba, 2024 a matsayin ranar da za ta karrama waɗanda suka yi nasara tare da ba su kyaututtuka a Gidan Mambayya da ke Gwammaja, Kano.
Sai dai wasu marubutan sun yi ƙorafin cewa dukkan zakaru uku na gasar ‘yan Kano ne.
Wata marubuciya da ta shiga gasar daga Jihar Kaduna ta faɗa wa mujallar Fim cewa, “Ni tun da na ga jerin sunayen gwaraza goma sha biyar da aka fitar waɗanda daga cikin su za a zaɓi uku a matsayin zakaru, na ce lallai akwai wata a ƙasa! Kusan dukkan su ‘yan Kano ne, sai wasu tsirarun mata, ɗaya daga ƙasar Nijar, sai wata daga Kaduna da wata daga Jos. An dai tuwo-na-mai-na kawai, ko in ce dakan ɗaka shiƙar ɗaka.”
Fitaccen marubuci, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, shi ne shugaban kwamitin alƙalan gasar.