• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, August 10, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Buri na in auri marubuci ɗan’uwa na, inji marubuciya Gimbiya Rahama

by ABBA MUHAMMAD
November 23, 2024
in Marubuta
0
Buri na in auri marubuci ɗan’uwa na, inji marubuciya Gimbiya Rahama

Gimbiya Rahama

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MATASHIYAR marubuciya Rahama Ahmad Muhammad, wadda aka fi sani da Rahama Gimbiya a fagen rubutu, haziƙar matashiya ce wadda tauraron ta ke haske a yau. Ta kasance marubuciya mai kaifin basira, wanda hakan ya sa ta samu karramawa daga ƙungiyoyi da dama.

Mujallar Fim ta samu damar zantawa da Gimbiya Rahama, inda ta feɗe mana biri har wutsiya game da tarihin ta, yadda ta tsinci kan ta a harkar rubutu, burin ta, yaren ta, da sauran su.

FIM: Ki faɗa mana tarihin rayuwar ki a taƙaice.

GIMBIYA RAHAMA: Da farko suna na Rahama Ahmad Muhammad, wadda aka fi sani da Gimbiya Rahma a fagen rubutu. An haife ni a garin Kano, cikin tsakiyar birni. Na yi makaranta tun daga firamare har zuwa sakandire haɗe da makarantar allo da Islamiyya tare da makarantar gaba da sakandire duk a cikin garin Kano.

FIM: Ke wace yare ce?

GIMBIYA RAHAMA: Ni Bahaushiya ce.

FIM: Shekarun ki nawa?

GIMBIYA RAHAMA (Dariya): Shekaru ai sirri ne, amma ban fi ashirin da ɗoriya ba.

FIM: Ya aka yi kika tsinci kan ki a harkar rubutu?

GIMBIYA RAHAMA: Na tsinci kai na a harkar rubutun littafi tun ina ƙaramar yarinya, lokacin ina makarantar firamare. Na fara rubutu tun kusan shekara goma sha biyar baya, amma rubutun bai fara ba sai da na shiga ƙaramar sakandire, har ta kai ga na fara rubuta dirama.

FIM: Da wane littafi kika fara?

GIMBIYA RAHAMA: Da littafin ‘Zamantakewa’ na fara.

FIM: Kin rubuta littattafai aƙalla guda nawa?

GIMBIYA RAHAMA: Littattafai na manyan da ƙananan labarai a yanzu za su kai ashirin da ɗoriya.

FIM: Littattafan ki guda nawa ne suka shiga kasuwa?

GIMBIYA RAHAMA: Littattafai guda biyu ne suka fita, ‘Aljannar Mace’ da kuma ‘Ƙani Na’.

FIM: Waɗanne irin ƙalubale kika fuskanta a harkar rubutu?

GIMBIYA RAHAMA: Ƙalubale kam an fuskanta mai tarin yawa! Sai dai fatan kar hakan sake faruwa in-sha Allah.

FIM: Ɓangaren nasarori kuma fa?

GIMBIYA RAHAMA: Alhamdu lillah! Nasara kam na same ta mai tarin yawa a harkar rubutu. Irin nasarorin da baki ba zai iya misalta su ba, tun daga suna, jama’a, kuɗi da karramawa.

A silar rubutu na haɗu da manyan mutanen da ban taɓa mafarkin haɗuwa da su ba a rayuwa ta, na sami karramawa ta satifiket sama da guda ashirin daga mabambanta ƙungiyoyi. A kuma silar rubutu na shiga manya da ƙananan gasar rubutu tun daga na zube har zuwa na waƙa, wasu an yi nasara wasu kuma ba a yi ba, duk da yake ita ma faɗuwar nasara ce.

FIM: Kin taɓa samun lambar yabo a kan rubutu?

GIMBIYA RAHAMA: Na samu lambobin yabo sama da guda ashirin, satifiket da awad.

FIM: Kin taɓa shiga gasar Hikayata ta BBC Hausa?

GIMBIYA RAHAMA: E, na fara shiga gasar BBC tun daga shekarar 2018 a jere har zuwa wannan shekarar ban yi fashi ba.

FIM: Menene burin ki game da rubutu?

GIMBIYA RAHAMA: Babban buri na a harkar rubutu na auri marubuci, kuma na ci gaba da cin gajiyar sa har ƙarshen rayuwa ta.

FIM: Kin taɓa rubuta labarin fim?

GIMBIYA RAHAMA: Na taɓa rubutawa sau kusan uku. Amma kasancewar ba babban darakta na rubuta wa ba, hakan ya sa aikin ɗaukar shirin bai je ko’ina ba aka daina.

FIM: Wane fim aka taɓa yi da labarin ki?

GIMBIYA RAHAMA: Ba labarin littafi ba ne ya zama a fim, ƙirƙirarren labarin fim ɗin ne aka rubuta. ‘So Da Kuɗi’ sunan ɗaya daga ciki.

FIM: Wane marubuci ko marubuciya kike kallo a matsayin gwani ko gwanar ki?

GIMBIYA RAHAMA: A maza Ayuba Muhammad Ɗanzaki, sai El-Ameen Daurawa tare da Jibrin Adamu Rano. A mata kuma Fatima Ibrahim Garba da Fauziyya D. Sulaiman.

FIM: Yanzu yawancin marubuta sun koma onlayin. Ita ma Rahama ta koma onlayin ɗin ne?

GIMBIYA RAHAMA: Da fari ni marubuciyar ɗab’i ce, to duba da yadda kasuwar adabin ta juya, kuma manyan marubutan ba sa taimakon ƙanana, hakan ya sa na koma cikin ƙanana iri na tun a wancan lokacin, sai dai a yanzu ni na tashi daga ƙaramar marubuciya zuwa babbar marubuciya, shahararriya wacce ludayin ta ke kan dawo, marubuciyar ‘Kallon Kitse’, ‘Cutar Numfashi’ da littafin ‘Ƙani Na’.

FIM: Kina da aure?

GIMBIYA RAHAMA: A’a, har yanzu ni budurwa ce.

FIM: Menene saƙon ki ga masoyan ki?

GIMBIYA RAHAMA: Masoya na su shirya nan kusa in-sha Allah zan fito da sababbin littattafai na waɗanda na fara rubutawa tun shekarun baya ban kammala ba, da wasu sababbi fil, duk nan ba da jimawa ba.

FIM: Mecece shawarar ki ga marubuta ‘yan’uwan ki?

GIMBIYA RAHAMA: Shawara ta ga ‘yan’uwa na marubuta, mu ci gaba da riƙe sirrin juna tare da yin bincike kafin rubutu.

Loading

Tags: adabiGimbiya Rahamalittattafaimarubuciyamarubutaonlayin
Previous Post

Kotu ta dakatar da gwamnatin Kano daga yin shari’a da Rarara

Next Post

Rarara zai gina masallaci a Sumaila

Related Posts

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro
Marubuta

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro

January 10, 2026
Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama
Marubuta

Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama

December 25, 2025
‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa
Marubuta

‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa

December 25, 2025
Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo
Marubuta

Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo

December 24, 2025
Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu
Marubuta

Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu

December 19, 2025
Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata
Marubuta

Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata

December 8, 2025
Next Post
Rarara zai gina masallaci a Sumaila

Rarara zai gina masallaci a Sumaila

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!