• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, November 2, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Dakta Muhammadu Uba Adamu (Kantoma), 1935-2020

by DAGA IBRAHIM SHEME
April 28, 2020
in Nijeriya
0
Dakta Muhammad Uba Adamu

Dakta Muhammad Uba Adamu

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un! A jiya Litinin, 27 ga Afrilu, 2020 Allah (swt) ya yi wa Dakta Muhammadu Uba Adamu, tsohon Kantoman Kano, rasuwa. Mutumin unguwar Daneji cikin Birnin Kano ne, amma gidan sa na Kawo Bus Stop a Nassarawa, kusa da unguwar Giginyu. 
 
Ya rasu da misalin ƙarfe 6:40 na yamma, daf da shan ruwa, a Asibitin Nassarawa, Kano. Ya bar mata biyu, ‘ya’ya 17 da jikoki fiye da 54. 
 
Babban ɗan sa shi ne Farfesa Abdalla Uba Adamu, Mataimakin Shugaba (Vice-Chancellor) na Buɗaɗɗiyar Jami’ar Nijeriya (National Open University of Nigeria, NOUN) wadda ya karɓi ragamar jagorancin ta a shekarar 2016,  kuma zai ƙare wa’adin sa na shekara biyar a Fabrairu, 2021. 
 
Iyalan marigayin sun ce bai yi wata cuta, jinya ko rashin lafiya ba, sai dai tsufa. Tashi ɗaya abin ya zo masa da safe, Allah ya karɓe shi daf da shan ruwan azumin ranar 4 ga Ramadan. Sun ce a rayuwar sa gaba ɗaya, sau huɗu ya taɓa kwanciya a asibiti. Wannan kwanciyar ita ce ta huɗun, kuma ta ƙarshe. 
 
An haifi Dakta Muhammadu Uba Adamu a Daneji a ranar 10 ga Disamba, 1935, a gida mai lamba 147, wadda yanzu ta koma lamba ta 97. Watau dai ya rasu ya na ɗan shekara 85 kenan.
 
Shi ne na uku a cikin ‘ya’ya biyar da su ka rayu waɗanda iyayen su su ka haifa. Sauran, ban da ƙanin sa, Alhaji Ɗanbala Adamu, mata ne, kuma duk Allah ya yi masu rasuwa da jimawa. 
 
Marigayin ya fara karatun sa na boko a ‘Shahuci Judicial School’, daga nan ya tafi ‘School for Arabic Studies’, sannan sai kuma ya tafi ‘Abdullahi Bayero College’ wadda ta zama Jami’ar Bayero, Kano, wadda kuma ya gama a 1968 da digirin farko a fannin Tarihin Siyasa (Political History). 
 
Ya je Jami’ar Ife da ke Ile Ife (wadda yanzu ake kira Jami’ar Obafemi Awolowo) inda ya yi gajeren kwas a kan nazarin Mulkin Jama’a (Public Administration).
 
Tun Malam Muhammadu ya na makaranta ya ke da sha’awar rubuce-rubuce, a inda ya rubuta wata maƙala mai taken ‘Some Notes on the Influence of North African Traders in Kano (1968), aka buga ta a mujallar ‘Kano Studies’. A cikin ta, ya yi bayani a kan yadda Larabawan Libya, Misira da Marokko mazauna Kano su ka mamaye Kano da al’adun su na ɗarika da kuma ire-iren abincin su da tufafi, har Hausawa su ka mayar da su nasu.  
 
An naɗa shi Di’o (District Officer) na Ɗambatta a cikin 1969, watau a zamanin mulkin Gwamna Audu Bako. A 1970 aka naɗa shi Kantoman Kewayen Kano (Kano Local Authority), wanda hakan ya sa ya zama kamar Magajin Gari. 
 
A zamanin sa ne aka yi gyaran Kano sosai, aka kuma zamantar da ita, kuma shi ya jagoranci kwamitin mayar wa da ƙabilar Ibo kadarorin su da aka dinga wawaso lokacin yaƙin Biyafara (1967-1970) a Sabon Garin Kano, kuma ya tabbatar da an mayar wa da kowa haƙƙin sa. 
 
Saboda irin aikin da ya yi ne ya sa shahararren marubucin waƙoƙin nan, marigayi Dakta Aƙilu Aliyu, ya rubuta masa waƙar yabo a 1971 mai suna ‘Zan Je Ziyarar Shugaba Dattijo Kantoma Uba’. Ya rubuta ta ne da ajami kuma ya kai wa Kantoma ita har gida a cikin 1974 saboda jinjinawa. 
 
Dakta Muhammadu Uba Adamu ya bar aikin Kantoma a 1975, sannan ya tafi University of Pennyslvania da ke Amurka ya ƙaro digiri na biyu a cikin 1976. Da ya dawo aka naɗa shi Babban Malami (Senior Lecturer) a fannin Mulkin Jama’a (Public Administration) a ‘School of Management’, Kano a Janairu 1979. Ya na aikin ya yi rijistar digiri na uku, watau PhD, a Jami’ar Bayero a fannin Kimiyyar Mulki (Political Science) inda ya gama a 1995. 
 
Ya yi ritaya daga aikin gwamanati a cikin 1995 ya na da shekaru 60, wato jim kaɗan da gama karatun sa na PhD, domin ya yi karatun ne da ma domin ƙara wa kan sa ilimi, ba domin neman cigaba wajen aiki ba. 
 
Bai tsaya a nan ba, sai ya shiga rubuce-rubucce. Littafin da ya fara rubutawa shi ne ‘Confluences and Influences: The Emergence of Kano as a City State’ (1999). Littafin ya samu karɓuwa, saboda haka nan da nan ya ƙare. Yanzu haka Farfesa Abdalla na da niyyar sabunta littafin domin fitowa da shi a baɗi. 
 
Amma saboda muhimmacin littafin wajen tarihin Kano, sai Hukumar A Daidaita Sahu, a yadda ta ke a wancan lokacin, ta ɗauki alƙawarin cewa in ya fassara littafin zuwa Hausa, su kuma za su ɗaukin nauyin ganin an yi ɗab’in littafin a maɗaba’ar ta gwamnatin Kano, ba sai ya biya ba. Nan da nan ya fara aikin fassara da kuma ƙarin bayani a kan wancan na Turancin. Kuma ya dinga kai fassarar Jami’ar Bayero saboda ƙwararru su inganta ta. 
 
Daga bisani Hukumar A Daidata Sahu ta buga sakamakon a littattafai guda biyar a 2007 masu  taken ‘Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri’. 
 
Waɗannan su ne:
 
Vol. 1: Kano Daga Dutsen Dala;
 
Vol. 2: Kano Daga Kwazazzabon ‘Yar Kwando;
 
Vol. 3: Kano Da Maƙwabtan Ta;
 
Vol. 4: Kano Daga Garko;
 
Vol. 5: Kano Daga Dutsen Bompai.
 
Sannan ya na bincika takardun sa sai ya ga waƙar Aƙilu Aliyu a 1974. Sai ya fara tunanin yin abubuwa biyu – rattaba tarihin abin da ya jawo waƙar, watau ayyukan da su ka yi na gyaran birnin Kano, lokacin marigayi Gwamna Audu Baƙo, da kuma waƙen ayyukan. Duk ya haɗe su a littafin da ya rubuta mai suna ‘Tuna Baya’ (2009). 
 
Hukumar KNUPDA ta Kano ita ta ɗauki nauyin buga littafin. Amma bai yi wannan ba sai da ya gama rubuta littattafan ‘Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri’ wanda A Daidaita Sahu’ ta ɗauki nauyin sa.  
Marigayi Dakta Muhammadu Uba Adamu (a hagu) tare da ɗan sa, Farfesa Abdalla … cikin Janairu 2017. Hoto daga: Abdulrahman Abdullahi
Bayan waɗannan, ya rubuta ‘Sabon Tarihin Asalin Hausawa’ (2011), inda ya danganta Hausawa da wani Fir’auna mai suna Housal a Misra wanda ya taho da mutanen sa, abin da ya zama ƙasar Hausa daga baya. 
 
A cikin 2011 sai Allah ya sa su ka haɗu da shahararren fasihin mawaƙin nan, Aminudeen Ladan Abubakar, wanda aka fi sani da ALA a Zoo Road, Kano. Bayan ALA ya gaishe shi, sai Kantoma ya ce ai shi ma ya na rubuta waƙoƙi amma ba shi da muryar da zai rera. Nan take ALA ya ce shi zai yi. Su ka koma gidan Kantoma inda shi Kantoman ya bai wa ALA waƙoƙin sa na gyaran Kano. ALA ya shiga situdiyo ya yi abin da ya saba – wato rera waƙoƙi cikin natsuwa. Sakamakon shi ne faifan sidi mai suna ‘Duniya Makaranta’, wanda ya ƙunshi waƙoƙi kamar haka:
 
1. Bolar Kano (24:34)
 
2. Hassada (10:47)
 
3. Badar (20:59)
 
4. Ɗan Maraya (12:49)
 
Idan akwai wani abu da ya ke faranta wa marigayi Dakta Muhammadu Uba Adamu rai a rayuwa, shi ne waɗannan waƙoƙin wanda har ya kusan komawa ga mahaliccin sa ya na sauraron su da na’urar ‘MP3 player’. Idan ya na sauraro, sai a ga fuskar sa cike da kwanciyar hankali domin tunawa da baya da kuma jin daɗin yadda ALA ke fito da ainihin abubuwan da su ka faru a cikin baitukuan. 
 
Allah ya gafarta masa da rahama, amin.

Loading

Previous Post

Mahaifin Farfesa Abdalla ya kwanta dama

Next Post

Waƙar gyaran Kano ta Aƙilu Aliyu

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Dakta Akilu Aliyu (a hagu) da Dakta Muhammadu Uba Adamu

Waƙar gyaran Kano ta Aƙilu Aliyu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!