SHIRYE-SHIRYE sun kankama na gudanar da wani gagarumin bikin baje-kolin littattafai da fasahohin Hausa a Kaduna a cikin wannan watan na Oktoba.
Bikin na ƙasa da ƙasa, wanda a Turance ake kira ‘Hausa International Books and Arts Festival’ (HIBAF 2021), zai gudana ne daga ranar 21 zuwa 23 ga Oktoba, 2021 a Gidan Sardauna (Arewa House) da ke Kaduna.
Wani kamfani mai zaman kan sa da ke Kaduna mai suna ‘Open Arts’, shi ne ya ke shirya bikin.
A takardar gayyata da mujallar Fim ta samu, jagoran shirya bikin, wanda kuma shi ne shugaban ‘Open Arts’, Malam Sada Malumfashi, ya bayyana cewa wannan biki za a yi shi ne tare da haɗin gwiwar Jami’ar Bristol ta Ingila.
Ya ce, “Burin bikin shi ne ya nuna kyawawan ayyukan adabin Afrika da aka samar a wannan zamani a fagen rubutattun waƙoƙi, kaɗe-kaɗe, zane-zane da wasannin kwaikwayo cikin harshen Hausa ga dubban matasa a faɗin Afrika ta Yamma.
“Jigon taron na bana shi ne “Fagage” (“Spaces”a Turance) inda bikin zai duba asalin samuwar adabin Hausa tare da tattauna batutuwa kamar jinsi, asali, al’adu da siyasa.”
Malam Sada ya ƙara da cewa manufar bikin na HIBAF shi ne ya haɗo fagen ƙirƙira da fagen zahiri, ya nazarce su don gane inda aka fito da kuma inda aka dosa.
A wata sanarwar ƙarin bayani da masu shirya bikin su ka aiko wa mujallar Fim, sun zayyana abubuwan da aka tsara gudanarwa a lokacin bikin, waɗanda su ka haɗa da koyar da dabarun rubuta labari, musamman ga matasan marubuta.
An buƙaci duk mai son shiga wurin bitar da ya aika da tsakuren labari da bai wuce kalma 500 ba, domin tantancewa, amma kada a wuce ranar 10 ga Oktoba ba a aika da shi ba.
Haka kuma akwai baje-kolin fasahar waƙa daga mawaƙan Hausa, inda za a ba marubuta waƙa damar ɓarje gumin su a fage na musamman da aka ba taken “Waƙa Daga Bakin Mai Ita.”
Ana sa ran marubuta waƙoƙin Hausa za su aika da waƙar su wadda ba ta wuce layi 40 ba, amma ba a iyakance jigo ko nau’in ƙwar ɗin waƙar ba.
An bayyana 15 ga Oktoba a matsayin rana ta ƙarshe ta karɓar waƙar da za a aika.
Adireshi biyu na imel inda za a aika da tsakuren labari ko rubutacciyar waƙa su ne:
openartsng@gmail.com ko hibaf@openartsworld.org
Sanarwar ta ce za a yi baje-kolin littattafai a rumfuna daban-daban da aka tanada domin masu cinikayya.
Har wa yau duk wanda zai sayi littafi an samar da garaɓasa ta zaftare farashin kowane littafi da kashi 15 cikin ɗari na asalin farashin sa. Wannan kuwa gudunmawa ce daga Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal, ga duk mahalarta domin cigaban Hausa da Hausawa.
Bugu da ƙari, za a gabatar da laccoci na musamman da su ka shafi tarihi da al’adu da adabi da nahawu da sauran batutuwa waɗanda su ka jiɓanci Hausawa.
Akwai filayen nishaɗi da wargantawa da ke fito da ƙimar Bahaushe a idon duniya a yayin bikin.
Sanarwar ta ce domin tanadin mazauni a wannan gagarumin biki na kwana uku, za a yi rajista da N1,000 ta hanyar aikawa da kuɗin ta ɗaya daga cikin waɗannan asusun bankunan:
1. Lambar Asusu: 0076260305
Banki: Sterling Bank Plc
Sunan asusu: Open Arts Development Foundation.
2. Lambar Asusu: 0560976738
Banki: Guaranty Trust Bank Plc
Sunan asusu: Open Arts Development Foundation.
Ana so idan mutum ya aika da kuɗin sai kuma ya tura saƙon tes kai-tsaye zuwa ga wannan lambar waya: 08124157817 ko kuma a tuntuɓa ta WhatsApp a wannan lamba: 08147326215.
Sannan kuma ana iya biya kai-tsaye ta wannan liƙau ɗin:
https://www.openartsworld.org/attend/
Idan an zaɓi biyan kuɗi ne a ranar bikin, an tanadi waɗanda za a yanki rasiɗi a wurin su kafin a sami damar isa ga mazaunin bikin, ko da yake a wannan yanayi kuɗin rajista zai koma N2,000 ne.
A ƙarshe, mashirya taron sun kira wannan taron da sunan “biki ɗaya tamkar da goma.”