• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Jami’ar MAAUN ta bayyana kyautar digirin girmamawa ga zabiya Magajiya Ɗambatta, kwana biyu bayan rasuwar ta

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
October 10, 2021
in Mawaƙa
0
Marigayiya Magajiya Ɗambatta a 1992 (a hagu) da kuma cikin 2019  

Marigayiya Magajiya Ɗambatta a 1992 (a hagu) da kuma cikin 2019  

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

KWANA biyu yau da rasuwar fitacciyar zabiya Magajiya Ɗambatta, Jami’ar Maryam Abacha ta ƙasar Nijar (Maryam Abacha American University of Niger, MAAUN) ta bayyana cewa za ta ba ta digirin girmamawa.

Haka kuma jami’ar, mai reshe a Kano, ta raɗa wa ginin sashen Tsangayar Shari’a ɗin ta da ke Kano sunan zabiyar.

Shugaba kuma mamallakin jami’ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, shi ne ya bayyana haka a cikin takardar ta’aziyya da ya aiko wa manema labarai daga ƙasar Faransa a yau Lahadi, 10 ga Oktoba, 2021.

A saƙon nasa, ya bayyana rasuwar shahararriyar mawaƙiyar a matsayin babban rashi ga ɗaukacin al’ummar arewacin Nijeriya.

A saƙon, Farfesan ya ce bayan sun yi la’akari da gudunmawar da marigayiyar ta bai wa al’umma ta hanyar faɗakarwa ne hukumar gudanarwa ta jami’ar ta sanya wa ginin sunan ta baya ga niyyar su ta karrama ta da digirin girmamawa na bayan rasuwa, wato ‘posthumous honorary degree’.

Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo

Ya ce, “Don girmama marigayiya Magajiya Ɗambatta (Halima Malam Lasan) da gudunmawar da ta bayar a fannin ilimi, mun yanke shawarar karrama ta da digirin girmamawa bayan rasuwa.”

Ya ƙara da cewa, “Mun yi shirin karrama ta a lokacin ta na da rai, amma sai ta rasu kafin lokacin taron.”

Kuma ya ce, “Za mu yi rashin barkwancin ta da shahararrun waƙoƙin ta.”

Farfesa Gwarzo, wanda kuma shi ne shugaban Ƙungiyar Jami’o’i masu Zaman Kan Su ta Afirka, ya bayyana rashin Magajiya Ɗambatta a matsayin abin takaici. 

Ya ce a madadin iyalan sa da hukumar gudanarwar ‘Maryam Abacha American University’ da ‘Franco-British International University’, ya na miƙa ta’aziyya ga iyalai da abokan arzikin marigayiyar da ma ɗaukacin al’ummar Jihar Kano da Nijeriya baki ɗaya.

Ya yi addu’ar Allah maɗaukakin sarki ya saka wa marigayiyar da gidan Aljannar Firdausi kuma ya ba iyalin ta juriyar haƙurin rashin ta.

Hoton da mujallar Fim ta tsakura daga bidiyon wani wasan Magajiya Ɗambatta a FRCN Kaduna a 1992

Ita dai Halima Malam Lasan, wadda aka fi sani da Magajiya Ɗanbatta, ta rasu ne a shekaranjiya Juma’a, 8 ga Oktoba, 2021, a babban asibitin garin Ɗambatta da ke Jihar Kano, ta na da shekaru 85 a duniya.

Loading

Tags: Franco-British University InternationalHalima Malam LasanMAAUNMagajiya ƊambattaMaryam Abacha American University of Nigermawakan hausamutuwaposthumous honorary degreeProf. Adamu Abubakar Gwarzozabiya
Previous Post

Hotuna: Wasila Isma’il ta yi murnar zagayowar ranar haihuwa

Next Post

Dalilin mu na shirya bikin baje-kolin littattafai da fasahohin Hausawa – Sada Malumfashi

Related Posts

Za a gabatar da littafin waƙoƙin Salma ɗiyar marubuciya Halima K Mashi ran Asabar
Mawaƙa

Za a gabatar da littafin waƙoƙin Salma ɗiyar marubuciya Halima K Mashi ran Asabar

August 23, 2026
‘Ya’ya biyu mata na Mudassir Kasim sun yi saukar karatun Alƙur’ani
Mawaƙa

‘Ya’ya biyu mata na Mudassir Kasim sun yi saukar karatun Alƙur’ani

August 2, 2026
Sani Danja: Waƙar ‘Barau Jigijim’ ta tayar da ƙura, ya ƙaddamar da gasa a kan ta
Mawaƙa

Sani Danja: Waƙar ‘Barau Jigijim’ ta tayar da ƙura, ya ƙaddamar da gasa a kan ta

July 15, 2026
Za a yi bikin naɗa Rarara Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa a Daura ranar Asabar
Mawaƙa

Za a yi bikin naɗa Rarara Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa a Daura ranar Asabar

December 11, 2025
Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi
Mawaƙa

Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi

April 19, 2025
Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala
Mawaƙa

Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala

October 28, 2024
Next Post
Malam Sada Malumfashi da fostar bikin baje-kolin 'HIBAF 2021'

Dalilin mu na shirya bikin baje-kolin littattafai da fasahohin Hausawa - Sada Malumfashi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!