WANNAN labarin da za ku karanta ya faru da gaske, ba tatsuniya ko ƙage ba ne.
Ni ne mutum na farko da ya fara shiga tsakanin Hauwa Ibrahim da ‘yan jarida bayan ta fara shiga rigingimu. Hauwa Ibrahim, wacce ta shahara da suna Ummi Zee-Zee, da kan ta ta buƙaci hakan daga gare ni, duk da kuwa a lokacin bai fi shekara biyu da na shiga harkar jarida ba.
Wani abu ne ya faru a watan Janairu, 2009, lokacin ina Editan Mujallar Matasa, wata mujalla da ta yi tashe lokacin mulkin marigayi ‘Yar’Adua, wacce kamfanin Katsina Media Links mallakin Malam Ɗanjuma Katsina, ke wallafawa. Mun buga wani labari a shafin Tauraruwa Mai Wutsiya, mai taken: “Illolin Shaye-shaye Ga Matasa: Darussa Daga Rayuwar Lil Wayne”. Ni na rubuta labarin bayan dogon nazari kan yadda harkar shan miyagun ƙwayoyi ta raunata rayuwar mawaƙi Lil Wayne, kuma a wancan lokacin shi ne abin koyi ga matasa.
A kan wannan labarin ne Ummi ta kira ni, ta na nuna rashin jin daɗi. A cewar ta, wai mun zagi mawaƙi mai tasiri a duniya. Ni ban ma san ta ba, saboda ban san kowa a harkar fim ba. Ta gama faɗin ra’ayin ta sannan ta kashe waya. Kafin ta fara magana ta gabatar min da kan ta da sunan Zainab Ibrahim (ba ta ce Ummi Zee-Zee ba).
Bayan kamar kwana biyu, sai aka sake kira na da wannan lambar ta Glo, ban yi ‘saving’ layin ba, amma ina gani na iya tuna an kira ni da lambar. Ta na magana cikin isa da izza ta ce, “Zainab ce”. Na ce, “Allah sarki!” Nan ne ta fahimci ban ma yi ‘saving’ lambar ba. Ta cika da mamaki, ta ce, “Ka yi laifi biyu. Na farko kun zagi Lil Wayne, na biyu ka ƙi ‘saving’ lamba ta.”
Sai mu ka yi dariya.
Lokacin da za ta kashe waya, bayan mun gama magana, sai ta ke ce min ai ‘yan jarida na da ƙarfin ikon gyara abu ko ɓata shi. Za ta so idan ta dawo Nijeriya mu tattauna. Lokacin ta na ƙasar Misra, ta je hutawa. Ni a lokacin ba ta ita ma na ke ba, saboda kai na ya ɗau zafi, mu na kici-kicin tsara mujallar mu ta Fabrairu, 2009.
Bayan watanni kamar uku sannan na gane ashe Ummi Zee-Zee ce ‘Zainab Ibrahim’ ɗin da ke kira. A ranar da wani ke faɗa min cewa ita ce, a rannan ta sake kira na a waya. A ranar mu ka fara haɗuwa. Ta gabatar min da wasu ƙorafe-ƙorafe kan abubuwan da ake wallafawa a kan ta. Ta nuna min wasu gidajen ta a garin da mu ka haɗu, ba Kano ba.
A lokacin da gaske akwai ‘yan kuɗaɗe hannun Ummi, sai dai ba zan iya cewa sun kai nawa ba. A lokacin ta na hawa motoci guda shida da ”customized number’ mai ɗauke da lambobi Zee-Zee 1, 2, 3, 4,5, 6. Da su ta ke yawo a Kano, Kaduna da Abuja.
Mu’amala ta da Ummi kawai harkar jarida ce. Duk da yake a lokacin ba ni da wata cikakkiyar gogewa a harkar jarida, amma na yi ƙoƙari wurin ba ta shawarwarin da na ke ganin ba kawai a harkar mu’amala da ‘yan jarida ba, zai taimaka mata wurin mu’amala da mutane da sauƙaƙe rigimar da ta ke faɗawa.
Lokacin da tsohon saurayin ta, Abdullahi Ɗan Chana, ya sako ta gaba, ni ke bada shawarar me za a yi, me kuma za a rubuta. A lokacin ta na tsananin ba ni tausayi ne, saboda irin tarin rigingimun da ke kan ta. Har ta kai wasu cikin ‘yan’uwan ta sun san ni.
Ta sake fuskantar sabon babin rigima ne bayan da ta koma Fatakwal da irin abubuwan da su ka shiga tsakanin ta da su Timaya, Jonah de Monarch da Weatherman. Da gaske ne Timaya ya amshi kuɗaɗe a hannun ta da sunan waƙa da soyayya.

Akwai wani abu da ya faru har ta kai na shiga tsakani. Jonah De Monarch, wanda su ka yi waƙar ‘Janglover’ tare ne ya so ya damfare ta. Ƙarshe dai ni aka nema na shiga tsakani, har sai da ta kai Jonah ya yi ta surfa min zagi. Da na ga abin hauka ya fi yawa ne na ce masa ni ba ɗan fim ba ne ko mawaƙi, ni ɗan jarida ne.
Na kawo kaɗan cikin waɗannan misalan ne don na tabbatar da cewa da gaske ana iya damfarar Ummi, saboda ta na da saurin yarda. Amma ko ni ban yarda cewa an damfare ta miliyan 450 ba!
Akwai wasu ‘yan jarida da ta amince musu ta ba su kuɗi (ta faɗa min nawa ta ba su) amma su ka wallafa wasu hotunan ta marasa kyawun gani da Timaya da Jonah de Monarch.
Saboda gajiya da shiga rigima ne dole ƙarshe na daina shiga waɗannan rigingimun, mu ka kuma daina magana da Ummi. Kuma ma dai, lokaci ya fara yi min ƙaranci; ga aiki, ga karatu duk a lokaci guda. Kafin mu daina, duk wata mu’amala da ta shafi harkar jarida da Ummi na ba ta wasu shawarwari kan yadda za ta kauce wa ci gaba da faɗawa irin waɗannan rigingimun, musamman ma lokacin da labarin ‘soyayya da IBB’ ya yi ta yawo.
Mutane da dama sun tambaye ni kan me ke faruwa har Ummi ke son kashe kan ta. Na yi ƙoƙarin bada amsa da “Ni ma ban sani ba, rabo na da yin waya da Ummi tun 2012”. Don haka ne ma na yi ƙoƙarin neman ta don jin dalilin da ya sa ta ke son kashe kan ta, wannan kafin labarin damfara ya fito kenan.
Zai yiwu ba gaskiya ba ne an damfare ta naira miliyan 450, amma a yanzu ita ‘patient’ ce ta ‘depression’. Mai jinya ce da ta ke buƙatar taimakon duk wanda zai iya taimaka mata har ta dawo hayyacin ta. Kamar dai yadda ‘yan Nijeriya da yawa ke fama da jinyar damuwar da ba su iya sanar da kowa.
Mutane sun faɗi ra’ayoyin su; masu kyau da munana. Gaba ɗaya mun manta cewa idan ƙarya Ummi ta yi kan damfarar da ta yi iƙirari, kenan ana da cikakkiyar hujjar da ya kamata a taimaka mata ta ga likita ko ƙwararre kan harkar da ta shafi ƙwaƙwalwa.
‘Depression’ gaskiya ne, musamman ga mutumin da ya saba da kuɗi kuma ya zo bai da su. Allah ya sa mu gama da duniya lafiya!
* Sulaiman Bala Idris ɗan jarida ne mazaunin Abuja. Shi ne tsohon Editan mujallar Matasa da jaridar A Yau
To Allah ya sauke Allah ya tsare dukkanin musulmi daga ibtila’i amin
Allah ya kyauta
To allah ya kyauta