DARAKTA a Kannywood, Malam Al-Amin Ciroma, zai angwance a farkon watan gobe.
Daraktan, wanda kuma fitaccen jarumi ne, zai yi wannan auren ne shekaru biyu bayan mutuwar auren sa da jaruma Wasila Isma’il.
Za a ɗaura auren sa da ‘yar’uwar sa, wata tsaleliyar Bafillatana, budurwa mai suna Malama Sharifatu Aliyu Buji, da misalin ƙarfe 2 a ranar Juma’a, 2 ga Mayu, 2025 a Masallacin Juma’a na fadar Arɗon Mayo Faram da ke Ƙaramar Hukumar Mayo Belwa, Jihar Adamawa.
Mayo Faram nan ne garin su Ciroma, wato ya koma gida ya darje kenan.
A katin gayyatar da angon ya tura wa mujallar Fim a yau, Al-Amin, wanda shi ne Talban Mayo Faram, an nuna cewa iyalan ma’auratan, wato marigayi Alhaji Oumar Ciroma da na Aliyu Usman Buji (Mai Anguwa), su ne suke gayyatar.

Idan kun tuna, a ranar 4 ga Yuli, 2023 ne mujallar Fim ta fara ba da labarin mutuwar auren Wasila da Ciroma.
A lokacin, auren ya riga ya mutu da kimanin watanni biyu.
Auren ya mutu bayan shekara 21.
Sun haifi ‘ya’ya biyar a tsakanin su – mata uku, maza biyu – amma ɗaya ya rasu. Yanzu suna da huɗu.
Mutane sun yi baƙin cikin mutuwar auren, kuma da dama sun yi ƙoƙarin sasanta su amma abin ya ci tura.
Tuni dai kowa ya kama gaban sa, domin dai Ciroma ya ci gaba da hidindimun sa yayin da ita kuma Wasila ta koma Kannywood a matsayin jaruma.