WATA kotun majistare a Legas a yau ta yanke wa fitacciyar jarumar Nollywood ɗin nan Funke Akindele hukunci saboda ta karya dokar zaman gida da kaɗaicewa sakamakon annobar koronabairus (coronavirus).
Tare da mijin jarumar, mawaƙi Abdulrasheed Bello, wanda ake wa laƙabi da JJC Skillz, aka yanke mata hukuncin.
An yanke hukuncin za su yi wa al’umma aiki na tsawon kwana 14.
Ana so a kullum za su yi aikin awa uku ban da Asabar da Lahadi.
Haka kuma kowannen su zai ziyarci wuraren taruwar jama’a har guda goma inda za su wayar da kan mutane game da illar bijire wa dokar da ta hana mutane watayawa a gari saboda cutar koronabairus.
Bugu da ƙari, kotun ta ce tilas ne kowannen su ya biya tarar N100,000.
Ita dai Funke Akindele, wadda ake wa laƙabi da Jenifa saboda shirin ta na diramar talbijin mai suna ‘Jenifa’s Diary’, ‘yan sanda sun kama ta ne saboda ta shirya wata liyafa a gidan su, wanda hakan ya saɓa wa dokar gwamnatin Jihar Legas.
Funke ta shirya wa mijin ta liyafar musamman ne a shekaranjiya Asabar domin ta karrama shi.
Kimanin mutum 20 su ka halarci dinar, ciki har da fitaccen mawaƙin nan mai suna Azeez Fashola, wanda aka fi sani da ‘Naira Marley’.
Dubban mutane a soshiyal midiya ne su ka yi kira ga jami’an tsaro da su kama Funke Akindele.
‘Yan sanda cike da motoci uku sun dira a rukunin gidaje na ‘Amen Estate’ da ke babbar hanyar Lekki-Epe inda su ka kama Funke da mijin nata.

Wata majiya ta faɗa wa mujallar Fim cewa su ma sauran mahalartan liyafar ‘yan sanda na neman su ruwa a jallo.
Tun kafin a je kotu, Jami’in Yaɗa Labarai na rundunar ‘yan sanda ta jihar, Bala Elkana, ya tabbatar wa da manema labarai cewa ‘yan sanda sun kama Funke sun tsare ta a ofishin C.I.D. na jihar da ke Panti, Yaba.
Wani abin mamaki shi ne ita dai Funke Akindele jakadiyar musamman ce ta Cibiyar Hana Yaɗuwar Cututtuka ta Nijeriya, wato ‘Nigerian Centre for Disease Control’ (NCDC) da kuma kamfanin Dettol.
An gan ta a cikin wasu tallace-tallace a ‘yan kwanakin nan ta na yekuwa ga ‘yan Nijeriya su kiyaye kan su daga kamuwa da koronabairus ta hanyar daina cuɗanya da juna da kuma kula da lafiyar su.
Daga baya, ta bada haƙuri ga jama’a kan lamarin, ta na faɗin cewa yawancin waɗanda su ka halarci liyafar abokan ta ne da su ka kasa tafiya gida saboda dokar hana yawo saboda koronabairus.
Dokar hana yaɗuwar cututtuka ta Jihar Legas ta shekarar 2020 (‘Lagos Infection Diseases Regulations 2020’) ta yi tanadin cewa duk wanda ya karya dokar ta hanyar tara jama’a, to za a iya kulle shi a kurkuku tsawon wata ɗaya ko a yi masa tarar N100,000 ko a haɗa masa duka biyun.
Mujallar Fim ta lura da cewa mutane da dama a soshiyal midiya sun yaba da cafke Funke Akindele da aka yi tare da hukunta ta.
Da yawa sun ce wannan ya nuna cewar ba ta fi ƙarfin doka ba, kuma hukuncin da aka zartar a kan ta babban darasi ne ga sauran jama’a.