AN yi kira ga masu sana’ar finafinan Hausa da su san abin da ya kamata su yi wajen kare mutuncin kan su da na sana’ar su ta yadda mutane za su riƙa kallon su da mutunci.
Wannan kiran ya fito ne daga bakin tsohon shugaban ƙungiyar ƙwararru ta masu shirya finafinan Hausa ta ƙasa, wato ‘Motion Picture Practitioners Association of Nigeria’ (MOPPAN), reshen Jihar Bauchi, Alhaji Umar Inuwa, a lokacin da ya ke tattaunawa da mujallar Fim.
Alhaji Umar, wanda tsohon Manajan Darakta ne na Hukumar Talbijin ta Jihar Bauchi, furodusa ne wanda ya shirya finafinai da dama.
A hirar, ya bayyana harkar fim da cewa sana’a ce wadda Allah ya yi wa albarka, amma sai ya zama mafi yawa daga cikin masu yin ta ba su san yadda ya kamata su gudanar da ita ba, don haka ne ta ke ta samun matsalolin da aka kasa magancewa.
Ya yi nuni da cewar harkar fim ta karɓu sosai a ƙasar Hausa har ma da duniya, domin akwai mutane da yawa da ba sa jin Hausa amma su na kallon fim ɗin Hausa, sai dai rashin inganci da shiriritar da ke cikin harkar sun yi matuƙar mayar da sana’ar baya.
Alhaji Umar ya ci gaba da cewa: “Duk wata harka sai an koye ta, amma a yau rana tsaka sai ka ga mutum ya zo wai shi ma ɗan fim ne; sai mace ta zo kawai ita ma ‘yar fim ce, a saka ta; idan mutum ya na da kuɗi sai kawai ya zo ya yi fim.
“Kowa zuwa ya ke yi saboda an bar ƙofar a buɗe, babu wani tsari da aka yi na shigowa da kuma yadda ya kamata idan mutum ya shigo ya gudanar da sana’ar cikin tsari.”
Furodusan ya ci gaba da cewa, “Ni a matsayi na na wanda ya san harkar fim tsawon lokaci, na shigo harkar finafinan Hausa da kishin ciyar da al’umma gaba, amma a yadda na ga su na gudanar da harkar akwai matsaloli masu tarin yawa, domin na fahimce su mutane ne da duk yadda ka kai ga ilimi a kan harkar fim to sai sun nuna maka cewar kai ba ka san harkar ba.
“A ganin su, su kaɗai ne su ka iya, don haka duk ilimin ka sai dai ka bi su yadda su ke yi, ko da kuwa ba daidai ba ne.
“Sannan mutane ne da son kan su ya yi yawa, domin haka idan ka zo za ka yi harka da su, sai dai ka yi taka-tsantsan, wani lokacin ma sai dai ka kawar da kai dangane da son zuciyar su.
“Don haka wasu daga cikin su idan ka yi harka da su da wuya ku gama lafiya ba su ha’ince ka ba.
“Wannan ya sa mutane masu mutunci su ke gudun harkar, saboda halayyar ‘yan fim ɗin.
“A yanzu za ka ga mata su na shigowa fim, amma buƙatar su ba ta fim ba ce ko faɗakarwa, sai don biyan wata buƙata tasu ta daban kawai.
“Don haka ya zama wajibi a gare su, musamman masu son cigaban harkar, da su da su tashi tsaye don ganin an inganta harkar fim tare da ciyar da harkar fim gaba, domin lokaci ya yi da harkar fim za ta tashi daga wasa ta koma sana’a kamar yadda ake yin ta a duniya.”