* So da ƙauna ya haifar da wannan aiki, inji Ala
JAGORAN marubuta littafi mai suna ‘Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (Ala)’, Farfesa Salisu Ahmad Yakasai, ya bayyana cewa sun yi littafin ne don taskace basirar mawaƙin tun ya na raye, ba sai bayan babu shi a zo ana ta kame-kame ba.
Yakasai ya faɗi haka ne a hirar da ya yi da mujallar Fim a wajen taron ƙaddamar da littafin mai shafi 650 a jiya Asabar, 22 ga Mayu, 2021 a ɗakin taro na ‘Musa Abdullahi Auditorium’ da ke cikin Jami’ar Bayero, Kano.
Littafin ya ƙunshi kalmomin waƙoƙin wasu zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙin Aminudeen Abubakar Ladan (Alan Waƙa) waɗanda ya rera.
Manazarta biyu, Farfesa Salisu Ahmad Yakasai na Sashen Nazarin Harsunan Nujeriya da ke Jami’ar Tarayya, Sakkwato, da Dakta Abu-Ubaida Sani na Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya da ke Jami’ar Tarayya, Gusau, su ne su ka rubuto waƙoƙin daga cikin fayafayen su.
Taron ya samu halartar wasu daga cikin ‘yan’uwan Ala, wato mawaƙa da marubuta da ‘yan fim, da kuma sarakuna, manyan jami’an gwamnati, ‘yan siyasa, jami’an tsaro da ƙungiyoyin sa kai da ɗalibai, da sauran al’ummar gari maza da mata.
A yayin da ya ke yi wa mujallar Fim ƙarin haske kan dalilan da su ka sanya su rubuta wannan littafi, Farfesa Yakasai, wanda ya jagoranci aikin, ya bayyana cewa sun ga dacewar ɗaukar mawaƙin a matsayin wanda za su rubuta diwanin waƙoƙin sa tun ya na raye, ga shi kuma da dama daga cikin jami’o’i a ƙasar nan su na sanya ɗalibai yin nazari a kan waƙoƙin domin su na tafiya bisa al’ada da kuma bada gudunmawa ga adabi a ɓangaren harshe.
Yakasai ya ƙara da cewa wannan aiki da su ka yi somin taɓi ne, domin kuwa so su ke a canza akalar rubuta waƙoƙin mawaƙa, a yi tun su na raye, ba wai sai sun mutu ba wani abin ya zo ya gagari manazarci samu.
Ya ce idan mawaƙa su na raye, manazarta za su yi iya yin su don fito wa da ɗalibai masu nazari hanya sassauƙa don fahimtar waƙoƙin.
Shehin malamin ya ce, “Kamar yadda mu ka sani, a ƙasar Hausa Allah ya albarkace mu da mutane masu fasaha ƙwarai da gaske, fasahar nan ta fannoni da yawa. Harshe da adabi da al’ada da kuma zamani duk tafiya su ke ba tare da an adana wasu ba.
“Kuma mun lura ana yin ayyuka da yawa, (amma) daga baya su na ɓacewa. To sai a wannan lokacin da ake so a gabatar da sababbi amma na bayan da aka yi, su kan su na bayan ba su san su ba, sun manta su. Hakan ya sa na lura abin da ya kamata a yi shi ne a tattara su wuri guda a riƙa adanawa saboda gaba.

“Wannan gaɓa ta ƙunshi abubuwa da yawa. Akwai nazarce-nazarce da bincike-bincike wanda masu nazari kamar ɗalibai da malamai za su rinƙa gudanarwa.
“Akwai mutane ɗaiɗaiku da ƙungiyoyi waɗanda su ke son nishaɗi, su na karanta irin waɗannan waƙoƙi. Akwai sarakuna da sauran malamai.
“Babu wani ɓangare na rayuwa, na zamantakewar al’umma, wanda waɗannan ayyuka ba su taɓo ba. Saboda haka sai na ga ya kamata a tattara waɗannan ayyuka a dinga adana su yadda nan gaba za a yi maganin salwantar su, ba za su ɓace ba.
“Wannan diwani na waƙokin Ala ya ƙunshi ɓangarori da yawa, inda a ɓangare na farko ya ƙunshi rayuwar shi kan sa Ala ɗin, kama daga yadda ya taso ya yi karatu da kuma irin yadda ya shiga duniyar waƙa.
“Kuma mun duba waƙoƙin sa da yawa waɗanda ya yi, sai mu ka tsara su a cikin jigo-jigo; akwai jigon sarauta, akwai na faɗakarwa da ilimantarwa, zamantakewar aure, ta’aziyya, ɗaukaka, da kuma waƙokin addini.
“Bayan wannan ɓangare na rayuwar sa, sai kuma mu ka tattara irin waɗannan jigo yadda da zarar an zo nazari, za a yi cikin sauƙi ba tare da an ɓata lokaci da wahala ba.
“Kuma kowane jigo akwai bayanai da yawa a cikin sa. Abin da mu ka yi ma yanzu shi ne mun fara ne kawai. Kamar yadda na faɗa, waƙoƙin sa cigaba su ke yi domin kuwa waɗannan tsofaffin waƙoƙi ne waɗanda mu ka yo farautar su daga cikin waɗanda ya yi, wanda wasu daga cikin su ma ya manta su, ba zai iya tuna su ba, amma mu mun yi farautar su mun samo su mun yi nazari mun kuma tattara su wuri guda.
“Mu na sa ran kuma nan gaba za mu shiga Diwani kashi na 2 da na 3, gwargwadon yadda rayuwa ta bada dama. Matuƙar zai cigaba da yin waƙoƙin, matuƙar za mu tattara waƙoƙin, mu ga cewa mun adana su ta yadda nan gaba za a yi amfani da su.”
Da ya ke amsa tambaya kan cewa akwai mawaƙa da dama a ƙasar Hausa waɗanda ke raye amma ba su samu irin wannan tagomashin na rubuta waƙoƙin su wuri guda ba kamar yadda aka yi wa Alan Waƙa, sai Yakasai ya ce, “Gaskiya mu da mu ke nazarin waƙoƙin adabi a jami’a kusan kowane mawaƙi ya na da ƙima da matsayi a wajen mu. Irin wannan aiki kusan farawa ce. Mu na sa ran nan gaba sauran mawaƙa ma za su ba mu goyon baya mu yi ayyuka irin wannan, domin ayyuka irin wannan ayyuka ne da za su amfani jama’a baki ɗaya.
“Saboda haka, sauran mawaƙa mu na yi musu albishir (da cewa) mu na nan tafe; idan mun zo su ba mu goyon baya.

“Lokaci ne ya canza na zamani, wato irin wannan gaskiya ne cewa sai mawaƙi ya mutu ake rubuta waƙoƙin sa, wanda kuma wahala ake sha kafin a samu wasu jawabai daga makusantan su. Misali, yanzu ɗauki na Rambaɗa, irin wahalar da aka sha, wanda hoton sa ma ba a samu ba, sai da aka samu jikan sa sannan masu zanen hoto su ka tsofar da shi. To wannan ai matsala ce.
“Amma yanzu mawaƙi ya na raye duk hikima da basirar da Allah ya yi masa ya gaya mana, mu kuma mu gaya wa al’umma yadda za a gina abin.
“Da man waƙoƙin Aminuddeen Ala manufar sa gina al’umma, shi ya sa waɗannan jigon su ka shafi rayuwar jama’a. Saboda haka yanzu gara kowane mawaƙi ya na raye tun yanzu ya gaya mana abin da ya yi, don wasu waƙoƙin sai mun tambaye su me su ke nufi a nan sun gaya mana, wasu kuma mu mu ke ganowa mu ke nazari.”
A nasa ɓangaren, Aminu Ala, wanda shi ne Ɗanburan Sarkin Gobir kuma Sarkin Waƙar Dutse, ya bayyana wa mujallar Fim jin daɗin sa bisa ganin wannan rana mai ɗauke da tarihi a rayuwar sa.
Haka kuma ya bayyana wannan muhimmin aiki da manazartan su ka yi a matsayin wani abu da zai ƙara masa ƙwarin gwiwa wajen ƙara hazaƙa da yin waƙoƙin da za su ciyar da al’umma gaba.
Alan Waƙa ya ce, “Wannan littafi da aka yi, wanda Farfesa Salisu Ahmad Yakasai ya rubuta tare da shi da Abu-Ubaida, kamar wani tarihi ne wanda aka kafa shi, saboda yawancin mawaƙa ba a yin rubutu a kan sha’anin rayuwar su sai bayan sun faku.
“Idan aka kalli su Dakta Mamman Shata, Jankiɗi, su Narambaɗa, da su Mudi Sipikin, duk an yi rubutu a kan su amma bayan rasuwar su. Amma ni ga shi na samu sa’a da rayuwa ta da ƙarancin shekaru na aka rubuta wannan littafin mai suna ‘Diwani’. Kuma na 1 aka yi, ba a ma tsaya a nan ba, za a ci gaba.
“Mu na yi wa Allah godiya da wannan rana da ta zama mai ɗimbin tarihi a gare mu.
“Duk da halin da ake ciki a ƙasa, mun samu rasuwa ta manyan sojoji, amma duk da haka al’umma sun samu sun halarci wannan taro. Wasu ba su zo ba amma dai sun aiko da wakilci. Ga masoya duk a gurin.
“Ba abin da za mu ce da Allah da ya ba mu wannan baiwar sai godiya.”
Da yake wasu na ganin mahaifa ɗaya Alan Waƙa ya ke da jagoran marubutan, wato Farfesa Yakasai, shin ko akwai wata dangantaka da ta sa malamin ya ɗauki waƙoƙin Ala domin rubuta littafin?

A kan wannan tambayar, Ala ya faɗa wa mujallar Fim cewa, “Alaƙa ta da Farfesa soyayya ce kawai. Sannan alaƙa ta biyu kuma ita ce adabi, da waƙoƙin da na ke yi waɗanda su ka shafi al’umma wanda su na jan hankalin sa ƙwarai da gaske, daga bisani soyayyar ta bayu zuwa ga yadda ni kai na ina kallon jami’a ina yabon malaman jami’a, musamman na ɓangaren harshe da adabi a kan irin zaƙaƙurancin da su ke yi wajen fito da kyawawan ayyukan Hausa da kuma fito da harshen Hausa.
“Sannan wannan abu da aka yi, sara aka yi a kan gaɓa. Ba na mantawa, wata rana Farfesa Malumfashi ya kira ni ya ce, ‘Ka na da wani masoyi wanda ba ka san shi ba, idan ya na sauraron waƙoƙin ka ya na hawaye.’ To kun ga wani abu ne wanda ya ke daga zuciya, kuma soyayya don Allah.
“Ya ƙara da cewa, ‘Ni ina neman alfarma, ko da sau ɗaya ne wata rana ko a kan layi ne ka ambace shi a waƙar ka saboda zai ji matuƙar daɗi.’
“Saboda haka ka ga shi bai san bayanin da Farfesa Malumfashi ya yi mani ba, shi ya sa na zo na yi masa waƙa mai suna ‘Walwalar Harshe’ saboda kuma ya yi wani littafi ya na hannu na. Da na karanta littafin, sunan sa ‘Walwalar Harshe’, sai na yi masa waƙa a kan wannan ‘Walwalar Harshen’.
“Sannan kuma akwai kyaututtukan da ya ke min musamman na littattafan sa wanda idan ya yi sai an naɗe a takarda an kawo mani saboda na karanta ko zan ƙaru da wani abu a ciki. Kan haka ne kuma aka yi sa’a shi ya na ra’ayin waƙoƙi na.”
A ƙarshe, Ala ya yi godiya ga ɗimbin jama’ar da su ka halarci wannan taro, ya ce, “Ban da bakin da zan gode wa jama’ar da su ka halarci wannan taron tare da marubutan da su ka tsaya tsayin daka domin ganin hakan ya tabbata, kana su ka yi rubutu duk a kai na. Ina godiya. Musamman irin su Farfesa Isa Mukhtar, Farfesa Sa’idu Gusau, wanda ya zama jagoran wannan taro har ta kai ga wannan nasara.
“Ina godiya ga AGF, musamman ɗimbin ayyukan da su ke kan teburin sa amma ya bari ya zo da kan sa.
“Ina godiya ga Janar Tukur Yusuf Buratai; duk da halin da ƙasa ta ke ciki amma sai da ya turo da wakilci.
“Ga kuma shugaban ƙaddamarwa, Alhaji Aminu Ibrahim Dabo, da wakilan Masarautar Kano da kuma ta Dutse.
“Allah ya saka wa kowa da alkairi, da fatan komawa gida lafiya.”






allah ya taimaka