
MUHAMMAD Usman, wanda aka fi sani da Razaki, fitaccen jarumi ne wanda ya yi suna da shirin ‘Daɗin Kowa’. A yanzu haka likkafar sa ta ci gaba inda ya shiga cikin matasan furodusoshi masu tasowa a Kannywood. Tuni har ya saki fim ɗin sa mai suna ‘Baban Ladi’ a shafin sa na YouTube mai suna ‘Yar AroTV wanda ya zuwa yanzu dubunan mutane suka kalla.
Domin jin yadda jarumin ya rikiɗe zuwa furodusa, mujallar Fim ta tambayi Razaki Daɗin Kowa ko ya aka yi hakan ta kasance? Inda ya fara da cewa
Sai ya amsa da cewa, “To gaskiya wannan ba wani sabon abu ba ne idan ka dubi yadda harkar fim ta ke a duniya, kuma ita ma masana’antar mu ta Kannywood duk haka abin yake, saboda duk wani jarumi da ya shahara a Kannywood za ka ga ya taba yi ko kuma ya na yin furodusin.
“To ni ma idan ka kalli rayuwa ta ai ba da shirin ‘Daɗin Kowa’ na fara fim ba. Na fito a finafinai da dama.Domin dai ka ga ni haifaffen garin Kano ne kuma duk karatu na a cikin garin Kano na yi har na zo na shiga cikin harkar fim domin na bayar da tawa gudunmawar.
“Kuma na fara a matsayin jarumi wanda har na zo na ke ɗaukar nauyin shirin fim wanda zan ba mutane su yi ni kuma ina matsayin babban furodusa duk da yake dai finafinan da na yi ba su da yawa kuma haka a harkar aktin ma ban yi finafinai masu yawa ba.”
Muhammad ya fara fim ne da ‘Daɗin Kowa’, shi ya sa ma mutane su ka fi sanin sa da shi. Daga nan ya na fito a matsayin jarumi a fim ɗin ‘Kwana Bakwai’, sai kuma ya fito a fim ɗin ‘Ya Mace’ da ‘Tarkon Ƙauna’.
Waɗannan su ne finafinai guda huɗu da ya fito a cikin su a matsayin jarumi.
A cewar sa, a yanzu ya sauya salo ya zama furodusan sabon fim mai suna ‘Baban Ladi’.”
Dangane da yadda aka shirya fim ɗin, Muhammad Usman ya ce, “Wato shi yanayin aikin ma ya bambanta da sauran aikin da na saba yi ko na saba gani. Domin ƙwarewar da na yi a wajen koyo da kuma ganin yadda ake gudanar da aikin fim, shi ya sa da na tashi aikin fim ɗin ban yi masa shiri na wasa ba. Don haka aiki ne da ya samu kulawa sosai da kuma bin tsarin da ya kamata a gudanar da aikin.”
Da aka tambaye shi irin saƙon da fim ɗin ya ke ƙunshe da shi kuwa, cewa ya yi: “An zo da wani salo ne wanda ba irin yadda mutane su ka saba kallo ba. Saboda haka fim ɗin ‘Baban Ladi’ ba na shakkar zai ba masu kallo mamaki, don haka ma bayan mun sake shi a YouTube a ‘Yar Aro TV mu ke raba shi ga masu turawa a waya domin saƙon ya shiga duk inda ake buƙatar a kalla.”
Ya ɓuntuna mana irin labarin da ke ciki, da ya ce, “Labarin na wata yarinya ne da ta ke fafutikar neman ta yi ilimi wanda hakan ya sa ta ke fuskantar ƙalubale iri-iri, har ta kai ga wani ya shigo ya na ƙoƙarin ya taimake ta inda shi ma ya rinƙa samun kan sa cikin matsala.
“Don haka fim ɗin ya na ɗauke da barkwanci da kuma abubuwa da dama na faɗakarwa da nishaɗantarwa.”
Ya faɗi yadda ya haɗa jaruman shirin, ya ce, “Domin aikin ya tafi cikin ƙwarewa, sai mu ka haɗa tsofaffin jarumai da kuma sababbi, ta yadda su tsofaffi su nuna ƙwarewar su, su kuma sababbi a ba su damar da su ma nan gaba za su ƙware.”
Furodusan ya bayyana gamsuwa da yadda fim ɗin ke samun karɓuwa a wajen ‘yan kallo. Ya ce: “Alhamdu lillahi ko a yanzu kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu daga yadda mutane su ke ta shiga YouTube ɗin mu su na kallo. Kamar yadda na faɗa maka a baya, cikin lokaci kaɗan dubunan mutane ne su ka shiga su ka kalla. Kuma za mu ci gaba da saka shi a duk ranar Laraba.
“Don haka ni dai buri na da wannan fim ɗin ya zama zakaran gwajin dafi inda zai zama a duk masana’antar Kannywood babu kamar sa, yadda ko su ‘yan fim ɗin ma ya zama su na kafa misali da shi.
“Don haka ina kira ga abokan sana’a ta da mu dage mu yi aiki na gaskiya.”