TA tabbata a yau Juma’a, 24 ga Nuwamba, 2023, editan finafinai a Kannywood, Hafiz Hamis (SB), ya yi bankwana da kwanan shago.
An ɗaura auren sa da abar ƙaunar sa, Iƙilima Tasi’u, da misalin ƙarfe 02:30 na rana, bayan sallar Juma’a a Masallacin Juma’a da ke Kabala Costain, Kaduna, a bisa sadaki N150,000.
Wasu daga cikin waɗanda su ka halarci ɗaurin auren sun haɗa da Sulaiman Sir Zeesu, Jamil Nafseen, Haruna Gidaje, Adamu Muhammad Turaki (A. Wamba), Ibrahim Wassh, Isma’il Edita, Ɗanladiyo Mai Atamfa da Abdul S.D.
An yi walima bayan an ɗaura auren a harabar masallacin, daga nan kuma aka wuce zuwa wata walimar a Layin Samba, Malali, Kaduna.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa angon ƙane ne ga ‘yar jarida, ma’aikaciyar gidan Rediyon Jihar Kaduna (KSMC), Samira Hamisu Malali.
Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba, amin.

![]()







