FURODUSA kuma ɗan kasuwar finafinai a Kannywood, Alhaji Muhammad Rabi’u Koli, zai aurar da ‘yar sa ta farko.
Za a ɗaura auren Hafsat Muhammad Rabi’u (Ummi) da masoyin ta Suraj Tijjani Suraj (Khalifa), da misalin ƙarfe 1:00 na rana a ranar Juma’a, 26 ga Mayu, 2023, a masallacin Juma’a na Sarkin Musulmi Bello da ke Unguwar Sarki, Kaduna.

A saƙon gayyata da Koli ya ke aikawa, ya kan ce, “Tare da girmamawa ina gayyatar ku wurin ɗaurin auren babbar ‘ya ta Hafsat. In ba ku samu halarta ba, addu’ar ku ya wadatar. Na gode.”
Allah ya kai mu da rai da lafiya.