• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Rasuwar jarumi Kawu Mala gagarumin rashi ne, inji Dattawan Kannywood

by DAGA ABBA MUHAMMAD
May 15, 2023
in Labarai
0
Marigayi Malam Aminu Muhammad (Kawu Mala)

Marigayi Malam Aminu Muhammad (Kawu Mala)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ƘUNGIYAR Dattawan Kannywood (Kannywood Foundation) ta bayyana alhini kan rasuwar ɗan fim din nan da ya rasu kwanan nan, wato Malam Aminu Muhammad, wanda ake yi wa laƙabi da Mai Chemist ko AZ.

A saƙon ta’aziyya da ya wallafa a soshiyal midiya, kakakin ƙungiyar, Alhaji Muhammad Kabir Maikaba, ya bayyana cewa rasuwar abokin aikin nasu da “gagarumin rashi”.

Maikaba ya ce, “Da sahalewar shugabancin majalisar ƙoli ta dattawan masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood, wato Kannywood Foundation, mu ke ba da sanarwa da taya duk ‘yan’uwa da abokan arziƙi da dukkannin ‘yan wannan masana’anta ta Kannywood alhinin rasuwar ɗaya daga cikin mashahuran jarumai na wannan masana’anta, wato Dakta Aminu Mai Chemist, wanda aka fi sani da Kawu Mala.”

Ya ci gaba da cewa, “Wannan majalisa mai albarka na jajanta wa wannan masana’anta bisa wannan gagarumin rashi da ta yi.

“Mu na yi wa Malam Aminu addu’ar Allah subhanahu wa ta’ala ya jiƙan shi, ya gafarta masa dukkan kurakuran sa. 

“Mu na roƙon Allah ya faɗaɗa, kuma ya haskaka makwancin sa.

“Yadda Aminu ke da tausayi wajen gudanar da ayyukan sa, ya Allah ka dubi bayan sa, ya Allah ka tausaya wa abin da ya bari, kuma ka yi masu albarka. Allahu akbar!”

Idan kun tuna, mujallar Fim ta ba da labarin rasuwar Malam Aminu wanda ya koma ga Mahalicci a ranar Litinin, 8 ga Mayu, 2023 a asibitin Nassarawa da ke cikin birnin Kano.

Marigayin jarumi ne a cikin shirin ‘Daɗin Kowa’ na tashar Arewa 24, inda ya riƙa fitowa da sunan Kawu Mala.

Ya rasu sanadiyyar matsalar ciwon zuciyar sa da ya tashi, kamar yadda matar sa da babban ɗan sa su ka bayyana.

Ya rasu ya bar mata ɗaya, Hajiya Amina Yusuf (Umma), da ‘ya’ya 11, maza takwas da mata uku.

Mutuwar tasa ta girgiza mutane a ciki da wajen Kannywood saboda farin jinin sa.

Loading

Tags: Daɗin KowaDattawan KannywoodKabiru MaikabaKannywood FoundationKawu MalaMalam Aminu Muhammadrasuwata'aziyya
Previous Post

Furodusa a Kannywood, Rabi’u Koli zai aurar da ‘yar sa ta fari

Next Post

INEC ta rantsar da Isah matsayin kwamishina a karo na biyu

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Dakta Mahmuda Isah ya na rattaba hannu kan takardar rantsuwar da ya yi

INEC ta rantsar da Isah matsayin kwamishina a karo na biyu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!