BABBAN furodusa a Kannywood, Abdul Amart Mohammed, ya saya wa iyalan marigayi darakta Aminu S. Bono gida a gab da lokacin da kuɗin hayar su zai ƙare.
Wata majiya ta shaida wa mujallar Fim cewa farashin gidan ya tasar wa naira miliyan huɗu kuma an saye shi ne a unguwar Ɗandago.
Abdul Amart Mai Kwashewa shi ne Shugaban Abnur Entertainment, ɗaya daga cikin manyan kamfanonin shirya finafinai a Kano.
Bayanin sayen gidan ya fito ne daga bakin Shugaban Ƙungiyar Daraktocin Kannywood, Malam Aminu Saira, a lokacin da ya ke gabatar da jawabi a wajen taron addu’ar bakwai ga marigayi Aminu S. Bono da ‘yan fim su ka gudanar a Majalisar Matasa ta Tarauni da ke unguwar Gyaɗi-Gyaɗi a cikin garin Kano.
An yi taron ne a yau Litinin da yamma domin yin addu’ar bakwai ga Aminu wanda Allah ya yi wa rasuwa a makon jiya.

Tun da fari, bayan an buɗe taron da addu’a, sai Malam Aminu Saira ya yi jawabi a kan mutuwa inda ya yi nasiha a kan jin tsoron Allah.
Ya ce: “Ita mutuwa wa’azi ce a gare mu, don haka mu yawaita tuba a wajen Allah kuma mu rinƙa kyautata mu’amalar mu kamar yadda kowa ya yi shaidar Aminu S. Bono. Domin ko taron jana’izar sa ya tabbatar da kyakkyawar alaƙar sa da jama’a.
“To, shi a yanzu Allah ya yi masa rasuwa, sai dai mu bi shi da addu’a. Wannan shi ne zai tabbatar da soyayyar da mu ke yi masa, don haka mu na roƙon Allah ya jiƙan sa, ya kyautata makwancin sa, kuma ya albarkaci abin da ya bari.”
Shi ma darakta Falalu A. Ɗorayi, a tasa nasihar, cewa ya yi, “Abubuwan da su ka bayyana a soshiyal midiya bayan rasuwar Aminu S. Bono kowa ya san wanene shi. Domin abubuwa ne da su ke tabbatar da kyawawan ɗabi’un sa.”
Ya ci gaba da cewa, “Ya kamata mu shiga hankalin mu, mu ƙara sanin inda mu ka saka gaba, domin a lokacin da Aminu S. Bono ya rasu duniya ta yi caa a kan mu da jafa’i.

“Don haka sai mu san abin da za mu rinƙa ɗorawa a soshiyal midiya. Mu zama jakadu ga al’umma. Mu kiyaye mutuncin mu da na ‘ya’yan mu domin ba mu san lokacin da za mu mutu ba.
“Domin a ranar ya je wajen Dakta Sarari sun gama magana a kan fim ɗin da zai yi da kuma irin gudunmawar da zai bayar. Amma ya na zuwa gida ya kwanta sai aka ji kawai ya mutu.
“Don haka ‘yan’uwa mu ji tsoron Allah a duk abin da za mu yi. Allah ya jiƙan sa, ya kyautata makwancin sa.”
Shi kuma darakta Ahmad S. Alkanawy ya yi nasiha ne a kan ‘yan fim su riƙa sanin mutanen da za su yi tarayya da su da kuma wajen da za su je don gudanar da mu’amalar su.
“Sannan kowa ya sani duk abin da mutum ya aikata idan ya mutu za a tambaye shi, don haka kowa ya ji tsoron Allah,” inji shi.

Shi ma Shugaban Zauren Majalisar Dattawan Kannywood, Malam Shu’aibu Yawale, ya ce: “Ya kamata mutuwa ta zama darasi a gare mu, don ba ka san lokacin da za ka mutu ba.
“Mu Allah ya yi mu a cikin harkar fim. Kuma kamar yadda kowa a cikin harkar sa a nan ya ke samun Wutar sa da kuma Aljannar sa, mu ma haka tamu sana’ar mu ta ke, don haka mu ji tsoron Allah.”
Ya ƙara da cewa, “A yanzu babbar matsalar mu ita ce kowa daga ya ga dama a yau sai ya zama ɗan fim. To wannan matsala ce babba wadda dole sai mun yi wa abin tsari don mu ceto masana’antar.”
An dai jawabai da dama. Bayan an gama, sai Aminu Saira ya bada sanarwar samar da wata gidauniya da su ka yi wadda za ta riƙa tallafa wa iyalan waɗanda su ka rasu.
A cikin jawabin nasa a kan hakan, ya ce, “Bayan rasuwar Aminu S. Bono abin da ya bayyana shi ne ya ke riƙe da iyayen sa baya ga hidimar iyalan sa. Sannan mun gano a gidan haya ya ke rayuwa wanda mu ka tabbatar da wata mai zuwa ma kuɗin hayar sa zai ƙare.
“Hakan ta sa mu ka yi tunanin yadda za mu tallafa wa iyayen sa don rage musu raɗaɗi da kuma ƙoƙarin samar wa da iyalan sa gida wanda kuma a yanzu alhamdu lillah wani daga cikin mu, wato Abdul Amart, ya saya wa iyalan sa gida.
“Don haka abin da ya shafi kula da iyalan sa ne a yanzu za mu sa gaba. Kuma a wannan lokacin mun buɗe karɓar gudunmawar ga duk wanda ya ke da niyyar bayar da tasa.”
An tara kuɗi masu waya a wurin taron kuma za a ci gaba da karɓa ana rubutawa.

A wata sabuwa, shahararren mawaƙin siyasa, Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara), ya bayyana cewa ya ɗauki nauyin karatun ‘ya’yan Aminu S. Bono.
Ya bayyana haka ne a lokacin da ya je ta’aziyya da addu’ar kwana bakwai ga iyalan mamacin a yau Litinin.
Rarara da tawagar sa sun je gidan iyayen marigayin don yi masu ta’aziyya, inda su ka yi addu’o’in neman rahama ga marigayin.
Bayan sun fito daga nan kuma su ka wuce gidan sa inda iyalin sa su ke, inda su ka yi masu ta’aziyya da addu’o’i ga mamacin.
An gudanar da saukar karatun Alƙur’ani na neman rahamar Allah ga marigayi Aminu.
Rarara ma ba a bar shi a baya ba, domin ya shiga cikin masu sauke Alkur’ani, shi ma aka ba shi wani ɓangare ya karanta.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa Aminu S. Bono ya na ɗaya daga cikin daraktocin da Rarara ke aiki da su, musamman idan zai yi aikin bidiyon waƙoƙin sa ko fim.
A shekarun baya, marigayin ya na daga cikin mutanen da Rarara ya ba kyautar mota.