FURODUSA a Kannywood, Hajiya Fatima Ibrahim Ahmad (Lamaj), ta yi wa Yusuf Nagazara, wanda aka fi sani da Yusuf Costume, da amaryar sa Maryam fatan zaman lafiya mai ɗorewa.
Lamaj, wadda ita ce tsohuwar shugabar ƙungiyar MOPPAN reshen Jihar Kaduna, ta yi wannan addu’ar ne bayan an ɗaura auren Yusuf, wanda yaron kamfanin ta ne.
Da ta ke bayyana wa mujallar Fim irin farin cikin da ta yi na ganin auren Yusuf, babbar furodusar ta ce, “A matsayi na na uwa ga ango da amaryar sa Maryam, ina yi masu fatan alkhairi da zaman lafiya mai ɗorewa.”

Lamaj ta ci gaba da cewa, “Yusuf yaron kamfani na ne, a nan ya fara aikin ‘costume’. Ya na da hankali da sanin ya-kamata.
“A yanzu ya na kasuwanci a Abuja, amma duk da haka bai bar harkar industiri ba, domin har yanzu in zan yi aiki ya na aiko min da ‘costume’. Gaskiya Yusuf bai manta da mafari ba.
“Ina fatan Allah ya yi masu albarka, ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba. Na yi matuƙar farin ciki da wannan aure.”
An ɗaura auren Yusuf da Maryam ne a ranar Asabar, 8 ga Oktoba, 2022, da misalin ƙarfe 2:00 na rana, a garin Maƙarfi, Jihar Kaduna, a kan sadaki N200,000.

An yi dina a daren ranar ɗaurin auren a otal ɗin ‘Silver Sand’ da ke Titin Katuru, Unguwar Sarki, Kaduna.
Kafin ranar ɗaurin auren, an yi bikin Kamu a Orage Hotel da ke Hayin Banki, Kaduna.
Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba, amin.


Comments 2