• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 30, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gargaɗin Amurka kan Nijeriya na tada hankulan jama’a, ya illata tattalin arzikin ta – Minista

by DAGA WAKILIN MU
November 7, 2023
in Nijeriya
0
Alhaji Mohammed Idris ya na gabatar da jawabi ga manyan editoci, yayin da jami'an sa su ka sa ido

Alhaji Mohammed Idris ya na gabatar da jawabi ga manyan editoci, yayin da jami'an sa su ka sa ido

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAN Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce gargaɗin da Amurka ta fitar kan Nijeriya ya na kawo babban cikas ga tattalin arzikin ƙasar.

Idris ya bayyana haka a lokacin da ya ke ganawa da editocin jaridu a ranar Litinin, a Abuja.

A ranar Juma’a ce, 3 ga Nuwamba, Ofishin Jakadancin Amurka da ke Abuja ya fitar da sanarwar “wata babbar barazana” ga manyan otal-otal da ke faɗin Nijeriya, amma ya ce jami’an tsaron Nijeriya na aiki tuƙuru domin daƙile barazanar.

Idris ya ce, “Abu mafi muhimmanci shi ne kada a yi wa barazana fassarar nuna cewa ta mamaye dukkan faɗin ƙasar nan, domin yin hakan ba wani alheri ba ne.”

Wasu daga cikin manema labaran da su ka halarci taron

Ya ƙara da cewa a kullum gwamnati ta na ɗaukar tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a da sauran dukkan maziyarta cikin ƙasar nan da muhimmanci.

Ya ce: “Mun fahimci damuwar da Amurka ke nunawa ko kuma ta nuna a cikin gargaɗin da ta fitar. Amma kuma mun haƙƙaƙe da cewa bai kamata kuma bai dace a nuna wannan barazanar ta shafi dukkan otal-otal ɗin faɗin ƙasar nan ba.

“Abin da mu ka lura shi ne yawancin wannan gargaɗin ba ya haifar da wani alheri, sai dai kawar ya firgita mutane su tashi hankulan su. Sai kuma kawo illa ga tattalin arzikin ƙasa da gargaɗin ke yi. Sannan kuma ya kan zama wata hanyar yi wa ƙoƙarin da gwamnati ke yi na samun masu zuba jari a cikin ƙasa zagon ƙasa.

“A kullum mu na bayar da fifiko wajen kare rayuka da lafiyar duk wasu baƙin da su ka kawo ziyara cikin ƙasar nan.”

Minista ya ci gaba da bayyana irin nasarorin ga jami’an tsaro su ka samu wajen daƙile matsalar tsaro a wasu jihohin ƙasar nan daban-daban a ‘yan kwanakin nan.

Loading

Previous Post

Shugaban INEC ya gargaɗi ma’aikata su yi aiki da gaskiya a zaɓen gwamnonin Bayelsa, Imo da Kogi

Next Post

‘Yan Nijeriya za su fara bin diddigin ayyukan da Gwamnatin Tarayya ke aiwatarwa – Minista

Related Posts

Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta bada tabbacin akwai tsaro a Abuja duk da gargaɗin da Amurka ta ba matafiya

June 23, 2025
Kiran Gwamnatin Tarayya ga ‘yan jarida: Ku zama jigo wajen gina dimokiraɗiyyar Nijeriya
Nijeriya

Kiran Gwamnatin Tarayya ga ‘yan jarida: Ku zama jigo wajen gina dimokiraɗiyyar Nijeriya

June 21, 2025
Ministan Yaɗa Labarai ya yaba wa Hafsoshin Soji kan cigaban da aka samu a fannin tsaron ƙasa a shekaru biyu
Nijeriya

Ministan Yaɗa Labarai ya yaba wa Hafsoshin Soji kan cigaban da aka samu a fannin tsaron ƙasa a shekaru biyu

June 20, 2025
Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Next Post
Minista, Alhaji Mohammed Idris, na gabatar da gabatar da jawabi a taron

'Yan Nijeriya za su fara bin diddigin ayyukan da Gwamnatin Tarayya ke aiwatarwa - Minista

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!