Assalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.
A MADADIN ni kai na da dukkanin iyalai da ‘yan’uwa da kuma ɗaukacin masoya na ina miƙa saƙon godiya marar iyaka ga wannan ƙasaitacciyar Hukuma ta Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano da kuma gwamnatin Kano a bisa wannan gagarumar dama da aka ba mu, mu marubuta littattafan Hausa.
Haƙiƙa wannan babban yunƙuri da hukumar nan ta yi na shirya mana gasar rubutun gajerun labarai ƙarƙashin jagorancin babban Daraktan ta, mai girma Alhaji Dr Abba El-Mustapha, yunƙuri ne na a zo a gani kuma abin a yaba matuƙa.
Wannan babbar dama ce aka ba mu wacce za ta taimake mu gami da ƙara farfaɗo da darajar rubutu da marubuta a idon duniya, kuma muna yabawa gami da jinjina da kuma godiya a madadin dukkanin marubutan Hausa.
Allah ya saka wa mai girma Alhaji Dr Abba El-Mustapha da alkhairi, ya kuma ƙara masa jajircewa da ƙwarin gwiwa da tsayawa a kan gaskiya kamar yadda kowa ya san shi a kan haka.
Ga kuma wani ƙarin tagomashin da aka yi mana albishir da shi, wato alƙawarin mayar mana da kowacce ranar 31 ga watan Disamba a matsayin Ranar Marubutan Jihar Kano da mai girma darakta ya yi mana. Muna godiya ga mai girma Gwamnan Kano, His Excellency Alhaji Abba Kabir Yusuf.

Haƙiƙa babu wata gwamnati da ta taɓa ba marubutan Hausa irin wannan damar ta kuma tafi da mu kafaɗa da kafaɗa cike da girmamawa da kuma mutuntawa a kaf Nijeriya sai a yau ƙarƙashin mulkin mai girma gwamna.
Allah ya ƙara masa lafiya da jajircewa da kuma gudanar da aiki tuƙuru kamar yadda muka shaide shi a kan hakan, musamman ma ayyukan jinƙai da na raya ƙasa.
Ina miƙa saƙon godiya ga dukkanin Ma’aikatan Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, musamman ma Director of Publications. Ina roƙon Allah ya ƙara ɗaukaka su baki ɗaya, ya sanya su fi yadda suke.
Ina godiya ga ɗaukacin marubutan Hausa baki ɗaya da suka kasance da mu a lokacin gudanar da wannan gagarumin biki na karrama mu tare da ba mu kyaututtuka. Ina miƙa saƙon godiya ta ga ‘yan’uwa na na jini da maƙota na da sauran abokan arziki da su ma suka kasance tare da mu a lokacin wannan gagarumin biki. Allah ya saka muku da mafificin alkhairi dukkanin ku, ya sanya kowa da kowa ya koma gida lafiya.
Na gode! Na gode!! Na gode!!!
Zubair M. Balannaji, Gwarzon Marubuci na ɗaya na gasar Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano 2024
