MALAM Umar Muhammad Sani Jigirya, wanda aka fi sani da Sallau a shirin diramar ‘Daɗin Kowa’, ya bayyana cewa masu shirya shirin sun shato labarin ta yadda ya fi ƙarfin duk yadda su ke tsammani, wanda hakan ya sa shi bai ga ranar gama shirin ba.
Ya ce: “Kusan gidaje sun yi yawa a ‘Daɗin Kowa’ kuma mutane sun yi yawa, don haka yaushe aka yi labarin wane da wane?”
Umar Jigirya dai ya na ɗaya daga cikin ‘yan wasan da aka fara shirin na gidan talabijin ɗin Arewa24 da su, kuma har zuwa zango na uku ana sa ran da shi za a ci gaba da tafiya, domin har ya rattaba hannu a yarjejeniyar wasan.
To sai dai wani lokaci a kan ɗan jingine shi, masu kallo su daina ganin sa, daga baya kuma sai a ƙara ganin sa ya dawo. Shin me ya sa haka?
A kan haka ne wakilin mujallar Fim ya nemi jin ta bakin jarumin dangane da irin rawar da ya ke takawa tun daga farkon shirin har ya zuwa yau.
Umar ya fara yi mana bayani da cewa: “Tun da farko an fara da ni ne tun daga ‘Daɗin Kowa’, aka zo ‘Sabon Salo’, yanzu kuma aka shiga ‘Wasa Farin Girki’.
“A yanzu matsayin da na ke ciki a ‘Wasa Farin Girki’ shi ne an kira ni na sanya hannu a kan aikin. Ka ga wannan ya tabbatar da ina ciki kenan.”
Ta ɓangaren gwagwarmaya ko ta yaya ya fara? Umar ya amsa: “To gwagwarmaya dai ga duk wanda ya ke kallon mu ya san ta inda aka faro, domin an fara ne tun daga babu Sallau har aka zo aka samar da shi, har aka zo aka yi tunanin a ajiye Sallau, har aka zo aka dawo da Sallau, kuma har aka yi tunanin bayan an dawo da shi ɗin a ƙara ajiye shi, sannan aka ƙara yin tunanin a ƙara ɗorawa.
“To amma dai ni irin kallon da na ke yi wa lamarin, ba shi mutane su ke yi masa ba, domin ni a yadda na ke kallon al’amarin, wani abu ne da idan ka kula, sun shato ne abin ya fi ƙarfin yadda su ke tsammani.
“Kusan gidaje sun yi yawa a ‘Daɗin Kowa’ kuma mutane sun yi yawa, don haka yaushe aka yi labarin wane da wane?
“To ba a ɗauko abin yadda zai iya ƙarewa ba, kuma ba a ɗauko abin yadda za a tsaya a yi ta labarin wani ba. Wannan ta sa dole sai dai a bi abin a hankali.”
Dangane da yadda mu’amalar sa ta ke kasancewa a bayan fage kuwa a matsayin sa na Umar Muhammad Sani Jigirya, cewa ya yi, “To a bayan fage alhamdu lillahi, domin gwagwarmaya ta ta kasance ina yin ‘yan wasanni na, har ana gayyata ta wurare, domin na je na nishaɗantar da mutane, sannan kuma ina yin harkoki na na aikin gidan rediyo, har yanzu ina yi ban daina ba, kuma ina zuwa garuruwa don na gabatar da shirye-shirye na.
“Kuma akwai harkoki na na kasuwanci ina yi. Kuma har da harkar siyasa ina yi, duk da sauran abubuwa dai da na ke yi ina nan ina yi ban fasa ba, saboda na ɗebo harkokin nawa da yawa ni ma!”
Mujallar Fim ta yi masa wata tambaya kamar haka: “Amma har yanzu abin da mutane su ke kallo shi ne ka kasa bambanta kan ka da matsayin ka na Sallau a shirin ‘Daɗin Kowa’ da kuma sunan ka na Umar Sani Jigirya.”
Sai ya bada amsa da cewa, “To ba kasa cire kai na na yi ba, domin idan ka kula a yanzu mu na zaune da kai ne mu na yin shira a matsayi na na Umar Sani Jigirya. Ka ga in da Sallau ne ba za ka zauna da shi ba. Don haka ko a yanzu ma ai an samu bambanci.
“Kuma yadda na ke mu’amala ta ina yi ne a matsayin ni Umar Jigirya ne, don haka mu’amalar Sallau ta na faruwa ne a cikin shirin ‘Daɗin Kowa’, don haka mu’amalar Umar Sani Jigirya mai kyau ce.
“Kai da kan ka yanzu ka gani yadda jama’a su ke zuwa mu yi magana da su, wannan ya zo idan ya tafi ma wani ya zo. To haka mu’amala ta ta ke kasancewa a tsakanin jama’a mata da maza.
“Abin mamaki, za ka ga mutane daga wasu ƙasashe kamar Benin, Chadi, Togo da sauran ƙasashe duk ana kira na, kuma su na bibiya ta ta shafi na na Instagram da sauran shafukan da na ke da su.
“Kuma wani abin alfahari sai ka je waje ka ga wani babban mutum ya kira sunan ka wanda kai ba ka ma san shi ba. To ina alfahari da wannan irin baiwa da Allah ya yi mini.”
Daga ƙarshe, Umar ya yi fatan alheri ga masoyan sa saboda ƙaunar da su ke nuna masa.
![]()







