KAMAR yadda aka sani, masana’antar Kannywood ba ta rabuwa da sababbin fuska ta kowane ɓangare. Ahmad Muhammad Umar, wanda aka fi sani da Ahmad D. Prince, ya na daga cikin sababbin fuska a wannan lokacin duk da cewa ya ɗauki tsawon shekara huɗu a masana’antar.
D. Prince matashin jarumi ne, sannan kuma mawaƙi ne. Ahmad mutum ne mai ladabi da biyayya ga kowa a industiri, domin duk ƙanƙatar ka idan har ya san ka na gaba da shi a masana’antar, to zai girmama ka.
Jarumin, wanda Bafulatani ne, kyakkyawa ne, son kowa ƙin wanda ya rasa, ga shi da fara da kuma son jama’a.
Mujallar Fim ta tattauna da shi game da tarihin sa, da yadda aka yi ya fara fim da waƙa, alaƙar sa da mawaƙi Kawu Ɗan Sarki, da sauran su. Ga yadda hirar ta kasance:
FIM: Ka faɗa mana cikakken sunan ka da tarihin ka.
AHMAD: Suna na Ahmad Muhammad Umar, wanda aka fi sani da Ahmad D. Prince. Ni haifaffen Maiduguri ne. An haife ni wata unguwa mai suna Damboa Road.
Na yi firamare na a Ƙaramar Hukumar Mafa, na yi ƙaramar sakandare na a Balabirim, sannan na ƙarasa a ‘Success Secondary School’ da ke Bolori. Haka na yi difloma a kwamfuta a makarantar koyon kwamfuta da ke kusa da gidan waya na Maiduguri, sannan na yi satifiket na Arabic, na kuma difloma a Goni College of Islamic Studies. A halin yanzu kuma ina yin digiri na a ƙasar Uganda ta onlayin, ina gab da gamawa.
FIM: Wane yare ne kai?
AHMAD: Ni Bafulani ne.
FIM: Me ya kai ku Maiduguri, bayan ku Fulani ne?
AHMAD: Ka san Fulani ba su da wani wuri ɗaya da za a ce lallai-lallai ga inda su ke da zama. Shi Bafulatani duk inda zama ya kai shi, ya kan zama muhalli a wurin shi. Sai kuma mu asalin mu ‘yan Sudan ne, mahaifiyar mu ta shigo da mu Nijeriya, sannan mu ka zama ‘indigene by citizenship’ a Nijeriya.

FIM: Shekarun haihuwar ka nawa?
AHMAD: An haife ni a ranar 1 ga Janairu, 1998; kenan a yanzu ina da shekara 24 da wata 8 a duniya.
FIM: Me ya ba ka sha’awar shiga wannan harka?
AHMAD: Abin da ya ba ni sha’awa shi ne gaskiya ina so in kai wani mataki da zan faɗa duniya ta ji. Wannan shi ne babban dalilin da ya sa na shigo industiri. Saboda na fahimci cewar ba zan iya siyasa ba, ka ga in ba siyasa ba ɗaukaka a cikin su dole da ma ɗaya in ka na yi za ka faɗa a ji ka.
FIM: Wa ya kawo ka industiri?
AHMAD: Gaskiya ni babu wanda ya kawo ni. Hasali ma yadda na ke son harkar fim, idan aka ba da hutun makaranta daga Maiduguri zan ɗauko jaka ta sai in taho Kaduna. Ban san kowa a Kaduna ba, na dai san cewa duk garin da ka je akwai wurin da ake kira ‘lodging’. Na kan zo in kama, idan kuɗi na ya kusa ƙarewa sai in koma Maiduguri.
Idan na zo kafin in koma duk da ban san sunayen unguwanni ba, idan yamma ya yi an faɗa min cewa akwai wani wuri Gamji, ‘yan fim su na yawan zuwa aiki a wurin, sai in je ina kallon ‘yan fim su na shutin, in su ka tashi ni ma sai in koma masauki na. A haka dai har na gama difloma. A lokacin ban samun aiki ba, sai na ce gaskiya zan koma Kaduna in shiga harkar fim.
A wannan lokacin ina da wasu kuɗi a wuri na masu nauyi, kawai sai na shigo Kaduna na zo na kama otal, da kuɗin otal ɗi na ya kusa ƙarewa, da ma a wancan lokacin da na ke zuwa na koma akwai wani bawan Allah da mu ka taɓa haɗuwa da shi a Kawo, shi ma ya je kallon ‘yan fim, sai na ke hira da shi. Sunan sa Sama’ila. Kafinta ne. Sai ya ke ce min ai shi a nan Kaduna ya ke, yayar sa ma ta na wannan sana’ar. A haka dai ya ɗauke ni mu ka je gidan su har na zama abokin sa, ya kuma gabatar da ni a wurin yayar tashi, mu ka saba, har ya zamana ma da na koma makaranta, bayan na gama difloma na na dawo, sai na sauka a gidan su.
Bayan na sauka a gidan su, ta na ɗan ɗauka na mu na zuwa wurin ‘yan fim in su na aiki. Bai wuce sau biyu ma na taɓa bin ta ba, sai ta tafi Saudiyya. Still, sai ƙanen ta ɗin ya haɗa ni da wani a Kawo, gayen ya na harkar waƙa, ba shi da alaƙa da ‘yan fim, amma ai tunda ya na waƙa na san wata rana zai haɗa ni da ‘yan fim. A haka dai har na samu damar tsunduma a cikin harkar.
FIM: A wace shekara ka fara fim?
AHMAD: Na fara fim a 2018.
FIM: Wane fim ne ka fara fitowa a ciki?
AHMAD: Gaskiya ba zan iya tuna sunan sa ba. Amma dai fim ɗin da aka fara ɗora min kyamara, fim ɗin wani furodusa ne ana kiran sa I. Zango. Sai dai kuma akwai babban fim ɗin da na fito a ciki bayan wannan, sunan ‘Hafeez’.
FIM: Yanzu ka yi finafinai za su kai nawa?
AHMAD: Gaskiya ban san yawan su ba. Saboda finafinan da ni na ja ba su wuce uku ba, sauran kuma za a kira ka ne ka yi sin biyu, sin biyar, sin goma ka tafi, kuma yawanci gaskiya ba na riƙe sunayen su.
FIM: Za ka iya tuna sunayen waɗanda ka ja?
AHMAD: Akwai ‘Duhun Dare’, ‘Baƙin Birni’, sai kuma ‘Ruɗani’.
FIM: Bayan fim, ka na waƙa. Ya aka yi haka?
AHMAD: A wancan Lokacin da aka haɗa ni da wannan mawaƙin, Nuhu Ambasada, da aka haɗa ni da shi, mai in zauna haka kafin ya haɗa ni da ‘yan fim, sai na fara koyon waƙa, don lokacin har kwana ina yi a situdiyo, na dai zama kamar yaron situdiyo haka. So, kafin in zama ɗan fim sai na koyi waƙa, sai da na fara cin abinci da waƙa sannan na ci da fim. Ina waƙar ne, da damar fim ɗin ta zo sai na ce da ma ai abin da ya kawo ni kenan.
FIM: Waƙoƙin ka nawa yanzu?
AHMAD: Gaskiya ban sani ba.
FIM: Faɗa mana wasu daga ciki.
AHMAD: Akwai ‘Balaraba’ da kuma ‘Gaskiyar So’. Waɗannan ne fitattu.
FIM: Wanene ubangidan ka a yanzu?
AHMAD: Iyayen gida na su na da yawa, gaskiya, saboda duk wanda na samu ya na sama da ni a wannan harkar ina kiran shi da oga, kuma su na da yawa. Amma dai a Kaduna ina da iyayen gida, oga Wassh ubangida na ne, Abdullahi Abu Uku ubangida na ne, a Kano Abdulhadi Nasidi oga na ne, saboda shi ya fara haɗa ni da ‘yan fim ɗin Kano, amma a yanzu Sanusi Oscar 442 shi ne ubangida na, domin shi ne da kan shi ya yi ‘signining’ ɗi na a matsayin babban yaron shi.
FIM: Waɗanne irin ƙalubale ka fuskanta?
AHMAD: Lallai an samu ƙalubale. Amma ni ƙalubale a kan maƙiya ban ɗauke shi ƙalubale ba, wannan na ɗauke shi gishiri ne na rayuwa. Ƙalubalen da na fuskanta ƙalubale ne a kan mutanen da za su gan ka su nq son ka ta sanadiyyar harkar. Wannan shi ne ƙalubalen da na fuskanta.
FIM: Nasarori kuma fa?
AHMAD: Alhamdu lillah! Nasarori kam ana kan samu, musamman irin yadda masoya na ke kira na daga garuruwa su na yi min fatan alkhairi da kyaututtukan da ba za a rasa ba da kuma alfarma.
FIM: Menene burin ka a kan wannan sana’a?
AHMAD: Buri na in kai matakin da za a san ni a duniya, kuma a ce in na faɗa za a ji, da ma don shi na shigo.

FIM: Mecece alaƙar ka da mawaƙi Kawu Ɗan Sarki, domin ana cewa ku na kama da shi?
AHMAD: Alaƙa ta da shi, shi mawaƙi ne, ni ma mawaƙi ne, sannan shi Bafulatani ne, kuma ni ma Bafulatani ne. Bayan wannan ba ni da wata alaƙa da shi, kawai kama ce.
FIM: Duk lokacin da aka tunkare ka da maganar ya ka ke ji a ran ka?
AHMAD: Wani lokacin ba na jin daɗi, wani lokacin ina jin daɗi. Amma inda matsalar ta ke ya za a yi mutane cewa wanene Kawu Ɗan Sarki, don mu na da bambanci. Kuma wasu lokutan har a kan waƙoƙi na a kan rubuta Kawu Ɗan Sarki, a kira ni a waya a ce Kawu Ɗan Sarki na kira ka ne in gaishe ka. Irin waɗannan abubuwan sai in ji wani wani iri. Ta ya zan sa mutane su gane ni daban, shi daban?
FIM: Me za ka ce wa masoyan ka?
AHMAD: Shi masoyi babu abin da za ka ce masa sai godiya da fatan alkhairi, domin duk mutumin da ya nuna ka ya ce ina son ka a cikin mutanen da kun fi dubu, gaskiya babu abin da za ka ce masa sai dai godiya da fatan alkhairi. A taiƙaice, abin da zan ce masu shi ne su taya mu da addu’a in dai su na so mu kai matakin da su ke so su gan mu a kai.