• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Shekara 1 da shugabancin MOPPAN a Kano: Mun samar da cigaba – Gidan Dabino

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
April 20, 2023
in Tattaunawa
0
Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, MON

Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, MON

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A WATAN Afrilu na shekarar 2022 ne aka rantsar da shugabannin Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Ƙwararru ta Masu Shirya Fim ta Ƙasa (MOPPAN), reshen Jihar Kano. Don haka a wannan watan da mu ke ciki ne su ka cika shekara ɗaya cur da hawa mulki. Shin waɗanne irin nasarori ne ƙungiyar ta samu a cikin wannan shekara ɗaya da su ka yi? A kan haka ne mujallar Fim ta tattauna da Shugaban ƙungiyar, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, wanda ya feɗe mana biri har wutsiyar sa kan irin cigaban da su ka samar a jagorancin da su ka yi, kamar haka: 

“To, kowa dai ya san mun karɓi shugabanci, kuma an tabbatar akwai matsaloli masu yawa, kuma ko da mu ka kama shugabancin, da man ba mu faɗi wani alƙawari da mu ka ce za mu yi wa mutane ba, don kada ma a kama mu da laifin, amma dai duk da hakan mun yi wasu abubuwa daidai gwargwado, domin mataki na farko mun shiga kafafen yaɗa labarai mun sanar da jama’a irin manufofi da kuma tsari. Kuma bayan wannan mun yi ƙoƙarin kai ziyarce-ziyarce zuwa wasu muhimman wurare kamar Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano da kuma Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa, kuma shi kan sa shugaban wannan hukumar mai kula da Arewa-maso-yamma ya nuna cewa in ban da mu duk wasu shugabannin da aka yi na jiha, babu waɗanda su ka taɓa zuwa sai mu, kuma wannan ya nuna cewa za mu yi aiki tare da sauran su, kuma ta sanadiyyar wannan akwai wasu abubuwa da su ka taso wanda mu ka zaburar da hukumar, duk da yake aikin ta ne, amma kuma an yi mata wata matashiya a kai.

“Kuma bayan nan mun ziyarci Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, mu ka gabatar masa da wannan ƙungiyar, kuma har ya yi mana wasu alƙawura, wanda in dai aka cika to mu na ganin in-sha Allah za mu ce ba a taɓa samun wani tsarin shugabancin MOPPAN na Jihar Kano da ya samar da hakan ba. 

“Sannan mun ziyarci Sanata Barau Jibril, shi ma ya yi mana alƙawari kamar yadda gwamnan Kano ya yi mana. Duk wannan idan Allah ya sa su ka cika, za mu ga ko MOPPAN ta ƙasa ba ta samu haka ba. Mu dai fatan mu shi ne Allah ya sa waɗannan alƙawura su cika kafin a miƙa mulki ga sabuwar gwamnati mai zuwa.

“Sannan akwai tarurruka da mu ka yi da ƙungiyoyi masu zaman kan su; wasu na gida ne, wasu kuma na waje ne. Duk kuma mun tattauna abubuwa da za a kawo wa wannan masana’antar cigaba, duk da dai ba ma son mu faɗi abubuwan da aka yi saboda ka san harkar yanzu wani ma sai a shekara ana tattauna ya za a yi. Amma dai mun tabbatar akwai su ba ɗaya ba biyu ba. 

“Sannan akwai haɗin gwiwa da mu ka ƙulla za mu yi da wata ƙungiya ta masu shirya fim ta ƙasar Nijar, wanda a zuwan da na yi ƙasar Nijar mun haɗu da shugabancin su, mun tattauna da su a game da yadda za mu yi aiki tare, kuma za mu ƙulla yarjejeniyar aiki da su har ta tsawon shekaru goma. Don yanzu abin ya yi nisa har ma ita uwar ƙungiyar ta ƙasa ta shiga ciki, domin sun zo taron KILAF Awards da aka yi an ci gaba da tattaunawa. Don haka ka ga wannan wata nasara ce babba. Domin wannan yarjejeniya ta ƙunshi ya ya za mu tallata finafinan mu a wannan ƙasashe, kuma yaya za mu kare haƙƙin mallakar mutanen mu na wannan ƙasashe.

“Sannan akwai wani shiga tsakani da mu ka yi tsakanin wani mawaƙi da wasu jarumai wanda mu ka shiga mu ka fita, ba tare da mun bar maganar ta kai ga kotu ba, wanda inda ta kai ga hakan, to abin zai ɓaci ne sosai. Da man dai fatan mu a samu maslaha ne a tsakanin mutanen masana’antar. 

“Sannan kuma a kwanakin nan akwai wani taro da za a yi na gasar finafinai a Amerika wanda su ma sun aiko da takardar gayyata, su na neman haɗin kan mu, wanda ana nan ana tattaunawar yadda za mu shiga wannan yarjejeniya ta yin aiki tare da kuma yadda za a yi tafiyar don a gudanar da wannan taron. 

“Akwai abubuwa da dama da mu ka yi duk da ba wai a rubuce su ke ba, amma dai akwai su. Kamar duk wani abu da ya shafi farin ciki ko baƙin ciki mu kan yi ƙoƙarin mu je. 

“Kuma mun yi ƙoƙarin sasanta ƙungiyoyi da ba sa ga maciji da juna. Kamar Arewa da MOPPAN na Kano ba sa haɗuwa, amma a yanzu mun haɗa kan su. Wannan ni a tunani na wani cigaba ne, kuma za mu ci gaba da yin irin wannan, wanda hakan zai sa a ga masana’antar rigingimu sun ragu, saboda dukkan mu mun yarda masana’antar ce a gaban mu, don haka babu wani dalilin da zai sa mu zo mu na rigima da juna. 

“Don haka mu na yin iya ƙoƙarin mu don ganin an magance irin wannan matsalolin.

“Sannan sai abin da ya faru na kwanan nan na ibtila’in da ya faru na bayan zaɓe inda aka ƙone wasu wurare na abokan sana’ar mu. To sai mu ka samar da asusu don tallafa wa waɗanda abin ya ritsa da su. An ba su tallafi, kuma har yanzu ana ci gaba da neman tallafin. Don haka fatan mu wannan abu ya ɗore, ya zama idan wani abu ya samu mutane ya zama ana tallafa masu.

“Abu dai mai muhimmanci da za mu duba a matsayin mu na ‘yan fim shi ne mu san kan mu tare da tafiya da juna, don haka kada bambancin siyasa ya sa mu rinƙa cin dunduniyar juna, domin mu sani ita gwamnati za ta zo ta tafi ne, amma masana’antar dai ta na nan, don haka duk gwamnatin da ta zo za ta tafi ne ta bar ka da mutanen da ku ke sana’ar tare, to idan kun ɓata, su dai naka ne. 

“Yanzu mutanen da aka bai wa muƙamai su ka yi ta faɗa da mutane, gwamnatin yanzu ta ƙare za ta bar su da mutanen. Don haka mu fatan mu duk waɗanda Allah ya bai wa a cikin ‘yan fim, to su kula da mutanen su ‘yan Kannywood, kada bambancin siyasa ya sa su ga ba za su tafi da su ba. Ku ajiye siyasa, ku dawo kishin masana’antar, wanda hakan zai sa mu ci gaba. 

“Sannan ita kuma gwamnati mai zuwa, mu na ba ta shawara da ta duba mu duk ‘ya’yan ta ne, da wanda ya yi ta da wanda bai yi ta ba mu duka ‘yan Kano ne, ta kalle mu a matsayin ‘ya’yan ta kamar sauran jama’ar Jihar Kano.”

Loading

Tags: Ado Gidan DabinoBarau Jibrinhaɗin kaiHukumar Tace FinafinaiKannywoodKanoKILAF AwardsMOPPAN
Previous Post

Gwagwarmayar jarumi, mawaƙi Ahmad D. Prince a Kannywood

Next Post

Furodusa Abubakar Anka na so a farfaɗo da zumunci irin na da a tsakanin ‘yan Kannywood

Related Posts

Abin da ya sa zan shirya fim mai dogon zango – Kabiru Jammaje
Tattaunawa

Abin da ya sa zan shirya fim mai dogon zango – Kabiru Jammaje

December 14, 2025
Abin da ya sa na fi shaƙuwa da marigayiya Hauwa Lawan Maiturare a duk aminai na – Bilkisu Yusuf Ali
Tattaunawa

Abin da ya sa na fi shaƙuwa da marigayiya Hauwa Lawan Maiturare a duk aminai na – Bilkisu Yusuf Ali

October 13, 2025
Tarbiyya a Kannywood: Bai kamata laifin wasu ya rinƙa shafar wasu ba – Maryam CTV
Tattaunawa

Tarbiyya a Kannywood: Bai kamata laifin wasu ya rinƙa shafar wasu ba – Maryam CTV

September 29, 2025
Rashin tsayayyen ubangida ke hana wasu jarumai yin suna – Mama Siddiqa
Tattaunawa

Rashin tsayayyen ubangida ke hana wasu jarumai yin suna – Mama Siddiqa

September 14, 2025
Bayan damfarar kuɗin magani: Halin da jaruma Halisa Muhammad take ciki yanzu
Tattaunawa

Bayan damfarar kuɗin magani: Halin da jaruma Halisa Muhammad take ciki yanzu

September 1, 2025
MOPPAN: Za mu haɗa kai da ‘yan siyasa don kawo cigaban Kannywood – Shehu Hassan Kano
Tattaunawa

MOPPAN: Za mu haɗa kai da ‘yan siyasa don kawo cigaban Kannywood – Shehu Hassan Kano

June 30, 2025
Next Post
Alhaji Abubakar Musa Anka

Furodusa Abubakar Anka na so a farfaɗo da zumunci irin na da a tsakanin 'yan Kannywood

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!