• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, May 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gwamnati ta taskace ‘yan Nijeriya miliyan 30 a Rajistar Al’umma ta Ƙasa

by DAGA WAKILIN MU
March 19, 2021
in Nijeriya
0
Gwamnati ta taskace ‘yan Nijeriya miliyan 30 a Rajistar Al’umma ta Ƙasa
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

Gwamnatin Tarayya ta ce ta rubuta sunayen mutane da ba za su gaza miliyan 30 ba a Rajistar Al’umma ta Ƙasa (National Social Rajista, NSR) wadda za a yi amfani da ita a samu sauƙin ceto mutane miliyan 100 daga fatara a cikin shekaru 10 masu zuwa.


Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ita ce ta  bayyana haka a taron Sakatarorin Dindindin na jihohi kan shirin gwamnati na magance matsalolin yau da kullum (National Social Safety Nets Project, NASSP), wanda aka gudanar a ranar Alhamis a Abuja. 


Ministar ta samu wakilcin Sakataren Dindindin a ma’aikatar, Alhaji Bashir Alƙali, a taron.


Ta ce aikin da aka ɗora wa ma’aikatar na gudanar da shirin na NASSP tare da tallafin Bankin Duniya, ana yin shi ne domin a rage fatara da matsalolin yau da kullum a Nijeriya. 


Hajiya Sadiya ta ce an tsara shirin na NASSP ne domin ya kasance ya na da ofisoshi daga matakan tarayya zuwa jihohi, har zuwa yankunan ƙananan hukumomi, wato ya nuna matakai uku na gwamnati. 

Ta ce, “A yanzu, rajistar NSR ta na da sunayen ‘yan Nijeriya miliyan 30 daga jihohi 36 da Yankin Babban Birnin Tarayya daga gidajen matalauta guda miliyan bakwai. 


“Idan an ƙara lissafawa, za a ga cewa an samo waɗannan gidajen ne ya zuwa yanzu a yankunan ƙananan hukumomi 699, mazaɓu 8,161 da al’ummomi 81,776 a sassan ƙasar nan. 


“An samar da rajistar ta NSR ne ta hanyar yin amfani da tsarin fasalin ƙasa da al’umma, ta hanyar amfani da jama’ar unguwa, wanda ofishin kula da tsarin a jiha (SOCU) ya ke tattarawa a kowace jiha. 


“Ofishin raba kuɗi na ƙasa (National Cash Transfer Office, NCTO), a yanzu ya samu gidajen matalauta da ke amfana da shirin guda 1,632,535 a al’ummomi 45,744 daga unguwanni 5,483 na yankunan ƙananan hukumomi 557 da ke jihohi 35 da yankin Abuja.”


A cewar Sadiya, wannan na nuna cewa an samu mutum 8,100,682 a gidajen da ke cin moriyar shirin ta hanyar wakilin kowane gida wanda ake kira ‘Caregiver’ ko ‘Alternate Caregiver’ wanda ake biya sau biyu a wata (N10,000). 

Ta ƙara da cewa a yanzu, gidaje 991,965 ne su ke karɓar kuɗi a jihohi 28 da yankin Abuja.


Ta nanata cewa dukkan waɗannan abubuwa an yi su ne da nufin cika burin Shugaba Muhammadu Buhari na ceto ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga matsananciyar fatara. 


Ta ce, “Don haka, akwai buƙatar a daidaita ofisoshin shirin na SOCU da yadda ake gudanar da shi. Hakan na da matuƙar muhimmanci.”


A nasa jawabin, Babban Kodineta na NASSCO, Mista Apera Iorwa, ya ce manyan sakatorin shirin a jihohi su ne ma’aikata masu sanya ido kan shirin a jihohin su.


Ya ce, “Akwai buƙata a gare mu da mu riƙa haɗuwa a kai a kai domin mu yi nazarin al’amura da tsare-tsare tare da gano hanyar da za a samu cigaban shirin.”


Mista Iorwa ya ce tilas ne manyan sakatorin su tashi tsaye domin su tabbatar ba a kautar da manufar shirin a jihohin su ba.

Ya ce an tsara cewa jihohi za su mayar da kuɗin ga Bankin Duniya domin za a yi binciken kowane asusu kuma idan aka gano cewa kuɗi sun salwanta, to tilas ne a dawo da su a biya.


Haka shi ma Kodinetan Shirin Tiransifar Tsabar Kuɗi na Ƙasa (Conditional Cash Transfer), Ibrahim Jafar, ya ce tafiya tare da dukkan masu ruwa da tsaki  a shirin ya na da muhimmanci ga samun nasarar shirin. 


Ya ce akwai matuƙar muhimmanci a san bambancin da ke akwai tsakanin Rajistar Masu Cin Moriya ta Ƙasa (National Beneficiary Register) da Rajistar Al’umma ta Ƙasa (National Social Register).


Ya bayyana cewa akwai wasu matsaloli da ake samu wajen biyan kuɗi, to amma nan ba da daɗewa ba za a warware yawancin su.


Hukumar Dillancin Labarai ta Nijeriya (NAN) ta ruwaito cewa a yayin da wasu Sakatarorin Dindindin su ke gode wa Ma’aikatar Harkokin Jinƙai saboda wannan damar da aka samu, wasu kuwa sun koka kan babbar tazarar da aka samu tsakanin su da SOCU saboda NASSCO. 


A lokacin da ya ke magana kan hakan, Mista Iorwa ya nanata cewa daga yanzu za a fara magance matsalar, kuma duk wani bayani da aka miƙa wa SOCU to za a miƙa shi ga su Sakatarorin Dindindin ɗin.

Tags: Bashir AlkaliDisaster Management and Social DevelopmentMinistry of Humanitarian AffairsNational Safety Nets ProjectNational Social RegisterPoverty AlleviationSadiya Umar Farouq
Previous Post

Ba abin da marigayiya Rabi’atu S. Haruna ta fi so kamar yabon Annabi, inji mijin ta

Next Post

Cewar Okoye: Jam’iyyu 18 kaɗai INEC ta sani a yanzu

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Cewar Okoye: Jam’iyyu 18 kaɗai INEC ta sani a yanzu

Cewar Okoye: Jam'iyyu 18 kaɗai INEC ta sani a yanzu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!