HUKUMAR Tace Finafinai da Ɗabi’i ta Jihar Kano ta bada umarnin daina nuna finafinai masu dogon zango 22 saboda sun saɓa dokokin ta, ta ce a daina nuna su a intanet da talbijin.
A cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na hukumar, Malam Abdullahi Sulaiman, ya fitar bayan wani taron shawara da masu ruwa da tsaki a harkar, hukumar ta ce finafinan da abin ya shafa an sake su ne ba tare da an tace su a hukumar ba.
A sanarwar, an ruwaito cewa Babban Sakataren hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, shi ne ya bada umurnin dakatar da haska finafinan bayan bincike ya gano cewar ana nuna finafinan bayan an yi kunnen uwar shegu da dokokin hukumar.
Sanarwar ta ce: “Finafinan da aka dakatar sun gaza bin ƙa’idojin da aka kafa na a miƙa dukkan finafinai domin su samu amincewar hukuma kafin a shirya su, tallata su, nuna su a intanet, ko haska su a talbijin.”
Finafinan da aka dakatar ɗin sun ƙunshi wasu waɗanda ke matuƙar tashe a wajen masu kallon finafinan Hausa, ciki har da Ɗakin Amarya, Labari Na, Garwashi, Daɗin Kowa, Gidan Sarauta, da Manyan Mata.
Sauran su ne Mashahuri, Wasiyya, Tawakkaltu, Miji Na, Wani Zamani, Mallaka, Kuɗin Ruwa, Boka Ko Malam, Rana Dubu, Fatake, Jamilun Jiddan, Shahadar Nabila, Tabarma, Kishiya Ta, Rigar Aro, da Wa Ya San Gobe?
Hukumar ta ce: “Tilas ne dukkan furodusoshi da mamallakan waɗannan finafinan su daina haska su a talbijin ko nuna su a intanet ba tare da ɓata lokaci ba, kuma ana buƙatar su da su miƙa finafinan nasu ga hukumar domin tacewa tsakanin ranar Litinin, 19 ga Mayu, da ranar Lahadi, 25 ga Mayu, 2025.”
Ta ƙara da cewa duk wanda ya ƙi bin wannan umurnin a cikin lokacin da aka gindaya zai fuskanci matakan shari’a.
Haka kuma hukumar ta yi kira ga kafofin watsa labarai da hukumomin kula da finafinai da su goyi bayan ta don tabbatar da tasirin dokokin tace finafinan.
“Muna kira ga tashoshin talbijin da Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talbijin (NBC) da su mara wa ƙudirorin mu baya don tabbatar da an bi dokokin tace finafinai tare da haɓaka ƙwarewa a industirin Kannywood,” inji ta.
Hukumar ta jaddada sadaukarwar ta wajen tabbatar da ɗa’a da kare al’adu a cikin finafinan Hausa.