• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Kannywood ba ta taɓa ƙyama ta saboda addini na ko ƙabila ta ba — Prince Daniel

* An yi wa maganar da na yi a Amurka gurguwar fassara, inji shi

by ALI KANO
March 25, 2025
in Labarai
0
Kannywood ba ta taɓa ƙyama ta saboda addini na ko ƙabila ta ba — Prince Daniel

Darakta Prince Daniel (Aboki)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
Darakta Prince Daniel (Aboki)

DARAKTAN fim ɗin ‘Mai Martaba’, Prince Daniel, wanda ake wa lakabi da Aboki, ya bayyana cewa masana’antar Kannywood ba ta taɓa ƙin sa saboda addinin sa ko ƙabilar sa ba.

Aboki ya faɗi haka ne a cikin martanin da ya yi a yau kan labarin da jaridu suka buga, ciki har da mujallar Fim, inda aka ruwaito shi yana cewa Kannywood ta ƙi shi saboda addini, kuma Nollywood ta ƙi shi saboda shi ɗan Arewa ne.

A martanin, wanda ya turo wa da mujallar Fim, daraktan mai tashe ya ce: “An jawo hankali na ga wasu labarai da aka buga masu ɗauke da kanu da ke nuna cewa wai na ce Kannywood ta ƙi ni saboda addini na, kuma Nollywood ma haka saboda inda na fito.

“Da farko dai, ban yi hira da wata jarida ko mujalla ba a kan wannan batu.

“Sai dai, don in faɗi yadda abin yake, ina so in ce babu ko shakka a maganar da na yi a lokacin ɓangaren tambaya-da-amsa na taron Nollywood in Hollywood a Los Anjalis, Kalifoniya, USA, a farkon wannan watan inda aka tambaye ni matsalolin da muka fuskanta lokacin shirya ‘Mai Martaba’ da hanyar mu ta zuwa Oscars.
“Na faɗi matsaloli irin su rashin tsaro a lokacin ɗaukar fim ɗin da ɗimbin ma’aikata a Arewa-maso-yamma, da rashin kuɗi — da yake babu wanda zai iya yarda ya ba mu kuɗin sa, da ganin cewa ni ‘sabon’ darakta ne wanda ke aiki da taron sababbin ‘yan wasa—da yadda muka sha fama a hakan.
“A wani lokaci, sai ya kasance Kannywood a matsayin wani ɓangare na industirin fim suka riƙa kallon mu a matsayin ‘yan Nollywood, yayin da su kuma Nollywood suke mana kallon ‘yan Kannywood ne don kurum daga Arewa nake.

“Na yi wannan bayanin ne da kyakkyawar manufa a lokacin—domin in taimaka wa masu sauraren mu a zauren taron su fahimci yadda rabe-raben industirin yake a Nijeriya da yadda ya zame mana matsala a lokacin.

“Na yi amanna da cewa ba a fahimci wancan bayanin da na yi ba.
“Ina so a sani cewa Kannywood ba ta taɓa ƙi na saboda ƙabila ta ko addini na ba. A gaskiya , ita ce ma babbar ginshiƙi na a matsayi na na mashiryin fim. Hakan a bayyane yake ta yadda muka samu cikakken goyon baya daga masu kallon mu abin ƙaunar mu a lokacin da muka haska fim ɗin a sinima, kuma daga su masu taka rawa a masana’antar —daga tsofaffin har zuwa sababbin.

“Ina ba da tabbacin cewa ni mashiryin fim a Nijeriya ne, duk da yake daga Arewa nake. Ina zama ne a Kano, inda nake gudanar da sana’a ta, kuma ita ce cibiyar Kannywood. Na samu cikakken goyon baya a nan, ba tare da an nuna mani bambanci ko kaɗan ba.

“Zan ci gaba da sadaukar da kai na ga yin aiki tare da abokan aiki na da kuma iyayen Kannywood ɗin domin ɗaga darajar industirin tamu—wajen ba da namu labarin ga duniya da kuma samar da aikin yi ga matasan mu, mu bambanta da irin yadda ake ɓata sunan Arewa da cewa daba ce ta rikici da tashin-tashina da ta’addanci.”

Loading

Tags: KannywoodMai MartabamartaninollywoodPrince Daniel
Previous Post

Kannywood sun ƙi ni saboda ni Kirista ne, Nollywood kuma saboda ni ɗan Arewa ne – Darakta Prince Daniel Aboki

Next Post

Kalli inda Prince Daniel ya ce an ƙi shi a Kannywood saboda addini (bidiyo)

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Kannywood ba ta taɓa ƙyama ta saboda addini na ko ƙabila ta ba — Prince Daniel

Kalli inda Prince Daniel ya ce an ƙi shi a Kannywood saboda addini (bidiyo)

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!