Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa ta amince za ta ɗauki nauyin babban taron ƙasa da za a yi kan hanyoyin haɓaka masana’antar fasaha domin inganta tattalin arzikin Nijeriya.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Kwamared Ibrahim Waiya, shi ne ya faɗi haka a cikin wata takarda ga manema labarai da ya saki a yau, inda ya ce amincewar ta biyo bayan gamsuwar da ta yi da takardar neman buƙatar hakan wadda ƙungiyar Kannywood Foundation ta miƙa mata.
Gwamnatin ta yi la’akari da yadda ƙungiyar, a takardar tata, ta nuna muhimmiyar rawar da Kano ke takawa a matsayin ta na cibiyar ayyukan al’adu da fasaha a Arewacin Nijeriya.
Kwamishinan ya ce: “Babban taron zai kasance wani muhimmin waje inda za a baje kolin ɗimbin albarkatun da Kano take da su a industirin fasaha, wadda ta haɗa da harkar shirya finafinai, kayan kwalliya, sana’o’in hannu, kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙe, rubutu, da ƙirƙirar saƙonnin intanet.
“Ana sa ran babban taron zai jawo muhimman masu ruwa da tsaki daga sassa daba-daban na ƙasar nan, waɗanda suka haɗa da hukumomin cigaban al’umma na ƙasa da ƙasa, ma’aikatun da hukumomin gwamnatin tarayya, ‘yan kasuwar fasaha, masu zuba jari, da kamfanonin manhajojin intanet irin su Netflix da Amazon.
“Abubuwan da za a tattauna a taron za su kasance ne kan yadda za a yi amfani da ɓangaren fasaha wajen faɗaɗa tsarin tattalin arziki, da samar da aikin yi, da bunƙasa ƙirƙira a cikin al’umma.
“Domin tabbatar da ingantaccen tsari da aiwatar da taron, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma amince da kafa Kwamitin Shirya Taro (LOC), wanda zai ƙunshi manyan masu ruwa da tsaki daga ita gwamnatin, da ɓangaren ‘yan kasuwa, da ƙungiyoyin masana’antar fasaha, da sarakuna gargajiya da kuma manyan makarantu.
“Taron ba kawai taron je ka na yi ka ba ne, sabon abu ne da za a yi amfani da shi wajen aza Jihar Kano State a kan gaban tsarin tattalin arzikin fasaha na Nijeriya.
“Kannywood, wato masana’antar mu ta finafinai, tare da sanannun masu sana’o’in hannu da muke da su, waɗanda an san su a duniya, suna ci gaba da samun ficen da ya dace. Ta hanyar wannan babban taron, Kano na fatan ta samar da haɓakar tattalin arziki mai ɗorewa, ta rungumi matasan mu, kuma ta buɗe sabbin ƙofofin wasu damarmarkin cigaba wanda ya yi daidai da hangen nesa tare da kishin jama’a irin na Gwamna Abba Kabir Yusuf.”
Gwamnatin ta yi kira ga dukkanin masu ruwa da tsaki da su bada goyon bayan su da sadaukarwa domin a cimma nasara a wannan abu na tarihi wanda ya dace da manyan muradan wannan gwamnati na ganin an ƙarfafa rayuwar matasa, an faɗaɗa hanyoyin tattalin arziki, kuma an inganta tare da farfaɗo da al’adu.”