• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

AFMAN ta taya Sarari murnar samun damar halartar taron baje-kolin finafinan Nijeriya a Toronto da fim ɗin ‘Kakanda’

by MUKHTAR YAKUBU
June 16, 2025
in Labarai
0
AFMAN ta taya Sarari murnar samun damar halartar taron baje-kolin finafinan Nijeriya a Toronto da fim ɗin ‘Kakanda’

Dakta Ahmad Muhammad Sarari

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ƘUNGIYAR masu shirya fim ta Arewa, wato Arewa Film Makers Association of Nigeria (AFMAN), ta taya babban furodusa Dakta Ahmad Sarari murna bisa nasarar ta zaɓen halartar taron baje-kolin finafinan Nijeriya na duniya a birnin Toronto na ƙasar Kanada, wato Toronto International Nollywood Film Festival (TINFF) da fim ɗin sa mai suna ‘Kakanda’.

Wannan sanarwar ta fito ne daga shugaban riƙo na AFMAN na ƙasa, Alhaji Salisu Mohammed Officer, wanda ya bayyana farin cikin ƙungiyar da alfahari da irin wannan gagarumar nasara da kamfanin Sarari Klassique Company Limited ya samu.

AFMAN ta bayyana wannan nasarar a matsayin shaidar hazaƙa, hangen nesa da jajircewar Sarari wajen samar da ingantattun finafinai da ke jan hankalin masu kallo a faɗin duniya.

Ƙungiyar ta jinjina wa sadaukarwar da ya yi wajen tabbatar da inganci a harkar fim, lamarin da ba kawai ya sama wa kamfanin sa yabo ba, har ma ya taimaka wajen bunƙasa masana’antar shirya finafinai a Nijeriya, musamman a Arewa.

Fostar zaɓen ‘Kakanda’ don zuwa taron Toronto

AFMAN ta ce nasarar Sarari wata hanyar ƙarfafa gwiwa ce ga sauran membobin ƙungiyar.

Ta ce kasancewar sa cikin AFMAN na ƙara wa ƙungiyar ƙima, tare da fatan samun ƙarin haɗin gwiwa da nasarori a gaba.

Ƙungiyar ta yi masa fatan alheri a ci gaba da tafiyar sa ta harkar fim.

Takardar taya murna da AFMAN aika wa Sarari

Shi dai fim ɗin ‘Kakanda’, ya lashe guraben zaɓe har shida a bikin baje-kolin finafinai na Kaduna (Kaduna International Film Festival) na bana.

Marubucin labarin fim ɗin shi ne Khalid Musa, yayin da Toka McBaror ya bada umurni.

Guraben su ne:

1. Best Indigenous Film

2. Best Editing

3. Best Actor – Male: Sadiq Ahmad as Junaidu

4. Best Actor – Female: Amina A. Shehu as Mairama

5. Best Supporting Actor – Male: Ado Ahmad Gidan Dabino as Malam Ilu

6. Best Supporting Actor – Female: Farida Adamu as Dela.

Loading

Tags: AFMANAhmadSarariKakandaSalisuOfficertaya murnaTorontoFilmFestival
Previous Post

Naɗa ni jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry Powder da aka yi zai amfani Kannywood baki ɗaya, inji furodusa Abubakar Galadima

Next Post

Tsohon Ministan Shari’a, Malami ya jajanta wa Adam Zango kan haɗarin mota da ya yi 

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Tsohon Ministan Shari’a, Malami ya jajanta wa Adam Zango kan haɗarin mota da ya yi 

Tsohon Ministan Shari'a, Malami ya jajanta wa Adam Zango kan haɗarin mota da ya yi 

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!