BABBAN Sakataren Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, Alhaji Abba El-mustapha, ya jaddada alƙawarin gwamnatin jihar, ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf, na wadata masana’antar Kannywood da dabarun zamani wajen shirya fina-finai.
El-Mustapha ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke gabatar da fom guda ɗari na koyar da dabarun aikin fim ga ‘yan Kannywood na shirin horar da su na tsawon wata biyu kan harkar finafinai da kasuwanci, wanda Cibiyar Finafinai ta Jihar Kano za ta gudanar.

El-Mustapha ya bayyana cewa wannan shiri dai wani ɓangare ne na ƙoƙarin da gwamnatin Jihar Kano ke yi na bunƙasa fasahar ‘yan Kannywood da samar masu dabarun shirya finafinai na zamani da ƙa’idojin aiki da dabarun kasuwanci don bunƙasa dogaro da kai.
Ya ci gaba da cewa, “Shirin na da nufin bai wa mahalarta taron ilimi da kayan aikin da su ka dace don samun nasara a harkar fim.”
Haka kuma ya buƙaci ɗaukacin mahalarta taron da su yi amfani da wannan dama mai ƙima da gwamnatin jihar ta ba su, tare da jaddada muhimmancin yin abin da aka horar da su don ciyar da sana’o’in su gaba da kuma ba da gudunmawa ga cigaban masana’antar fim baki ɗaya.
Ya ce: “Manufar wannan horon da za a gudanar ita ce faɗakar da masu shirya finafinan mu da ayyukan zamani da ƙa’idojin aiki ta yadda za su kasance masu dogaro da kai da samun nasara a harkokin su.”

A ƙarshe ya yaba da gagarumin goyon baya da haɗin kai da gwamnati ta bayar wajen aiwatar da shirin da sauran tsare-tsare da ke amfanar masana’antar.
A nasa jawabin, Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Wasa ta Jihar Kano, Malam Alhassan Kwalle, ya bayyana matuƙar godiya ga gwamnan Jihar Kano bisa jajircewar sa ta inganta masana’antar a jihar.
A cewar sa, “Muna godiya ga Gwamna Yusuf da ya ɗauke mu a matsayin waɗanda su ka cancanta na wannan damar don inganta ƙwarewar mu da horon da za a ba mu. Mu na da tabbacin cewa membobin mu za su iya yin gogayya da takwarorin su na duniya.”